← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 141 OF 178

Sashe 141

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kaddai kana nufin kace yatafi da fushin yayansa akan munanan laifukan daya dinga aikata masa da iyayensu? kaddai kacemun yatsani ganin yayansa ne salis shiyasa yabar garin dan girman mahaliccunmu Allah?!!,,,,, sakinsa yai yaduqe jikinsa qasa yana kuka yake cewa "billahel azeem salis a dud inda qanena yashige arayuwa koda kuwa ace zan rasa dukiyata, lpia ta, raina,saina gano gudan jinina na nemi yafiyarsa najiyar dashi jin dadin rayuwa sannan zan samu salama a cikin zuciyata..can yatsaida kukan tareda miqewa tsaye yana share hawayen sa cikin murmushi dole yake cewa murya narawa "kaicona salis nabar iyayena da dan uwana da baqincina aransu wanda narantse da girman Allah mahallicina salis bansan sanda hankali ya gurgurshe mun daga jikina ba harta kaini ga aikata musu wannan mummunan laifukan dani kaina bazan iya yafewa kaina shiba face qanena yaya femun...kakarewa mgne tai nadan lokaci sannan yasamu mgnr ta dawo masa yaci gaba da cewa"zan nemosa a rayuwa, salis zan Shiga duniya nemo qanena jinina mudawo muyi rayuwarmu cikin farinciki kamar yanda muka farota kamun wannan mumunan qaddarar data afko mani.. yaqarashe mgnr tareda rungume salis yana sake fiddo hawaye masu tsananin zafi da quna a zuciya. sosai zuciyar salis yaji takaraya shima yafara hawayen tausayin mukhtar danzuwa yanzun kam ya yarda cewa💯wato d'ari bisa d'ari hankalin mukhtar din sa yadawo jikinsa inda har yake fadin wannan maganganun masu ciwo dubaga ma yanda yakeyi kamar zai shide wajen mgnr sbd qona masa rai da abinda ya aikatawa ahalin nasa kuma yake fad'a da bakinsa kunnensa nasake jiye masa hakan, kuma dud sanda kuwa mummunan furuci daya yafito daga bakinsa dangane da abinda yaiwa qanen nasa a rayuwa kukansa dad'a qaruwa yakeyi danya lura da hakan sosai shi dady salis din. hannunsa dady salis ya kamo suka shiga cikin motar mukhtar din shida Kansa dady salis din ke tuqi batareda yasake cewa dady mukhtar din komi ba, baitsaya ko'ina ba sai qofar gidan baba Ismail din dankuwa yanada tabbacin baije office ba yau yana gida yau weekend. dady salis yace"muje qanenka nacikin gidannan bar yanzun dan wasa nike maka baibar gari ba"dagudu dady mukhtar yayi cikin gidan kuwa. hakan kuwa akayi dan nan saman qaton shimfidadden carpert suka samesu shida mama Zainab suna fira yayinda heendun ke kwance saman qafafun mama Zainab tana mata parking din tulin gashin kan nan nata data gama mata shartarsa. ai suna ganin mukhtar din yashigo gidan yana tunkarosu babu wanda baiji d'ar aransa ba dan atunaninsu koyaji mgnr cikin heenduh ne yashigo wulaqantasu kamar yanda yasaba. dan haka kallonsa kawai suke suna jiran jin damai yazo kuma yau. tuni heenduh tadauki mayafinta ta rufe kanta bayan ta miqe zaune tanawa dady salis sannu da zuwa danko kallon inda dadyn mukhtar yake tsaye ba taiba sam. sosai mukhtar yaji zafin hakan a karo na farko a rayuwarsa ace wacce take matsayin 'yarsa take nuna masa halin ko'inkula haka? amman kominene yama faru shine sila ay. tuni hawaye suka sake cicciko masa a idanunsa dawani mugun hanzari ya ida isa gaban qanen nasa baijira komi ba ya rungumesa yana cigaba da zubda hawaye na tsantsar nadama cewa yake "qanena ga yayanka yadawo gareka yana mai neman yafiyarka akan munanan abubuwan daya akaita gareku da iyalinka,, qanena kawa girman Allah da iyayenmu kadubeni cikin salama batareda ka tuno abinda na'aikata gareka ba kayafen qanena nayi nadama