Sashe 137
Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
'Yan uwan, suma kuma su mama Zainab da baba Ismail iriyar tuanin kk jameela hakan ne aransu kuma suke fata. shima daddy salis gida ya wuce. su mama Zainab ne suka shiga gida heendun naqoqarin binsu ciki a d'arare babu zato taji an ruqo mata qasan hijab..dasauri tajuyo ganin doctor ne keta marairaicewa akan tatsaya su gaisa da baby nayler cikin inkiya dayake mata ata cikin nagartattun idanunsa zuwa nata,aiko cikin kunya ta fuzge hijab dinta dan ganin mama Zainab tajuyo takamasu ahakan, aiko da gudu tayi cikn gida shi murmushi abinma yabasa, ahaka yatafi yanajin zuciyarsa wasai yau na tunanin su mama Zainab sunsan yasan wacece heenduh garesa inda harda babban sheda ma ajikinta. heendu kuwa tana shiga gidan nasu tasamu su mama Zainab zaune nn tsakar gida aiko cikin kunya ta rab'asu tabi ta jikin bango tana qoqarin shigewa cikin dakinta knn taji baba Ismail yace "yaki zonan ki zauna heenduh na" wata sanyayan ajiyar zuciya ta sauke jin mgnr tasa cikin kulawa bakamar d'azun ba daya tashi hankalin ta, kazalika koda tajuyo taga fuskar mama Zainab asake itama hakan baqaramin dadi da nutsuwa ya kamata ba lokaci daya. danhaka cikin qarfin gwiwa ta dawo tazauna kusada baba Ismail din kanta qasa dan kunyar cikin jikinta take jiwa kanta dan tasan izuwa yanzun iyayen nata sunsan tayanda tasamu cikin dud saitaji kunyar m@ had'a idanu takeji dasu ita kam yanzu. sosai su mama Zainab suka lura da hakan dan haka suka dubi juna shida mama Zainab sukai murmushi. baba Ismail yai gyaran murya yace "daga farko mun fahimci zancen baibai heenduh dudda damn muna tantaman tarbiyyar da mukai miki bazaki iya watsi da'ita ba saidai zuwan qaddara wacce ta rigayi fata kuma, muna miki addu'an Allah saukeki lpia, snn kuma mamanki zata dinga baki kulawa insha Allah, yanzun kije d'akin ki huta ko Inda ansha kuka dagake har Maman naki" yayi mgnr cikin myrmushin son mgn. afakaice mama Zainab ta wulqa masa harara tadubi heenduh tace "jeki daki heenduh inkinason wani abun kimim mgn" haka heenduh tawuni daki komi takeson ci kuwa mama Zainab sai tai mata shi kankace mi... farinciki yadawo cikin rayuwar heenduh sabanin dazun dayai mata balaguro a jiki. abin Allah kuma daga mama Zainab har baba Ismail sai sukaji son cikin jikim heenduhn tasu har cikin ransu dazuciya daya kuma. washe garin ranar da misalin qarfe tara na safe dady salis zaune cikin motarsa yana driving dan tafia airport dauko babban aminin nasa wanda jirginsu zai sauka nanda hour guda, kuma daga khaleepa har Hjy furdauseey babu wanda mukhtar din yafadawa zaidawo yaudin dan sosai yakeson musu surprise. dady salis din na'isa airport din tunkan yafito ya miqa hannunsa ya dauko sanyayen laksera mai duhu yad'an sha kad'an ya rage iya adadin yanda rubutun nan daya karbo zai ida cikashe robar, bismilla yai tareda fasa qullin rubutun ya zurara sa ata bakin robar duka sannan ya karkad'e ya mayarda murfin a kai ya rufe tareda ajiye robar lemon gaban motarsa. sannan yafito ya qarasa wajen zaman tarbar baqin na airport din wanda keda jama'a da dama dasukazo daukar 'yan uwansu da abokan arzuqan su suma. ba'a dau rabin awa ba jirgin su yasauka matafiyan suka fara saukowa one by one yayinda dady mukhtar shine mutum na uku a sahun fitowa, sosai yanisa tareda shaqar iskar Nigeria dinsa ahankali yakejin kewa ta babban shaqiqinsa qanensa kuma dan uwansa wanda baisan miyasa ba akwanan nan yake matuqar jin hakan ajikinsa musamman ma yawan mafarkan