← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 178

Sashe 52

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

tace "ke rufa mana asiri mu mutu maza su kaimu tomu kam mahaukatan inane dahar zamu fita anguwar nan haka da take cike da sa'idinawa? After dressing zaki saka ko hijab in yaso ma cire in mun isa wajen" sa'a tace"aho yanzun naji Batu ay" nan heendu ta maida baqar doguwar rigar jallabiyarta saman kayan kamar dai yanda ta shigo, itama sa'a ta saka doguwar hijab dinta sannan suka d'auki jukkunansu suka kulle gidan suka tsaida napek suka shiga suka tafi. sun dan jima sannan suka isa wajen da ake partyn, wani qaton waje ne an qawata sa bnda casu babu abunda kakeji na tashi wajen sannan kuma can gefe motoci ne na alfarma wanda samarin wajen suka zo dasu, heenduh sarkin son rawa harta fara taku a napek kuwa, daman tun a napek suka cire kayan da suka daura akai tareda cusasu cikin jukkunnan suka zuge. nan suka daura wani matacin gyalensu wanda 'yan matan kewa laq'abi da *'uryatin* akai, wnda iyakarsa wuya nan sukai rolling dashi suka tasarwa shiga hall din suna taku d'ai d'ai suka samu waje gefen amarya inda shauran class mates dinsu suke suka zauna tareda sauran qawayen amaryar kowace naji da knta wajen,saidai kuma heendu abinda ta tsana ai mata wato kallo shi samarin wajen kuwa suka tasata dashi harta fara tunanin barin wajen amman da aka saki wani kidan sai tsintar knta tayi a filin rawar tana riqe da sa'a suke takawa cikin yangarsu ta mata isassu. kan kace mi tuni aka fara musu ruwan liqe fiyeda sauran matan dake wajen tuni wajen ya dauki tafi raf raf harda amarya da ango kuwa saida suka tafawa salon heendu,, saida heendu ta gaji sannan dan knta ta koma mazauninta yayinda kowane saurayi keson mata mgn amman ganun basu samu damar yin hkn bane daga fuskarta yasasu kallon nesa nesa da ita dan su azatonsu yar mnya ce ko gidan sarauta yanayin takunta da shan qamshinta, mamaki ne ko al'ajabi koko idanunsa ne suke masa gizon itace koko mai kama da itace a kalar wannan wajen?? tambayar da doctor khaleepa kewa kansa knn tun lokacin da su heendu suka shigo hall din nan itada sa'a, bai qara tsinkewa da itacen bane saida yaga yanda take juyin rawa in slowly, yayi matuqar mamakin miya kawo ta nan bikin friend dinsa ashir kabeer? duban inda yake zaune yai can qarshen chairs ya zauna sakamakon alfarmar daya nema daga abokin nasa na cewa nan zai zauna saboda hatsaniyar wurin tabbas yasan zata haifar masa da ciwon kai, shi sam iriyar wannan wuraren ba zuwansu yake ba, danshi baida son ma hayaniya at all a rayuwar sa, sanin halinsa yasa Ango ashir amincewa daya koma bayan ya zauna kamar yanda ya keso dudda yaso ya zauna kusa dashi din kamar yanda aka tsarawa manyan abokan ango da na amarya. wani murmushin takaici ya saki ganin kalar kayan data sa har tazo cikin wannan qattin tana gwatse gwatse, shin mama tasan da hakan kuwa? tambayar dayaiwa zuciyar sa knn, lumshe idanuwa yayi bayan ya cire farin medical glass dinsu na likitoci tareda sake jawo preesing cap dinsa gaba ya rufe rabin fuskarsa, tun zmnsa awajen yayi hakan gudun shawagin 'yan mata a kansa shiyasa ya rufe rabin fuskar tasa daga kishin giden da yake, kur6ar juice d'inda ke hannunsa yayi bayan ya dubi agogon hannunsa yaga duhu ya fara, dan tsoki yaja tareda qara watsa idanunsa gunda heendu suke zaune, sake d'auke fuskarsa yayi danji yai gaba daya zaman wajen ya ishesa shiyasa kai tsaye ya miqe tsaye tareda komawa cikin motarsa bai tintec glass ya kwanta tareda kunna ac sbd zafin dayaji na ratsa sa, ganin kiran ashir kabeer ango, saida yad'an motsa sannan ya zaro wayar daga jeans d'insa sannan ya d'aga tunkan yace wani abu ashir yace "haba *likitan mata* yaya ana tsaka da friends event kuma zaka fita ina kallon kafa, snn ga kuma manyan babies cike a wuri please man ka dawo ka bayyana musu kanka nasan dole ladies su girgiza in sunsan da kalar ku wajen nan dan AllAh ka dawo man"saida ya muskuta tareda saka ear pies a kunnen sa yace "no ashir bazan iya zama wajen nan ba amman nai maka alq'awalin ina cikin wajen nan har sai an tashi partyn nan sannan znwuce ok? dole ashir ya haqura badon yaso ba sanin dayai cewa indai khaleepan yai mgn babu canjawa bare qarya a cikinta. haka waje ya cigaba da, kasancewa har