← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 178

Sashe 8

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

👁🥡👁 🅿6⃣. *D* a dare bayan sallar isha'e ne mukhtar ya shirya cikin wata 'yar shaddarsa wacce bata wuce arxiqin talaka ba, kalar brown ce, dudda ba sabuwa bace amman babu wani aibu jikinta dan taji guga ta kwanta tayi luf bisa fatarsa ta usulin fulanin yola, fara tas da ita, hakama hular sa daya sanya bata boye lallusan sumar gashin kansa ba daga bayan qeyan sa wacce ke kwance lub lub. d'an lobia dinsa ya matso ya murza a jikinsa, mukhtar kam akwai tsafta da son q'amshi,, tsakar gida ya iske baban nasa ya durqusa har qasa ya gaishesa, cikin faraa baban ke amsawa, a kunyace mukhtar yace "baba zanje wajen firdausey ne" tuni fara'ar baban ta qaro yace ''af toto yarinyar wajen mlm zayyanu knn? "eh baba" yayi maganar kansa duq'e, baban ya sake cewar "masha Allah, AllAh ya sanya alheri a neman to, ai mariqinta mutumin kirkine mlm zayyanu mai almajirai gaskia" Cewar baban, amman kuma can qasan zuciyarsa yake fatan Allah yasa ita yarinyar firdausey bata dauko mummunan hali iriyan na uwar taba meron tsimbe, dan kuwa dai kaf anguwar tasu kowa yasan mugun halin meron tsimbe. wanda shi kansa mlm zayyanu tafi qarfinsa wani lokacin. ismail dake karatu can qofar dakinsa ya d'aga murya cikin tsokana yace "aminn babanmu, yaya a gaisheta in kaje kuma kada ka dad'e fa, dan inka dad'e baka dawo ba gskia biyoka zanyi dan bazan juri rashin ganin kaba indai nasan kana anguwar nan" baba yace "to sarkin surutu yi abinda ke gabanka zaifima, murmushi mukhtar kawai shidai yayi ya miqe tsaye baba yace "kai kuma ka gaishemun da mlm zayyanu din sosai" to baba insha Allah" da sauri ismail ya biyo bayan mukhtar yace "yaya bari na rakaka waje ko?, "to qanena aida ka zauna ma kada na tadoka daga karatunka" yace "a'a nidai yaya muje ai nan da qofar gida ne kawai fa please " dole mukhtar ya yarda suka fita taren sunajin sanda baban ke cewa inno ta miqo masa tabarma wacce suke zama qofar gida shida su baba yawale suna fira kan goma tayi sannan kowa ya dawo gida cikin iyalinsa . har qofar gidansu salis ismail ya rako yayan nasa sannan ya juya ya koma gida. har dakin maman salis mukhtar ya shiga ya gaisheta sannan ya tambayi ko salis na ciki, maman salis tace " yajima da shiga bayi wanka mukhtar amman nasan yanzun zai fito ya gidan yasu innon taku?" "suna lpia kuma suna gaisheki ma" "ina amsawa kam mukhtar" bari na kawo maka ruwa, nan taje ta kawo masa ruwan masu sanyi na randa cikin kofin sulba babu jimawa salis ya shigo dakin mamar tasu shima ya shirya cikin wani yadin shadda kaida ka gansu shida da salis kasan samari ne masu jini a jika, duban sa mukhtar yayi yace "amman fa ka dade mlm ko so kake muyi dare kn muje?" yayi maganar yana hararar salis d'in, dariya salis ya saki yace "ina zamu knn? "ban sani ba" cewar mukhtar cikin sake hararar sa. sai lokacin salis ya gane zuwa wajen firdausey abokin nasa yake nufi. ta6e baki salis yayi ya dubi mama yace "dan Allah mama ki yima mukhtar dinnan nasiha narasa miyasa dud matan dake anguwar nan yarasa wacce zai ce yanaso zai aura sai firdausey diyar meron tsimbe kiji fa mama dan Allah? ni wlh da