← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 178

Sashe 39

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

By
*Xexen Fasaha*
[1/17, 3:10 PM] Xainab Documen: 👁👁
🥡🥡
👁👁
*DA SAURAN KALLO !!!*

Story and writing
by
Xayyneb 💤💤

Fasaha online writers f. o.w.

*🌳imparting valuable knowledge and entartaiment is our concern*🌳.

~dedicated to my mom Sadeeq hawwas~

-https://www.facebook.com/Fasaha-Online-Writes-751775151851852/?referrer=whatsapp.

👁🥡👁
🅿2⃣3⃣.
Sauya fuskarsa mukhtar din yayi kawai yayi kwana da maganar da fadin "ok done boy jeka take care AllAh ya tsare mana kai" saida khaleepa ya d'an duq'o sumb'aci iyayen nasa a gefen fusakokinsu sannan ya fice da sauri yana fadin "ameen dady na da momy"
bayan fitarsa ne mukhtar ya dubi firddausy yace
"miyasa kika hanani aiwatar da manufata?
murmushi tayi sannan ta d'an kurb'i ruwan lemon hannunta sannan ta dubesa tace" hmmn, lokaci yayi da zamu canza taku akan abubuwan da mukewa su Ismail a gaban khaleepa kasan miyasa?
girgiza mata kansa yayi, saida ta taso ta zauna jikinsa sosai tana shafa tafin hannunsa sannan tace"na lura adud sa'ilin da muka ciwa matsiyatan mutanen can mutunci tofa mai tsada na yakan d'auki tsawon lokaci kan mu fara gane kansa a gidan nan, jiya fa abunda kaje kai ma isma'il a gida nasan saboda shine yasa hkn ransa ya baci harya fita da safe batare da ya nemomu ba abinda bai tab'a yi mana knn ba, to kaga knn in dai har muka ci gaba da yin hakan gaba yaya knn? munaji fa muna gani d'anmu zai gujemu a kansu, shiyasa yanzun abunda nikega yafi kawai shine mu daina masu abinda muke musu na rashin mutunci akan idonsa, koba haka ba? dan gskia ni bazan juri ganin bacin ran d'ana ba akan wasu mutane qasqastun bayi ba marassa madogara wanda hatta abunda zasu ciyarda kansu gobe tofa saisun nemesa a ranar sanna suci, hmmm wlh naji baqincikin baq'in abuncin daya ciwo gdn nn jia wlh bakaga iriyar kalar haraswar da ya dinga yiba uwa zai amayo yayan ciKnsa waje fa,abinci ne suka dura masa wanda bai saba cinsa ba dan mugunta fa? hm amman harya iya hanawa aje ai musu magana kmr ynda yace, wai ba laifinsu bane shine ya nace sai yaci sannan suka bar masa yacin, hmm! kai jama'a abun nn na d'aure mun kai fa alhajina wlh tsoro nike kada su janye mun yaro na dud sanda yasan cewa akwai auransa akan wannan shegiyar aljanar yar tasu mai tsinannen kyaun tsiya uwa Aljana, kaini abun nan na damuna wlh gashi sam bata da tsoro yarinyar alhajina karfa ce wlh kada kaso kaga ynda nike daga akan ta daina shigowa mun gidan nan amman na kasa hana shegiyar 'yar nan ta fiye naci.
sauke ajiyar zuciya mukhtar yayi yace "naji komi kibar batun wai zai gane cewa matars ce dan wannan wani kuma shudaddiyar tsohuwar magana ce data gabata shekara da shekaru dan haka kima daina sa damuwar hkn a ranki, kuma gameda zuwana gdn jiya dandai kece ma kikasa naje a bayan hkn da ni rabon dama nasa dan iskan matsiyacin a idanuna nama kwan 2 kinsan ni yanzun batashi nikeba ayyukn gabana muhummai nafi sawa gaba na dan wlh ni har ma mntawa nike dashi a rayuwa bare nasa damuwar hkn a raina, sannan kuma gameda shigowar 'yarsa gidan nn ki qyaleta ta gaji ta daina wataran , dan komin abunta dai bazata dawwama a gidan ba in tazo dole ta koma gidan matsiyacin ubanta ta kwana kuma zataita ganin abubuwa da mahaifinta bai mallakesu ba a gidan konan taji haushi ai mun qaru da hakan, dan baqinciki nasu mu shine farinciki a garemu, to dnnhaka ki janye komi na nuna wata damuwa a ranki ki fita harkasu madam d'ina kamar ynda na fita kada tunanin hkn ma ta jaza miki ciwo please forget them kinji ko, murmushin jin dadi firdauseey tayi tace "yass alhajina an gama hakan kuma za'ayi shawarar ka abun dauka ce" sun jima sannan ya tashi ya wuce toilet dan yayi wnka ita kuma ta wuce kicen dan cigaba da bawa masu aikin order kan ayyukan da suke gudanarwa da kuma dinner din da suke shiryawa.