a rayiwa ta, wlh qanena nikaina ban cewa ga dalilin dayasa Nike maka haka a lokacin, dan sainayi nakoma na zauna kuma nadingajin zafin hakan mai ciwo a cikin qasan zuciyata dan billaheel azeem nagaza sanin miya sameni a lokacin jina nake kamar baniba ne wani mutum ne daban ke rayuwa a jikina..amman a yau najini a jikina nine, nine mukhtar din Ismail na inno da baffa..!!! kayafemun qanena gani na durqushe a gabanka yau ina yafeyanka kayafen dan darajar iyayenmu qanena" yayi mgnr tareda durqushewa saman gwiwowinsa hannuwansa hade waje daya ya fuskanci Ismail alamun Neman tuban sa qarara a fuskarsa dahar lokacin bata daina zubda hawaye ba. gaba dayan wajen saida jikinsu yai sanyi dajin kalaman mukhtar dan mama Zainab da heenduh suma basusan sanda suka dinga share hawaye facey facey a fuskarsu na tsananun tausayin nadamarsa daya nuna qarara yana kuka kuma. Allah sarki dagudu baba Ismail yashige jikin yayan nasa shima yana kuka, amman shi kukan farinciki yake na dawowar yayansa garesa, d'an uwansa talli daya a rayuwa hankalinsa yadawo garesa tomi yafi wannan dadi da farinciki bayaga yadinga godia ga Allah mabuwayi gagara misali. saida sukai kuka sosai dan tunowa da rayuwarsu ta baya dasukai da iyayensu mai dadi saidaga bisani baba Ismail yadinga cewa"wlh nina nayafe maka Yaya na, daman ban riqekaba a raina Sanin yanda muka shaqu da juna nasan cewa komin Daren dadewa muddan darai a jikinmu zaka dawo ga gudan qanenka,zamu cigaba da yin daddadan rayuwar mu cikin salama da qaunar juna kamar yanda muka saba tun yarinta". yaqarashe mgnr tareda qara riqe yayan nasa yana hamdala gamida yiwa annabi salati. jikin kowa zuwa lokacin ya mutu mururus a wajen kuwa sbd kukan babba tashin hankali ne dashi. daqyar suka saita hankulansu suka zauna nan kan carpet din sosai gaba dayansu sann mukhtar yace"ngd sosai qanena daka yafemun ngd ngd"! mgnr yake yana goge hawayen fuskarsa dasuka gaza yanke masa har lokacin, yana murmushi kuma. kamo hannuwansa baba Ismail yai yace"yayana kadaina damuwa dan qanenka komi yawuce garesa tamfar ba'aiba dan haka kadaina *tuna baya* kan wannan lamarin daya wuce ma dan Allah" yayi mgnr cikin murmushi" shima dady mukhtar din yayi wani qaqararren murmushi baice komiba dan ko haryanzun abunda yaiwa qanen nasa dud inya tunosa baqaramin bugun zuciyarsa yake qara yiba. d'an bata fuska baba Ismail yai sbd lura da hakan dayai dan haka yayi nufin furta masa abinda suka saba cewa juna shi sa'ilin yarinta dadud in daya yaga dayan a halin damuwa, sake duban yayan nasa yai yace *"zanyi fushi dakai na tsawon minti daya yayana,* inhar baka daina damuwa haka bafa"yaqarashe mgnr cikin d'an murmushi.,Allah sarki nan take mukhtar yasaki dariyan dabai shirya ba sbd tuno wannan ta'adar tasun dayai. nantake sika ida yin d'ayar ta'adar tasu wato suka had'a hannu🤜🏻🤛a dun qule suka sake sakin dariya cikin farinciki kmr su cinye juna dan murnar farincikin shiryawar tasu yau a rayuwa cikin hukuncin Allah. cikin murmushi dady mukhtar yadubi mama Zainab datake qara goge qwallar farinciki tana mai fatan Allah sa wannan shiryuwar harda yayar tata furdauseey. jitai dady mukhtar din yace"Zainab kema kiyafemun laifukan danai miki dankema kinada haqqi akan furta yafiyarki a kaina danna matsa muku number haqiqa a rayuwa" dasauri mama Zainab ta girgiza kai cikin kakalo murmushi tace"bakomi Yaya mukhtar nayafe maka ubabgiji Allah yayafe mana baki daya" aminn suka amsa harda dady salis dake gefensu yanata faman zuba murmushi. " 'Yata kema zaki yafewa baban naki ko?" cewar