← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 178

Sashe 77

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

👁🥡👁 🅿3⃣8⃣. *S* hiko baba Ismail murmushi yayi bayan wanke hannunsa da ya gamayi cikin wata roba ta daban, sannan ya sake duban heenduh cikin wani sabon murmushi nasa yace"heenduh na kada ki dad'e tashi kije inda kinji maman ki tana mana canca kwato bayan zumuncin dare zamu" yayi maganar cikin tsokanar mama Zainab din. da murnar b'oye heenduh ta miqe tace"danaje bazan jimaba ai babana" shima baba Ismail miqewa yayi yace "dole nema ai kiji kewa heenduh na inda sa'an ki tai nisa damu dan dama itace abokiyar firan daren naki, nima jirani mu fita tare dan dan leqa gidan baba yawale daga nan na wuce majalasin mu" marairaicewa mama Zainab tai ta dubi baba Ismail tace"yanzun kaima fitan zakayi? ni kadai a gida kamar wacce ba'aso? kan baba Ismail yayi mgn wayar heenduh dake daki ta shiga ringing da sauri heenduh tabar wajen zuwa daki, hakan yabawa baba Ismail damar kamo hannuwan mama Zainab ya dan sumb'acesu sannan yace "wayace miki ba'a sonki matas? ke bakison yawan son da nike miki ne yahanani hangen wata ba? cikin jin dadi mama Zainab ta dan sumbaci hannun baba Ismail tace "soyyarka gareni fiye mun komi take na rayuwa da hakan ne nima nike son amun alfarma naje wajen mama na na dubota" "An miki alfarma uwar gidan isma'il adawo lpia" rufe idanunta mama Zainab tayi sannan ta budesu cikin jin dadi tace"ngd mijina abin alfahari na, ina roqon ubangiji Allah yanda kai mana wannan alfarmar Allah yayi mana alfarmar ganin shumiryawarku kaida d'an uwanka Yaya mukhtar shiryawa ta muddin rai kuma!" saida gaban Baba Ismail ya d'an buga dammmm!!! kafin ya iya sauke ajiyar zuciya bayan zare hannunsa daga cikin natan dayai sannan ya furta da cewa"Ameen, dauko mayafin naki saimu fita tare ko..... kamin ya ida maganar tasa saiga wani yaro yayi sallama. dubansa Baba Ismail yayi bayan amsa sallamar dayai yaron mai suna imam yace "baba wai ana sallama a waje" baba Ismail yace ''imam Kasan mai sallamar ne? Kuma wayace ka Kira masa a gidan? imam yarone mai wayau ga surutu rairai abinda ma ba'a tambayesa ba sai yace. dan haka yace "bansan yaba baba amman yace ince mai gidan zan kira masa kaga harma ya bani sweet ma mai dad'i inasha, amman d'an babba ne mutumin fa baba dan zaiyi sa'an kawunka mai gidan kud'in can ma (yana nufun mukhtar) kuma harda ma motarsa yazo babba qatuwa sabuwa full" murmushi mama Zainab da baba Ismail sukai na surutun imam heenduh data fito daga daki bayan gama wayarta datai da musaddiq yana cemata yashigo gari kozatai masa alfarmar ganinta?take ta basa amsa da cewa a'a tana aiki ne saidai zai iya shigowa gobe,, amman haka yaita mata nacin dan Allah koda basuyi fira ba shi ta taimaka masa ma ko leqowa ne tayi yaga kykkyawar fuskarta dayaketa mafarki amman ta kafe dai a'an, dole ya haqura badan yaso ba Inda tai masa alqawalin tura masa sabbin pics nata sannan ne hankalinsa ya kwanta haka ta fito dakin zuciyarta na mata saqe saqe na yaya tarayyarsu da musasdiq zata cigaba kuwa inda tasan a matsayin matar wani take kuwa? da wannan tunanun ne ta fito ta iske kalar surutun da imam kewa su baba Ismail din. tsoki tai bayan ta kalli agogon wayar taga har 8 da 28 na dare. girgiza kai baba Ismail yayi ya sake duban imam