wajen qarfe tara sannnan aka tashi, nn samari suka fara daukar yan matan suna wucewa dasu gidajensu. qwarai sa'a tai mamakin badai tafiya heendu taifa ta barta ba? dan daman tun dazun take zanzamin su tafi kada mama tai fad'a gashi har goma na shirin idawa. taji haushi kam ynda har tatafi ta barta gashi kuma tabar mata jikku nansu a hannunta. "badai haka ta koma gida ba da kayan jikin nata ba? tambayar da sa'a taiwa knta knn a mamakance. yanzun kam ta tabbas cewa kam heenduh ta wuce abinta kuma ganin saura ita d'ai ya rage tsaye bata shiga motocin da 'yan matan keta shiga ba suna tafiya a wajen yasata shiga itama suka tafi nan kuwa waje ya koma ba kowa kamar ba'a ta6a taron jama'a wajen ba kuwa, gashi hasken gun ma ba wani wadatacce ba ne sosai. su sa'a basufi minti biyar ba da barin wajen saiga heendu ta 6ullo ta wani d'an lambu hannunta riqe da mango dayake tana matuqar son mangwaro shiyasa tana ganin dj din wajen ya gama bayanin komi angama har an fara shirin daukar mutane ma. mafarin knn taje tsinkosa ganin ynda yayo qasa qasa alamum basai tasha wahalar curo wa ba, dan ita harga Allah sam tama mnta da an fara tafiya shiyasa ta zauna nan taita shan mangwaro wajen guda uku manya manya, tana gamawa ne taje wajen famfo ta wanke hannunta tareda qara tsunko d'aya ta ruq'osa a hannunta tareda nufin kaiwa mamanta itama. wayam taga wajen tuni ko tsoro ya baibayeta ta dora hannunta a knta tareda cewa "wayyoni heenduh na shiga ukku na"!!! abinka gamai saurin kuka tuni idanunta suka fara kawo ruwa ganin koda nan ma knta isa titi ba qaramin nesa ne da wajen ba. kife kanta tai a cinyoyin ta tana tsinewa sa'a a ckn zuciyar ta na tafiyar mata da kaya datai a jakkarta, yanzun haka zata doshi hnya har gida da wannan shigar kamar 'yar good evening sai kace wata karuwa? tunanin da take a ranta knn, jin haushin kare ne data jiyo a wani wari nn kurkusa yasata zabura ta miqe taresa barin wajen cikin sauri 2 gudu 2 tana waiwaye gabnta na dakuwa da qarfi na tsabar tsoro. hango mutum da rayi ya nufi mota hannunsa dauke da wani abu ya saka bayan motar dake kusa dashi ga alama motar tasa ce kuma tafiya zaiyi shima. dudda bataga fuskarsa ba amnan da gudu ta isa wajen, (doctor khaleepa ne ya samu wani haraban tsaftacaccen guri tun bayan da aka kira sllr magrib bai baro wajen ba saida yai isha'e yana nn zaune saida yaji kidan ya rage sann ya nado abun sallar tasa ya tafo, yayi mamakin ynda yaga har an tashi duba wayarsa yayi da ake kira tun lokcn d yake sllr saiyaga har 12 missed cull daga ashir 3 kuma daga momynsa sai 2 daga yunus, bai maida reply na kiran ba ya nufi motar kawai tareda saka pray mate din a set back), yana qoqarin shiga motar ne yaji murya a bayansa ta mace tana cewa "mlm dan AllAh ka taimaka ka kaini gd wlg bn samu abun haw....... tuni heenduh ta kasa qarasa mgnr tata ganin wnda batai mamaki ba awajen ne, wani dad'i taji ya ziyarceta har tana sauke ajiyar zuciya na ganin komi ya zo mata cikin sauqi, cikin murna tace "laaa doctor kaine nan daman.... shiru tai ganin wani mugun kallo na qyama da tsana da yake wurgo mata,, ita ba abun tace zata rama ba tai masa rashin kunya ba yaqi daukarta dole ne ta kwantar dakai kota samu ya temaka matan, jitai yace "Allah ya sawaqa da in d'auki qazanta najasa kamarki a cikin motata, saidai ki kwana anan inhar kuwa saina d'aukeki marar kunyar qarya kawai mai watsi da tarbiyar iyaye" Qwarai ranta inyai dubu toya baci amman babu ynda zatayi tanaji tana gani ya dinga daddatsa mata munanan magan ganu masu zafin gaske amman kuma tayi shiru fuskarta na kallonsa tasa idanunta na tsiyayar da qwalla gwanin tausayi, dan tuni bakin masifar nata ya mutu dud tsoro ya baibayeta wajen, tabbas yau tasan khaleepa bai sonta yanzun ganin datai yana shirin shiga motarsa ya barta wajen aiko da gudu cikin kuka ta aza qirjinta saman bayansa ta had'esu gam gam tareda q'amqamesa tana gunjin kuka tace "wlh doctor ko zaka kasheni bazan bari ka tafi ka barni wajen nan ba saidai komi zaka mun kamun shi nina d'aukarwa raina shi yanzun nan"!!! tayi maganar tana qara cuccusa kanta da jikinta a bayansa hannuwanta zagaye saman cikinsa duka, hawaye sun mata kaca kaca a fuska jikinta ko ina rawa yake kamar zata katse takeji a lokacin kuwa,,.....,
Chapter 52 · 0% Book details