dady mukhtar din daya dubi heenduh cikin fara'a. akunyace tace"sosaima nayafe maka komi duka dady" taqarashe mgnr cikin miqewa tsaye dasauri tabar wajen tashige dakinta ranta fal qal murnar hadin kawunan iyayen NATA. dariya sukai mata nan take dady salis yasasu kowannen yai salatin annabi Muhammad s.a.w. dan qara jadada farincikinsu kan hakan. bayan sunyi harda add'ou harga iyayensu sun shafa ne sannan dady mukhtar yaita kallon gidan qanen nasa cikin mamaki danyasan da gidan aiba haka shike ba dandud yamace sa'ilin daya sansu cikinsa. baba Ismail ne yalura da hakan dan nhaka yace"yayana wannan gidan namu Yaya salis nema yagyara mana shi sannan yabani manager a ma'aikatarsa(dayake shima dady salis yashaidawa mukhtar din ma'sanaantar tasa daya bude) danhaka kaga komi na rayuwarmu yacanza cikin ikon Allah"cikin tsantsar farinciki dady mukhtar ya rungume dady salis yana masa godiyar alherin dayaiwa qanen nasa, shiko dady salis nunawa yai babu komi ai dud yiwa Kaine an rigaya da zama daya. sunjima suna zaman farinciki da mgnr cikin heenduh da dady mukhtar yaimusu cikin tsananin jindadin zai samu jika a jinin dan uwansa. sai wajen qarfe sha biyu na safiyan ranar sannan dady mukhtar ya dubi qanen nasa yace "kozaka biyomu ne asibiti qanena?" cikin mamaki baba Ismail yace"waye babu lpia yayana?" dady salis ya amshe dacewa"Hjy furdauseey CE amman jikin yayi sauqi" dady mukhtar yace "dan khaleepa ma yace zata iya dawowa gidan yau'' Allah sarki Nan take baba Ismail yamiqe, mutum mai sanyi hali dan Sam baituno rashin mutuncin Hjy furdauseey ba amman yadubi mama Zainab yace jeki maman heenduh ki dauko mayafinki mutafi ganota tare..dady mukhtar yace"dama kabarta qanena" girgiza kai baba Ismail yai yace"ai dubiya CE yayana bakomi"hakan kuwa mama Zainab tahado kayan abinci tasaka a basket sannan sukatafi harda heenduh ma. Suna isa dakin da Hjy furdauseey din take nan suka iske Hjy Hadeeza harda zarah sai khaleepa dake zaune gefe momyn tasa yana bata ruwan tea a tea spoon zuwa cikin bakinta da Allah ya temaketa yadawo daidai daga gurmud'ewar dayai hakama kuma hannunta yadawo daidai shima. Hjy fuedauseey naganin yanda dady mukhtar yariqo hannun baba Ismail tuni zuciyarta ta tsinke babu shiri ta qware da tea din bakinta dan ganin abun take Uwa a mafarki. "sannu Hjy" suka hau mata yayinda dud rabin hankalin doctor kega heenduh dayaga sai faman kumburi take tana cika tana batsewa wanda shi yakasa gane dalilin hakan, yayinda a bangaren heenduh ba komi ne yajaza mata hakanba face ganin zarah datai kusada shi. nanko suka hau bankawa junansu harara a boye itada zaran kowace kishi na cinta dankuwa Hjy furdauseey tafada musu komi yafaru dangane da mgnr cikin heenduh tun kamin shigowan khaleepa ma dakin tana fada musu tana kuka , lokacin cikin dabara Hjy Hadeeza tadinga kwatanta mata da tabar tada hankalinta inyaso in sun koma gida sasan abinyi . shiyasa koda su baba Ismail sukai mata yajiki kadaran kadahan ta amsa musu wato a daqile babu yabo babu fallasa. danzuwa yanzun kam tashaida haduwan kawunansu da junansu yadawo. jitake uwa tai hauka ko lokacin. sosai khaleepa yakeson kebawa da sugarn tasa sai alama yake mata da 'ido amman sai faman sake daure masa fuska take tanashan qamshi, yayinda Hjy furdauseey taqurawa cikin heenduh ido tanaji Uwa ta tausheta taita bugun cikin harsaita mutu snn zata barta. dan dai kawai rashin imani kalar na hjy firdauseey. dole khaleepa yahaqura kuwa badon yasoba ganin dayai lollipop din tasa Asama take
Chapter 141 · 0% Book details