yace ''naji ya isa haka fad'i ba'a tambayeka ba jeka kace masa gani nan ina zuwa." haka imam ya fita shima baba Ismail ya daura takalman sa tareda saka hularsa yaqara kuskure bakinsa da ruwan butarsa sannan ya fita. Wanda ya ganine jingine jikin motarsa tareda wata 'yar matashiyar yarinya riqe da hannunsa ba qaramin girgiza da mamaki yayi ba. da sauri baba Ismail ya qarasa wajen mutumin suka rungume juna saiga baba Ismail na fiddo hawaye na tunano dad'ddan rayuwarsu da sukai dashi da dan uwansa tunkan komi ya hautsine musu da mukhtar yayansa. da qyar yadago kansa ya sake dubansa cikin rawar murya baba Ismail yace"Yaya salis kaine yau nagani koko dai mafarki nike? murmushi salis yayi bayan ya share hawayen fuskar daya gani na Ismail yace"nine qanenmu shekaru da yawa ko? cikin Myrna matuqa baba Ismail yace"kashigo man yaya saika tsaya waje maimakon kawai ka shigo bama saika aiko ba ....haka yai musu shinfida aka zazzauna mama Zainab ta gaishesa itama cikin mamakin ganinsa, heenduh ma ta gaishesa dudda bata sanshi ba amman saitaji mutimin yayi mata yanda taga yanada sakakkar fuska gamida kamala a yanayinsa, gashi yanda tashin farko baby (wato 'yar salis dinta liqewa zama kusada heenduh tanata mata surutu yarinyar mai kyau itama) sai riqe hannun heenduh take taqi sakinta kamar daman ta santa. heenduh kuwa jitai 'yar matashiyar yarinyar ta burgeta. anan bayan mama Zainab ta kawo musu ruwan randar su masu sanyi suka sha aka cigaba da gaisawa saidaga bisani fuskar salis ta d'an canza saboda tuno maganar dazaiyi baqaramin b'ata masa rai take ba dud inya tunota. dan tunda yazo garin a yammacin yau mamansa ta fad'a masa halinda mukhtar ya sauya na yanda yamaida d'an uwansa Ismail kare ma yafisa daraja gunsa, wanda hakan bai wuce har dasa hannun wannan hatsabibiyr matar tasa ba firdausey cewar Maman nasa. tun lokacin jikinsa yaji yana rawa dan bacin rai harma yanaji cewan a ransa inama mukhtar na qasar ayau dayaga dawane ido zai kallesa akan abunda yaiwa Ismail harya yunqura zai je gidan dan ciwa Hjy firdayseey mutunci dan dama bawai sonta yakeba tun usuli yakejin tsanarta, saida mamarsa ta kwantar masa da hankali da cewa komi a hankali ake binsa ya haqura har shi mukhtar din yadawo nanda sauran watanni 2 kamar yanda yace din sunyi waya ya fada masa. amman kuma sosai yayi mamakin yanda mukhtar babu ranar da ba zasuyi waya ba da junansu ba amman ko kusa koda wasa bai taba fada masa abunda ke faruwa ba tsakanin junansu wato shida qanen nasa Ismail. amman ya yanke hukuncin bazaice komi ba harsai shi abokin mgnr tasa ya dawo sannan zaiji dalilin faruwar hakan dan yana ganin wannan qasqantanciyar maciyar amana kamar firdausey batakai harya tsaya yana challange na maganganu da itaba dan ji yake inta fada masa maras dadi zai iya saka hannu ya maketa wajen a matsayinsa kuma na aminin mijinta kuma yakega hakan bazai kyautu ba, danko bakomi mijinta nasa ne shima kuma nasa ne kamar dai yanda suka taso, shiyasa ya d'aga mata q'afa har mukhtar d'in ya dawo sannan asan biri da gatansa. dan haka zuciya babu dad'i salis yasake duban Ismail yace"qanena naji abinda yafaru tsakaninka da d'an uwanka kuma ni wlh baitaba fadamun kalar zaman da kuke ba a tsakanin Ku....shuru yai dan ciwon abun still yaqi Barin ransa, sakin huci yayi mai zafi sannan yaci gaba