khaleepa kuwa yana isa hospital d'insu yayi parking a moto park nasu na ma'aikatan nan ya fara tafiya harya shiga cikin asibitin nan yaita gamuwa da nurse sunata kawo gaisuwa da fad'in ''barka da yammaci sir" da "yawwa" kawai yake amsawa yana cibgaba da tafiyarsa batareda yako kalli inda suke ba, dayake yawancin sisters d'in da nurse nurses d'in asbitin dud 'yan mata ne wayayyu aka zuba 'yan bokon gasken gaske ma kuwa, shiyasa kowacensu kesaon ganin tasamu shiga a wajen wannan had'adden handsome likitan matashi mai jini a jika ta ko'ina baida matsalar rayuwa a cewarsu, saidai kuma dai dukknsu tsabar kwarjin da yake musu ne yasa suke kasa shishige masa kamar sauran mazan doctors d'in, dan ko gani yayi doctor sun kirasu ana conversation to indai yana wajen barin wajen yake fuskarsa a kame, jiyake qwamma yaje office d'insa ya kunna kallo a laptop nasa yayi daya zauna wajen yakeji, babu wnda baisan hln muskilan cin doctor khaleepa ba kaf hospital din nasu kuwa,shiyasa yana shiga d'akin Theatre ya iske matar ta farko Alhamdulilla aiki yayi kyau, nan ya rubuta mata wasu magunguna a wani d'an kati wanda za'a siya mata ta dunga sha,
bai jima ba a cikin asibitin ya fito ya shige motarsa dan q'agare yake ya koma gida yaje yaga ya jikin mama zainab dan tun d'azun daya baro gidan still tana ransa shiyasa yana shiga anguwar tasu motarsa kawai ya shigar harabar gidansu ya sake fitowa ya nufi gidan. harya wuce wani waje da ake suya su naman kaji sai kuma yayi tunanin bari ya siya ya tafarwa mama Zainab dashi koda Zataji dadin bakinta taci, nan ya tsaya ya sa aka sa masa guda 3 cikin leda mai layi layi sannan ya wuce gidan kai tsaye ya shiga da sallamar sa, yaji shiru babu amsa, zama yayi nan bisa tabarmar bai jima ba saiga mama Zainab ta fito daga cikin d'akin jikinta sanye da hijab alamun sallar la'asar ta gama, cikin fara'a ta zauna tana fad'in "yi haquri khaleepa kana sallama kaji shiru gashi kuma ina salla ne nazata ma ai heenduh na nan inda nan na barta zaune tana latse latsen wayarta sanda na farka, kaga ashe to tama fice babu mamaki wajen sa'a ta tafi kai wannan yarinyar Allah shirya dai" wani d'an guntun murmushi ya d'an saki wanda iyakar leb'ensa na q'asa ya tsaya sannan yace ''yaya jikin mama? "jiki kam dai Alhamdulillah khaleepa dan ina tashi daga barcin
nan bayan shan magungunan nan bakaji yanda naji sauqin lamurran ba sosai cikin yardar Allah, kuma gashi na samu qarfin jiki na yanda ya kamata, Allah shi albarka dai ngd fa"
a ransa ya amsa da aminn amman a fili ledar ya ajiye mata yace "mama gashi ko zaku buqaci wannsn keda small dad shine na kawo muku, nan mama Zainab tace
"kai ayya khaleepa d'awainiyar nn kada tai ma yawa haka damu dan Allah ka rage wasu abubuwa kaji?"
cikin muryarsan nan din kuma yake cewa "to mama jinike in bnmaku ba wanike da a dud anguwar nan daya fiku?, ku daina cewa komi dan Allah mama" shiru mama Zainab tai tana tuna tsananin kirki iriyar na khaleepa sam bai d'auko halin mamansa da bbnsa ba ta wannan fannin tunani take ita rabonsu ma da cin wani abu mai dad'in azo agani a gidan harta mnta watan ma na shekar bare ranan, zuwa can
dai tace "to shiknn khaleepa mun karba mun kuma gode qwarai da gsk... sallamar baba isma'il ne ta katsewa mama zainba mgn, nn suka amsa masa sannan baba isma'il ya zauna nan kan tabarmar dayake iriyar ta gidan biki din nn ce tabarmar tanada girma amman dutta fara farfashewa sbd jimawar datai.
cikin girmamawa khaleepa ya gaishesa cikin murmushi baba isma'il yace "yawwa dai bokan turawa ykk kaima?' "Alhambdulilla small dad"
yayi maganar yana kallon nad'in bandage dake q'afar ta baba isma'il d'in.
bai q'asa a gwiba cikin tsabar tausayawa ya sake cewa "small dad sannu ciwo kaji ne, miyasa baka kira ba nazo munje hospital namu ba?"
ganin yanda ya damu yasa baba isma'il din yin murmushi yace
"a'a kwantar da hnkalinka likita namu bawai wani west ciwon yaiba kuma bagashi anmun dreesing ba, kada ma kadamu kaji ko?"