ace ma zainab ce yake nema d'iyar mlm zayyanu din da sai na taya sa murnar dace da abokiyar rayuwa ta gari amman wlh firdausey ita kanta da mamanta masifa ne zama dasu kowa yasan hakan" tunda salis ya fara magana mama cikin mamaki take kallon mukhtar sai zuwa can tace "mukhtar da gaske ne abinda naji salisu na fade na kanason firdausey 'yar meron tsimbe matar mlm zayyanu mai almajirai? kai a sunkuye mukhtar yace "eh mama hakane" shiru mama tayi ta fad'a zurfin tunani, ta jima tana jinjina maganar mukhtar din a kwanyarta sannan ta sauke ajiyar zuciya ta kai dubnta ga mukhtar din tace "ni a matsayin mahaifiya nake gareka mukhtar dan haka komi zai cutar dakai zan fad'a maka gskia a kansa, amman ga tambayata gareka a karo na biyu da fatan zaka amsamun su? "insha Allah mama" "miya kaika neman 'yar meron tsimbe kai kuwa, ka kuwa san halin mahaifiyarta kuwa? shiru mukhtar yayi zuwa can yafara mgn knsa na kallon qasa "mama ai bata biyo halin mamarta bane shiyasa, shiru maman salis ta sakeyi tana mai cigaba da kallon mukhtar din sosai, "to inma neman auren ahalin gidan kakeso mizai hana bazaka nemi auren Zainab ba diyar shi mlm zayyanu din ba wannan agolar ba maras tarbiyya?" wannan karon shiru mukhtar yayi kuma yanayin fuskarsa ke nuna baiji dad'in kushen da maman salim kewa su firdausey ba, kuma ai yasan da Zainab din yace yanason ita firdausey din inda dai shi ba makaho bane, shifa abinnan ya ishesa kowa ne abokinsa sai ya kawo kushen tarayyan su da fiddausi to shi kuma yakega danmi zasuna ta kusheta bacin ba iriyar kalar halin maman ta gareta ba waima? sarai maman salem ta lura da yanayin sauyin fuskarsa da maganar, ta kuma lura cewan lallai mukhtar yayi zurfi a son yarinyar yayi nesa maran jin kira kuwa har ta soma tunanin anya kuwa meron tsimbe batayi wani abun akan mukhtar ba kuwa dan yaso 'yar tata duba ga yanda dud samarin anguwar babu wanda ya nuna koda wasa yanason irin nata? yanke shawara tayi kawai ta qyalesa amman gobe sai taje wajen mamarsa inno taji kotasan da mgnr dan yanda ta d'auki mukhtar a matsayin danta bazataso ace ya fad'a tarkon makiran mutanen nan ba, tashi tayi ta basu waje batareda ta qara furta komi ba, mukhtar ya dubi salis yace "dalla mlm ni kataso muje in zaka rakani" salis yace "kai wlh bini a sannu sai nace bazan jeba fa" hararsa mukhtar yayi yace "Allah kuwa baka isa ba ka 6atan lokaci sannan kuma kace bazaka rakani ba" saida salis ya qara jajja masa rai sannan sukaiwa mama dake tsakar gida tana kunna fitilan joni sallama sannan suka fita ta bi mukhtar da kallon tausayi nan kuwa ta fara tuno maganar da sukayi da maman zainab matar mlm zayyanu din dataje gidan dayake aminiyar tace sosai sosai tunkan ma a auro meron tsimbe. a lokacin suna d'aki itada maman zainab din ta bude mata gwanjon safunan sanyi da riguna wanda ita maman zainab din ke siyarwa kawai saiga ita firdausey din ta bankado labulen jikake kuwa jigib ta kayan shanyar da zainab tayi saman igiya saman jikin mmn Zainab din ko bushewa basuyi ba hasalima har digon ruwa wasu kayan keyi daga cikinsu dayake bata jima da wankin ba ita zainab din maman tata ta aiketa siyo kalanzir bakin hanya, sai jisukayi firdausey din tace "baccin iskancin banza