da cewa''Amman inda gani na dawo yanzun komi zai yaye cikin yardar ubangiji saina kawo qarshen al'amarin hatsabibiyar makirar matar nan tasa dan inada confidance wannan halayen bana abokina bane an cusa masa sune a ransa ina nan ina jiran dawowarsa sannan mun hadu dashi ga da ga zamuyi mgnr kada kudamu insha Allah matsalar ta yanke zaku dawo fiye dada kaida yayanka da yardar ubangiji Allah wannan alq'awali ne qanenmu"!. Cikin murmushin qarfin hali baba Ismail yace "mungode Yaya salis Allah shi amnice" yayi maganar zuciya a kare dan yana ganin yanda yayansa nan yai nisa a q'insu da tsanarsu babu abinda zai canza, to kuma saiyai la'akari da dud kowane tsanani da wahala Indai aka saka Allan a ciki tofa tabbas abin zai shanye tsab yadawo normal komin kuwa kalar cukurkudewar qulle qullen sa kuwa. duka wajen suka amsa da "aminn". saida zuciyarsu tai sanyi sannan baba Ismail ya kalli baby sannan ya dubi salis yace''Yaya salis wannan 'yar mu ce amman dai ko?dannaga kama" rai a d'an sake salis yace "eh aminatu ce amman anfi kiranta da baby amnat, kaganta nan kuwa fitinanniya ce ko'ina zanyi saita liqemun". dariya sukai sannan mama Zainab tace "aiko dai da gaskiar ta dan garin bata saba dashi ba." baba Ismail cikin murmushi yace "gskia kam saidai a hankali zata saba a cikinsa inda tadawo zama parmanet a cikinsa" jisukai tsulum baby amnat tace"nidai dady ka tafi man da wannan Aunty mai kyau a gida dan tana da kyau kuma ina sonta". dariyar shirmen baby amnat salis yayi bayan ya kalli heenduh yace''to 'yata kinji abunda qanwar ki tace zaki yarda kibimu gidanmu? baby amnat ta amshe da cewa"pleases Aunty mai kyau muje gidanmu momy na ta ganki Momy nama tanason abu mai cau dan ita na biyo nima wannan habitats". d'an sanyayyen murmushi heenduh tai mata takamo hannunta tace"zanje gidanku amman ba yauba baby amnat na" sosai baby amnat taita murna hadda maqale jikin dadynta salis su dankusu suna mata dariya. sai wajen tara saura sannan dady salis ya tashi zasu tafi bayan ya ajiyewa baba Ismail kudi masu yawa tareda cewa tsarabarsu nanan tafe,, dan har a ran salis ya tausayawa Ismail ganin halin dasuke ciki na buqatar temako Amman inda ya dawo yanzun insha Allah yana ganin Ismail yagama kukan babu dan yanaso ma su zauna su tattauna yanda zai canza masa Sana'a ta hanyar basa isasshen jari mai kauri yanda shima zai tsaya da qafanunsa sosai. saida baba Ismail yakai salis har gidan baba yawale kamar yanda salis ya nema, nan suka iske baba yawale suka gaisa da maganar yaushe gamo, dazai tafi yai masa alheri shima sannan suka rakosu har mota baby amnat nawa heenduh bye bye har suka bace. ganin tara har tayi yasa mama Zainab fasa zuwa gidan nasu da niyar gobe da safe taje yayinda shi kuma baba Ismail ya wuce majalasin su . ganin mama Zainab tayi gaba hakan yasa heendu tai niyyar shiga gidan baba dahara danta samu ta lab'e koda zauren gidan ne intaga maman nata ta shiga gida saita fito ita kuma ta tafi. ganin mama Zainab ta juyo yasata d'an dakatawa gabanta na d'an bugu bugu na tsoron hanata zuwa dan tara tadan gitta isuwan yanzun. mama Zainab tace"shin wai dan Allah bazaki haqura ba heenduh da zuwa gidan baba dahara sai gobe in Allah ya kai mana ranmu ba? sam batason yawan musuawa maman nata dudda ranta baiso kuwa haka tabi
Chapter 77 · 0% Book details