baffansa da inno dayakeyi dazarar ya runtsa kuwa, babban ma abunda ke tada masa hankali yanda muraran cikin mafarkin nasa dazarar yaga iyayen nasa saiyai yunqurun binsu amman saiyaga sun juya masa baya alamun kamar suna fushi dashi ma,, qwalwarsa kuma tatushe yanason tunano wane laifi yaimusu amman sam yakasa saima yaji wani abun daban yataso yatokare wannan tunanin nasa. mafarkin dayai Daren jia da baffansa shine yana zaune saiga baffansa yazo har inda yake babu abunda yake cewa face"kariqe addo'e mukhtar domun addua da azkar muddin takobin mumune ce kaikuma kajima da daina yunsu dudda kanada ilimin sanunsu, salla akan lokacinta tana yawan kucce maka mukhtar sbd zafin neman duniya shin tayaya in kanaqin yin hakan salla Kn lokacinta da addu'oen Neman kariyar ta ubangijinmu kowanne abu bazaiyi tasiri akanba ba in aka maka?" daidai nan ne kuma mukhtar din ya farka, haka yawuni sukuku tun lokacin dan daqyar ma yaqarasa shirya komi nasa sannan yabaro qasar. sauke ajiyar zuciya yai tareda ida saukowa saman matakalan jirgin yatunkaro inda yahango daddy salis suna tsattsaye. sosai dady salis yaga abokin nasa yaqara haske da stayi da kakkauran jiki, kyau da annuri alamun hankalinsa kwance,saidai alamun manyanta data fara rizqarsu. cikin tsantsar farinciki suka rungume juna suna dariya saidaga busani suka kwashi trolleys dinsa sukasa a motor suka shiga suma suka fara tafia. cikin murmushi dady salis yadubi dady mukhtar yace"welcome back to our nation my big friend fatan komi lpia ko?" cikin murmushi dady mukhtar yace"oh thanks so my big friend All is fine alhamdulilla ya qasar tamu Yakuma yarana su meenat" "Komi lpia abokina,yayi mgnr tareda dauko laksera dinnan mai rubutun Mlm aciki yadubesa yace "gashi kadan taba abu mai sanyi natanadar maka shine domin nasan zai amfaneka tareda zama garkuwa a cikin jikinka" sosai dady mukhtar ya fadada murmushinsa ya miqa hannunsa ya karba tareda furta "Kasanko daman ina buqatar Abu mai sanyi kasan whether tacan data nan Nigeria tasha mana bambam shiyasa dud bayan lokaci nikejin qishi gakuma zafi,but nasan zandaina daga yau Inda nadawo qasata abar alfaharina ko friend" murmushi sukai daganan ya bude murfin robar zaifarasha dasauri dady salis yace "my friend zaifi maka kyau kafin kafarasha don't forget bismilla kafara bismilla zaifi ma'ana" "hakane abokina nasha'afa ne kuma na gode datunatarwa amini na qwarai'' yayi mgnr cikin murmushi tareda yin bismillsn yakafa bakinsa arobar yafara sha wanda bashine ya janye robar ba saidaya shanye lemon tas sannan. cikin murmushin jin dadi dady salis yace"gskia abokina kaji qishin ruwa fa inaga" dady mukhtar yace"wlh kuwa kuma bakaji yanda hadin lemon nan yaimyn ba babu qarfin gass dinnan nasa sosai kmr ammasa surki ne" wani murmushi dady salis yasakeyi ataqaice yace"inaga haka yazo maka kai" shiru dady mukhtar yai jin yanda zufa keta ketowa a jikinsa saifaman share goshinsa yake da hankicerf. sosai dady salis yalura da hakan shiyasa yaishiru harsuka qaraso anguwar tasu akuma gate dun gidan dady mukhtar din. yunus ne yaga fitowarsu motan danhaka yayi saurin isowa wajen yafasa shiga motarsa zuwa inda zaijen ga lokacin. gaishesu yai cikin farincikin dawowan dady mukhtar din snn dakansa yadunga daukar jikkunan yana shigar dasu ciki. nan dady salis yadubesa yace"zan wuce friend saimun hadu anjima" cikin rashin jin dadi dady mukhtar yace"haba mana friend bazamu shiga tare cikin gidan ba knn?" girgiza kai dady salis yai cikin fara'a yace''inaso