← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 178

Sashe 19

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

👁🥡👁 🅿1⃣3⃣. *B* affa dai shiru yayi bai ce komi ba kuwa sai zuwa can yace"dole ne daman adinga yiwa mutum uzuri a rayuwa mukhtar bare ita da dalilinta ma mai qarfi ne dan saida lpia ake iya aikata komi" inno ta ce "hakane mlm mudai adduarmu Allah ya sauketa lpia itada Zainabu inda inaga ai dud ma kusan lokaci daya ne haihuwar tasu zai kama" "aminn dai" inji baffa. mukhtar yace "baffa ko kana da wanda zaka bawa kujarar ne danni bnsnma wanda zan tattago yanzun cikin qurarren lokacin nan ba baiyi latti ba, dadai salis nanan saina kirasa ko exchange na kaya sai muyi a jakana to gashi bai gari kuma" baffa yace "to Masha Allah lallikam bawa baya ci sai rabonsa ka bawa babanka yawale itan saimu tafi tare, sai kaje kai masa bayani dan daman bamu jima da rabuwa dashi ba yanzun yana gida". inno kanta tayiwa baba yawale murna itama, haka mukhtar yaje yasamu baba yawale a gida yai masa bayanin tafiyarsu mecca nanda lokaci kadan, Allah sarki saiga baba yawale yana kukan farincikin yake shirya wasu 'yan kayansa yanata yiwa mukhtar addua da fatan gamawa da iyayen sa da duniya lpia da arziq'in mai d'aurewa. sai gashi babu jimawa baba yawale yagama parking d'insa nan mukhtar yakira yaransa wani daga cikin yaransa na ma'aikatarsu kan yakawo musu mota yanzun zai kaisu airport, kan ado masinger yazo har sungama kimtsawa su baffa da Ismail da zainab nan sukaita shisshiga maqotansu suna yi musu sallama babu jimawa ado yazo nan suka sanya kayansu a booth suma suka shiga motar zuwa camp d'in alhazai, jama'ar dake tsaye dan ganin tafiyar tasu sukaita d'aga musu hannu tareda fatan alheri har sai da sukaga motar tasu ta 6ace daga titin anguwar tasu sannan suka koma gidajensu cike da sha'awar ahalin. koda suka isa airport babu jimawa jirginsu yafara yin louding batareda 6ata lokaci ba komi ya kammala cikin yardar Allah suka d'aga zuwa q'asa mai tsarki. Meron tsimbe kuwa kamar jira take subar airport d'in dan sune 'yan rakiya, daga nan sukayi shatar mota sai qauyen 'yan maraya. dole suka cewa mai motar ya ajiyesu nan gefen hnyar da zata sadasu da inda gidan boka marakusa yake dan mota bata isa wajen. tafiya suke cikin duhuwar tsaunukan kamar ba'a jeba, sunyi tafiya sosai sannan suka fita daga cikin duhuwar bedukan basu qara wata tafiya mai tsawo ba kuwa sai gasu tsaye dai dai bukkar boka marakusa wanda wajen ke kamar bola sakamakon tarin tulin kayan q'azantar dake danq'are a wajen. meron tsimbe ta dubi 'yar tata tace "ke anya kuwa dai firdauseey marakusa na nan dan banji alamunsa ba wajen... kan ta qarasa ida maganar tata sukaji an wani qyqyace musu da wata iriyar qaqqafar dariya mai ban tsoro wacce gaba d'aya saida dajin ya amsa da wata iriyar kuwwa mai tartsatsi, Ai babu shiri su meron tsimbe suka zube wajen tareda qanqame juna itada firdauseey, sai ihun kuka suke dn harga AllAh saura kad'an subar hayyacinsu dan tsoro da firgici. a qalla sun d'auki sama da mintuna ashirun da biyar sannan sukaji an tsagaita da dariyar ance "marmaza ku juyo nan dangin shed'an ubana" ai kuwa babu shiri a gaggauce suka juyo har suna karo da fuskokin juna suka ida zubewa a q'asa sosai sukai zaman dirshan. wata dariyar ya qara kecewa musu da ita sannan yace "kai ku natsu sosai dan dud wani mutum mai tsoro da kuma d'an 6urbushin imani baya zama inwa d'aya da marakusa bokayen hatsabiban duniya." dole suka nutsu suka daina