har zata zo ta cika wa mutane igiya da shanyar wasu tsummukaran kayanta bacin nima ga tawa shanyar nan inaso zanyi,, ita kuwa mm salis ganin mmn Zainab din batace komi ba tasan kuwa daman bazata ceban danba qaramin haquri take da ba, mafarin knn ta dubi firdausey tace "haba kekuwa firdausey aida kinyi haquri kayan sun bushe inyaso saiki shanya naki... kan firdausey din tace wani abu kuwa saiga meron tsimbe din kamar an Jefota tsaye saman qofan dakin mmn Zainab din ta kama qugu ta riqe tace "to tsohuwar munafuka anqi a bari kayan su bushe nace Anqi din, inkuma kin isa kizo ki maida kayan saman igiya wlh kiga inban nakad'a miki na jaki ba a gidan nan ba har sai anzo an fitar dake, munafuka to ita kanta Zainab din da kuke cewa itace tar gida firdausey kuma nakawota agolanci inda ba gidan mahaifin ta bane munafukai to wlb bari kuji tafita power ta qarfin iko a gidan nan zayyanu dinma daya ajiyeni yayi kad'an yace zai wulaqanta min 'ya na barsa bare ku cakuri cici cukon benci kunzo dakin kun kulle kuna cin naman mutane danye matsiyata"!!! tana maganar ne tana zazzaro ido da wata qatoton muryanta wacce har waje saida aka juyota hakan yasa mlm zayyanu dake koyawa almajirai karatu a qofar gidan kuwa yayi saurin tasowa yana nad'e babban rigarsa wajen sauri har carbin hannunsa na zamewa qasa yana duqawa ya d'auka. yana shiga ya taras da masifar da meron tsimbe din keyi yace "haba mero miya kawoki har bakin qofanta bayaga neman fitina iririyar taki da kika saba? cikin tsawa da hayagaga meron tsimbe tace "masifa anje anyi ai daman nasan da kazo babu wanda zaka bawa rashin gskia inba muba, wlh zayyanu ka kiyaye gamuwanka da mahallaci dan bakai man adalci ka tsaneni nida 'yata a gidan nan" "ni bn tsaneku ba mero halinkune na rashin da'a ke sa bakwa zaman lpia da mutane ina mai tabbatar muku in kuka gyara halayenku kuka dawo na gari kowa zai soku zai qaunace ku kum.... "dalla ni rufemin baki tshohon banza kawai kaima ai munafikin ne" ta qarashe maganar tana nunasa da yatsa idanunta a tsaitsaye, taci gaba da fad'in shanyace kuma an watsar ayi dud abunda zaayi muna dai dai da kowane banza a gidan nan wlh" tana gama fad'in hakan ta dubi firdausey tace "jeki shanyarki 'yata ba gidan ku bane amman kunfi uban kowa matsayi a gidan nan" cikin dariya firdausey tace "shiyasa nike sonki mama na Allah dai ya barmun ke kicimin uban maqiya na wlh" "aminn d'iyata fad'i kanki tsaye " tana gama fad'in hakan ta bangaje mlm zayyanu ta wuce har rawaninsa na tiqan qasa "girgiza kai yayi yace "Allah ya shuryeki mero" cikin tsiwan masifa tace "shirin jigida ba" bai sake cewa komi ba harta shige daki tana murza wani shafaffen d'uwaiya nata q'asa q'asa uwa na kura. firdausey kuwa shanyarta take tana wasu waqe waqenta na futsara wacce rashin tarbiya ce tsantsa kawai a cikinsu amman babu kunya haka take yinsu gaban mmn salis d'in da mmn Zainab sai kuma mlm dake tsaye kansa a qasa, ya jima a haka sannan ya d'ago ya dubi mmn Zainab yace "jameelatu kiyi haquri nasan kina haquri da mutanen nan, to dan Allah na roq'eki ki q'ara akan nada kinji ko, Allah shiyi miki albarka" maman Zainab tace "bakomi mlm aminn" Lokacin da yazo fita daga cikin
Chapter 8 · 0% Book details