Sashe 50
Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
👁🥡👁 🅿2⃣7⃣. Lokacin da doctor khaleepa din ya fito waje yayi matuqar mamakin ganin heendu tsaye bakin motar musaddiq. daman musaddiq yasan tane? to inya santa tayaya bai ta6a ganinsu tare ba? , tambayar da yakewa kansa knn, sam jiyayi bai iya shiga gida kamar yanda yai niyya saima samun waje yayi nan cikin barandar gidansu inda suke zama bisa fararen kujerinsu shida friends d'insa dud in sun samu lokacin hkn. bayan ya zauna bisa kujerar tareda d'ora qafafunsa bisa wata kujerar daya bisa daya yana girgiza su yai setin inda su heendu ke tsaye yana kalla qasa qasa zuciyar sa na masa wani ba dad'i2 yakeji lkcn. amman bazaka ta6a cewa yadamu dasu ba bare ya kallesu amman kuma dud rabin hankalin sa na wajen dudda knsa naga kllon fuskar wayarsa daya tsurawa ido yana lallatsa ta. acan 6angaren su heendu kuwa sa'a na tafiya musaddiq ya juyo rareda tsurawa kyakkyawan surar fuskar heendu ido ya saki murmushi yace"mai hasken zuciya ta ina matuqar son fararen idanun nan naki da hancin nn naki gamida baki Allah sa in minyi aure ki bani baby girl mai kama dake sak din nan haka babyn raina" a yatsine heendu tace"hmm qwamma da kace mace ma" cikin 'yar dariya yace bakison ki haifi baby boy ne? "qwarai fadi kanka tsaye ni mace nikeson haifa dud in nai aure, ko awane haihuwa zanyi zanso naita haifar ta" kama baki musaddiq yai yace "lallaikam gimbiyar mata a gaisheki gskia kam kina son baby girls naga alama "yayi idashe yin maganar tasa tareda bude murfin gaban motarsa ya fiddo wani dan babban kwalin waya ya miqa mata tareda cewa ga barka da jumaa amman dan girman Allah kada kuce bakiso dan nasan halinki,,,murmushi heendu tai ta saci kallon inda doctor khaleepa yake zaune dan tun wucewarsa take satar kllonsa har inda yake zaune, dan haka wata zuciyar tace mata "ki kar6i kyautar wayar nan man heendu kodan ki q'ara k'onawa dan rainin hankalin nn rai nan take ko ta miqa hannu daya ta karba a yangance tareda furta kalmar "thankzzzz" haka musaddiq yaita fira itako gimbiyar sai wacce taga dama sannan take zabar mgnrsa daya ta basa amsa har tagaji da tsayuwar ta dubesa tace"zan koma gida musaddiq kasan bn jumurin tsayuwa daiko? murmushi yayi yace "nasani gimbiyar mata amman sai yaushe za'amun alfarmar sake dawowa dan na kalli wannan iriyar kyakkyawan fuskar taki gimbiyar mata? saida ta dan sake yatsina lips dinta sannan tace "komi knn mayi waya" daga haka ta juya ta shige gidan baba d'ahara mai qoli2 shiko yabi bayanta da kallo dan gaba daya yarinyar tayi kota ina, sauke ajiyar zuciya yai tareda shiga motarsa ya bata wuta tareda nufa hanyar gidansu, dayake can qasan layin gidansu yk. tun lokacin da doctor khaleepa yaga heendu ta karb'i abu cikin kwalin da musaddiq ya bata dudda baisan komi ba ne a ciki amman saida yaji kamar dai babu dad'i haka a ransa, daga qarshe dai dayaga abun kamar zaisha tunanin sa tabe lips kawai yai tareda korar tunanin hkn a brain dinsa ya gyara zamnsa yaci gaba da touching din wayarsa knn yaji muryar yunus na cewa "yadai friend kai d'aya ne zaune a wajen haka? amman to nayi mamaki dan nasan baka zama kai daya wajen koko kana jiran wani abu ne?" dubnsa doctor khaleepa yayi