kahuta sosai inkai wanka kaci abinci abokina zamu hadu tonight insha Allah danzanje office ne yanzun" "To shiknn my friend ngd saimun hadun" musabuha sukaqarayi snn suka rabun. lokacin ne yunus yafito daga gidan yasake yiwa dady salis barka da dawowa cikin jin dadi dady mukhtar ya amsa sannan yunus yashiga motarsa cikin sauri domin yaqagara ya isa hospital dinsu khaleepa danya fado masa zuwan bazatan dadyn nasa. dady mukhtar kuwa afalo yaci karo da Hjy furdauseey tana qoqarin fitowa taga mijin NATA. aiko qanqamesa tai tana ihun murna jikinta sai b'ari yake batasan dalilin faruwan hakan ba. ruwan wanka ta hada masa yashiga yayo yafito yazura jallabiya sukahau dining saifaman nan danan takeyi dashi hatta abuncin ita tabasa ma. saidaya gama cin abuncin sannan suka dawo nan qasan falon suka zauna cikin washe baki hjy furdauseey tadubesa tace"oni auran maitsada na da zarah yatafo knn Inda kadawo... dakatar da ita yai yace"haba Hjy ta kibari Mayi mgnr daga baya yanzun ina buqatar hutawa ne"sororo tai tana kallonsa aranta take furta"ni furdauseey yau mi kunnena ke jiye mun ne? Mukhtar keman musun yagaji fa akan mgn dazan masa sabanin da dajikinsa har rawa yk wajen sauraran uzurina? amman dayake muguwar yar bariki ce ata kowane fanni shiyasa tai saurin saita nutsuwarta tareda cewa''afuwan to alhajina ahuta lpia... tana qoqarin miqewa saiga khaleepa asukwane yashigo falon. hakanne yasa takoma ta zauna. a hanzarce yaqarasa jikin dadyn ya kwanta yace"barka da dawowa my dad imiss you a lot" cikin sabon murnushi dady mukhtar yace"miss you too my don, my gental man yanaga kaqara girma haka kama zarce handsome mi momynka take girka maka kakusan taddoni agirma?" dariya Hjy furdsuseey tai tace"wlh kuwa alhajina nima ina mamakin budewar da maitsada na yake qarayi Uwa mai sabon aure, amman inaga hakan yasamo asali ne daga dokin auransa dayake da zarah ko maitsada na?" nanda nan khaleepa yaji ransa yabaci Da mgnr zarah data sako. tsam ya miqe yana yamutsa fuska yace"Momy dady zankoma hospital daman ina cikin ayyuka ne natafo ganin Dad na" yana gama fadin HK yaisaurin ficewa yashige motarsa yabar anguwar. Acan falo kuwa dady mukhtar yaturawa Hjy furdausey jikkunan tsarabovinsu sannan yadauki sauran yanufi dakunsa dasu bacin yace mata zai kwanta yadan huta. dole tahaqura ta kwashi kayan tashige dakunta badan taso So ba. khaleepa sai ana gama sallar isha'e ya shigo cikin anguwar. Har qofan gidan baba Ismail yaje ya tsaya da motarsa yana son Shiga gidan amman wata masifaffiyan kunyarsu yakeji, sosai yamatsu dason ganin baby pace cut sugar n tasa yarasa yadda zaiyi. saiya fito kamar zai nufi gidan snn ya koma motar tasa kuma, wayarsa yajawo yadanna number heenduhn amman katsam yaji ana cewa it's switch off. runtse idanunsa yai gam sosai yaji kansa nason yafara ciwo ransa namasa babu dadi zuciyarsa nabasa kalar d'aci2 wata zuciyar tace"kai maganin matsalar nan khaleepa koka samu sauqin zyciyarka gamida dawowar matarka hannunka kadaina zagaye zagayen nan dan abun yayi yawa gskia. yana gama tunanin hakan da sauri kuwa ya juya kan motarsa zuwa gida. dawani sabon saurin yakashe motar yashigo falon gidan inda ya iske momynsa da dadynsa zaune a falon suna kallon tashar BBC London. ganin yanda yafado musu falon a sukwane yasasu saurun miqewa tsaye dan azatonsu ba lpia ba musamman ganin yanda sukai idanunsa sunyi jazur jijiyoyin kansa suntaso rad'a rad'a. agigice kuwa Hjy furdauseey ta matsa gabansa tana kamo hannuwansa take cewa"mai tsadana