"to small dad AllAh baku lpia dukanku" amunn suka amsa, khaleepa ya sunkuyar dakai qasa yace "kuma dan Allah small dad kuyi haquri akan abinda dady na yai muku jia dan Allah, nasan nina jawo muku bacin ran,
da sauri baba Ismail yace "kaji ka, nifa harma na manta da hkn dan haka kada ma ka damu knka kaji?" mama Zainab tace "komi ya wuce khaleepa Allah dai ya sasanta tsakanin iyayen naku aminn"
Nan wajen yai tsit na yan mintoci kan baba isma'il ya tashi ya je d'aki nan yabar mama zainab tanawa khaleepa q'arin godiya akn d'awainiyar su. shidai bai sake cewa komi ba,
suna haka saiga heenduh ta shigo hannunta riqeda handouts guda 2 tana ganinsa kuwa bayan had'a idanu da sukai akaron farko tareda sakarwa junansu kallon banza wani d'an siririn tsoki suka ja a tare, sai dai dud abin nan kuma ashe da sukaiwa juna mama Zainab na kallonsu, ita kam tarasa miya jaza wannan qin da sukewa juna?sam bassa shiri bare a jitu.
itads mlm sunsha tsawatar musu akan hkn amman kmr ba gaya musu ake ba girgiza kai kawai tayi dan gskia har cikin ranta bataso taga rashin jutuwarsu yayi tsawo kamar na iyayensu fatanta a koda yaushe Allah ya had'a musu kan 'ya'yan nasu kar abun yayi yawa kuma gana iyaye ganasu ai sai abin yayi yawa kuma.
kai tsaye heenduh tayi hanyar d'aki dan ganin sa datai wajen yasa taq'i yowa nan kuma.
mama ta bita da kallon takaici tace "ke zonan heenduh" tana tuquburi da turo baki ta dawo can nesa da tabarmar ta zauna tace mama gani,
''daga ina kike da izininwa kika fita? kinsan dai bannason wannan yawon marar dalili ko?"
mama naje fa wajen sa'a nefa aro handouts zan duba sbd ance munads test gobe a school shiyasa na aro sabida zanyi karatu an jima kan na kwanta amman kuma kiyi haquri mama"
mama tace "babu laifi to ni daman yawon ne banso, kuma bakiga d'an uwanki bane zaki wuce d'aki bazaki gaisheda Shiba?, wai heenduh yaushe zakuyi hankali ne keda khaleepa har kuso junanku a matsayinku na makusantan 'yan uwa na jini emm? cikin sake turo baki heenduh tace "tofa mama shine ai bai wa mutane mgn ni sai nai masa?
"ni yimun shuru sakaryar banza baya girmeki ba? na gaya miki bansan wannan shashancin zaki gaishesa koko saina buge wannan bakin naki na tsiwa wa mutane?
Sake duban sa tayi a karo na biyu suka sake hade ido wanda tsananin hasken fararan idanunta daya gani sosai yayinda baqin cikinsu shima yake baqi sosai yasashi wani saurin d'auke fuskarsa daga tata yanna wani tabe lips kamar yaga abun qyama amman miyasa gabansa ya fadi ba a haduwar idanunsu a wannan karon. hakan da heenduh ta gani ne yasata q'ara quluwa akan abunda yai matan kamar yaga kashi dai? Quta tai a ranta tace wlh baccin mama kai kayi kad'an dana tanka maka d'an rainin hankalin mutum kawai, kamar bata so ta bude baki daq'yar tace "sannu"!!!!
bata jira komi zaice bata kwasa taqara gaba zuwa cikin d'aki daman tasan ba amsawar zaiba koda ta gaishesa saiko gashi ile bai amsan ba saima taji ya miqe tsaye bayan shigarta d'aki yanaiwa mama sai anjima, tanajin fitarsa ta miqe tana fad'in "dubesa kawai d'an mannin sense, ni ai gidan ka iske indai kan halinka ne toka samu dai dai kai dan wallahi ko can wahala tana ga matan da suka mato maka suka damu dakai wlh badai niba heenduh dankuwa nafi qarfin tunanin ka fiye da, q'ima.
jin kiran da maman ta ke mata yasa ta matsawa daga gaban tagan dakinsu wacce ke nuna mata waje bayan gama leqen ficewar khaleepa da tagamayi.
"gani mama" abunda tace knn bayan ta iso wajen, hararta mama tai tace ''je leqa dakin babanki kiga in barci yake"
"to"
tna zuwa ta iskesa yana kishingid'e da carbinsa yana ja tace "laaaa baba ashe ba barci kk ba?, tashi zaune yayi yace "a'a heenduh na ba dai barci ba ai babu kyau ma barcin bayan la'asar dan yana haddasa b'acin rai da dai sauransu"
kan ma heendu tace wani abu saiga mama Zainab ta shigo d'akin baban hnnunta daukeda ledar kazar da khaleepa ya kawo musu.
Chapter 39 · 0% Book details