yajima sannan yasamu ya bude bakinsa yace"no yunus kawai dai ina dan futawa ne nan din shiyasa" gyara zama yunus yayi yace "oh koda naji dai mutumina, but ya naga ba baka shirya zuwa buga Ball bane? naga baka sa kayan ba, gashi kuma dud sauran friends namu sun shirya su muhsin da lawal da muazzam fa" saida doctor khaleepa yad'an mammatsa gefen kansa da yatsunsa guda biyu sannan ya furzar da iska yace"yunus bansan ya akai banjin dad'in zuciya ta bane da jiki na ina tunanin masassara ne keson riqe ni" yunus yace "subhanalla friend indai ko haka ne yakamata ka shiga ciki ka d'an sha magani saika kwanta ko? " girgiza kai doctor khaleepan yayi tareda cewa"zanje buga ball dinnan banson na kwanta ne hot fever dinnan ta saukar mun qwamma inje in excercise na buga ball dinnan kozan samu qarfi qarfi bari na shirya ynxun gani nan fitowa" yayi maganar yana mai miqewa tsaye. Yunus yace ''to inda kace hakan ai lpia lau" bai jimaba sai gashi ya shiryo cikin wasu fararan kayan q'wallo masu ratsin baq'i wanda sukai matuqar qara haskaka zatin surarsa,farar safar iya gwiwarsa ta tsaya sakamakon yanda dai kayan qwallo suke kamar ynda kowa yasani. duqawa yai tareda ida d'aure cambus din igiyoyin takalman sannan suka wuce play ball din tareda sauran friends din nasu. heendu kuwa tana shiga gidan baba d'ahara ta isketa tana toya q'uli q'uli cikin man gyad'a wanda q'amshin sa dud ya buge wajen da sauri heendu ta ajiye gyalanta da kwalin wayar ta isa wata kujera dake gefen baba d'ahara d'in ta zauna tareda fadin "tsohe ya naga q'ulin yau kad'an ne kuma ba kamar na kullum ba? " baba d'ahara tace"kedai bari hendo wannan q'ulin na alq'awali ne yau mukai dasu zasu zo karb'ar ragowar masu sarin nasa, dayake jiya suka zo suka d'auki wani, shine nike sauri na ida kona samu naje gidan bikin nan gobe da wurwuri" heendu tadan lakuto tunkuzar da qaramin yatsanta guda daya ta sa bakinta ta tsotse sannan tace "biki zakuyi ne tsohe?" baba d'ahara tace"kaji yarinyar nan kuma dai? kaddai kin mance da bikin zeenatu nane 'yar qanwa ta wanda za'a fara sa gobe? zaro idanuwa heendu tai tace "Allah kuwa tsohuwa na mnta ashe gobe ne ake fara bikin? baba d'ahara tace "aikodai gobe ne ga mai yawancin rai" matsowa heendu tai tareda ruqo d'ayan hannun baba d'ahara tace"yawwa tsohuwar nan wani temako nikeson kimin wajen mama dan Allah kamar yanda kika saba yi muna kinji 'yar baba d'aharar baba yawale?" da baba d'ahara harta janye baki tana wa heendu kallon hadarin kaji iriyar dai ynda tsoffi ke karkace fuska amman tanajin heendun ta sako mata batun baba yawale a ciki tuni ta saki fuskarta dan baba d'ahara tana matuqar qaunar baba yawale ba kad'an ba kuwa. duban heendu tai tace"ina saurarinki Allah sadai ba wata qaryar zaki sani naje lankatab'awa uwarki zainabu ba kamar ynda kuka saba sani keda sa'a, nidai dan Allah yaran nan kudaina sani qaryar nan hka dn shekaru na ja fa suke farinciki nane mani inga kun fuddo mazajen aure muyi mu aurar daku koma huta da yawon nan naku na gaira babu sabar" fari heendu tai wa baba d'ahara da idanun tan nan tace "kai caiiiii Tsohuwar nan baki iya cin ribar zance bafa, yaseen jiya na jewa baba yawale da maganar aurenku fa" tuni baba d'ahara ta wangalr baki tareda ajiye tunkuzar dake hannunta tasake duban heendu sosai tace"kai 'yar nan hendo fad'a mun to yaya ce miki? d'an tsinano baki heendu tai tace ''kamin na fad'a miki komi na shirya fatan dai zaki mana yanda muke so ko baba d'aharas ras tamu? cikin dariya baba d'ahara tace "kaji ja'irar yarinya da wayau wato so kike miyi bani gishiri na baki manda ko? ''yawwa baba d'aharas ras kinje gana dai knn" kingane so nike koda yaushe ne inkin gama tuya kuli kulin nan kije ki samu mama ki mata bayanin muma zamu jewa zeenatu walima goben nasan inda kece kikai mata mgnr da knki zata yarda kinji ko dan Allah baba d'ahara?! please nida sa'a zaki ce mata zamu je" kama baki baba d'ahara tai tace "o'oni yaran zamani, to kenan ina kukai niyyar zuwa inda ba wajen bikin zeena d'in kuka yanki tikitin nufa ba? murya qasa qasa heendu tace "kin gane ko baba d'ahara wlh kuwa partyn wata class mate dinmu zamuje gobe ne ake yinsa nasan kuma inna cewa mama partyn wata ne zamuje zata hanani zuwa ne shiyasa nazo na had'a wannan planing din kinji ko baba d'ahara, dan Allah ki taimaka mana kada kisa muji kunyar qawar nan tamu kuma wlh tayi masifar yarda damu a matsayin big friends nata" baba d'ahara tace "manyan abokai na shegantaka ko na yan bokon zamani?' heendu tace "Wayyo baba d'ahara kada kice haka man please zakije dai yanzun ko? walle fa in baki jeba nima bazan fad'a miki plan da zan shirya gameda auranku da baba yawale mairan qarfe na ba inna gama tsarawa ba" saida baba d'ahara ta harareta sannan tace "to naji zanje amman saida dare inna gama tuyar nn fa, da sauri heendu tace "inda dai zakije ai babu matsala baba d'aharas ras ta" nan ma baba d'ahara tace "amman fa akwai matsala hendo,, cikin zaro idanuwa heendu tace "amman kuma wace iriyar matsala kuma?! kan baba d'ahara tace wani abu saiga sa'a ta shigo gidan tace "hmn ai daman nasan heendu ki na nan inda kince mun yatafi, naje gida mama tacemun baki shigo ba shiyasa nayo nan" heendu ta jawo hannun sa'a tace "ke dalla yimana shiru cakwai-kwaiwa bari kiji... nan ta fad'a mata yanda sukai da baba d'ahara yanzun gameda zuwa fatin hapsat. itama sa'a cikin d'an tsoro2 tace"tofa baba d'ahara wace matsala kuma dai? Baccin muna kuma murna komi ya tafi yanda aka tsara? " heendu tace"nima dai shi nagani ai" baba d'ahara saida ta kwashe q'ulinta tasake zuba wata tunkuzar amai sannan tace "matsalar itace ni ba gobe zan dawo ba sai gata inda dai mu zamuyi hidimar abuncin bikin can gidansu amaryar kunga dawowar mu tare daku zaisha ban ban knn ko? sauke ajiyar zuciya heendu tai tace"kai ni wlh harkin tsorata ni baba d'ahara, to ai indai haka ne mu munji dad'i kunga bamu ba zullumin ko zaki rigamu dawowa gida a goben bare har mama ta tambayeki mu ina muka tsaya koko sa'a?!" sa'a tace "wlh kuwa kedai q'awas dan inaga bawai da wuri za'a gama fartyn nan bama" baba d'ahara ta coge baki tace"ah to wannan kuma ya rage ruwanku, nanta juya taci gaba da tsame qulinta, qarshedai basu baro gidanba saida suka ci zogale da quli wnda baba d'ahara d'in take siyarwar a alakoro kamar ynda suka saba dud in sunzo sunyi Sa'ar tayi san. daga nan kuma gidan kaka jameela heendu suka nufa wato mamar mama zainab knn, suna wucewa kuwa ta