kyarman jin muryarsa da kuma gamdakatar da sukayi da mummanar suffarsa marar kasa misiltuwa. meron tsimbe ta bude baki knn da shirin yi masa bayanin abinda ya kawosu wajen taga ya d'aga mata hannu yace "dakata ja'ira in kika kuskura kika ce uffan gameda abinda ke tafe daku sai d'an tsimbirbirin aljani yaci q'aniyarki kuwa, dan bai son ai masa shisshigi a lamarin kai saqonsa dan dud wanda yazo nan shike fad'a mana matsalarsa bawai sai kai ka fad'a ba da bakinka ba" tuni meron tsimbe tai saurin datse bakinta har tana datsewa da harshenta wajen rufewa aikuwa babu shiri tasaki wani d'an marayan fitsari daga nan inda take yashe a zaune kamar mai neman gafara, ga mamakinsu sukaji boka na zayyano musu bayani akan mukhtar a inda yake cewa "ku arna kunzo nan da buqatar a shafe muku tunanin mukhtar mijin firdauseey daga kan ahalinsa da kowa nasa gamida sa musu zazzafar q'iyayyar su a ransa yazamana bazaije wajensu ba da alheri face sherri shima kuma babu wanda zaije wajensa yayi masa wata alfarma, sannan ya zamana sai abunda matarsa ta umarcesa zaiyi koba haka ne buqatar taku ba?" cikin rawar vaki suka dinga cewa "e... eh e... marakusa hakane" 6at sukaga ya 6ace sun daina ganinsa babu abunda yaci gaba da tashi a wajen kuwa face dariyarsa,wannan karon hatta d'an dake cikin cikin firdauseey saida ya hautsina dan firgita aikuwa ta dafe cikin tana faman "wash2"!!! na azaba, gani sukayi walll!!! bokan ya dawo kamar walqiya ya dawo zaune a inda ya 6ace, hakan yasa tayi saurin danne ciwon jin yana cewa "munan magani d'aya rak muke badawa ba'ai mana jeka ka dawo dan mun yarda da maganinmu" gani sukayi ya bud'e tafin hannunsa babu komi a cikinsa ya turasa cikin wani makeken kunnensa sai gashi ya fiddo wani ganyen magani qwara daya yana cigava da tofa wasu d'asimai na suddabaru akan ganyen sai sukaga ya wurgasa a sama ya6ace 6at ganyen, amman a haka bokan ya dinga sambatu idanunsa na'a rufe bayan ya dantsi k'asa dake wajen ya watsa ta a sama saiga ganyen nan ya dawo k'ulle cikin wata farar leda d'anye shakab dashi ya juyo ya miqawa firdauseey yace "ungo nan wannan ki tabbatar dud sanda ya dawo qasar nan inda tsumvirbiri yace mana bai nan to dud sanda ya dawo ki tabbatar kinsa masa sanwa da wannan ganyen a ciki yaci sa" cikin rawar baki firdauseey tace "to boka ganyen bazai yi komi ba in aka dafa san knn? tsawa ya daka mata yaxe "ke!! kul!! kada ki mana zancen iska anan kinji ko?'' "kayi haquri boka" cewar meron tsimbe tanawa firdauseey daquwa ta cikin gyalenta akan ta kiyaye harshenta. boka yace "wannan ganyen da kike gani koda zaiyi shekara talatin kina sanwa dashi bazai canza ba, abinda yasa nace kiyi masa sanwa dashi kuwa shine sabida maganinki na jikinsa, dazarar kina sanwa dashi a abincinsa tofa sihirin zai dinga bin jikinsa a hankalin harya girmana, yanda zakiyi amfani dashi kuwa shine inya dawo zakiyi masa sanwa dashi tsawon kwana uku to daga nan saiki saka ganyen a cikin masai to nan d'an tsimbirbirin ajlanina zaije ya d'auko manshi ya kawo mun, kinsan shi a wajen najasa yake rayuwa, shikenan faqat aikinki yaqare dan wannan sihirin indai ya cisa saiya dauki tsawon shekaru da yawa bai sakesa ba dazarar kuwa kinga alamun zai sakesa kiyi marmaza ki dawo nan saimu qara baki irinsa, Hahahahahaha!!! bokan yasake kecewa da wata dariya sannan yace "ku ajiye mana kud'in anan ku wuce arna banza ga wasu cotumers din na nan tafowa" jiki na rawa firdauseey ta bude jikka ta d'auko damen kud'i 'yan dubu dubu guda 3 ta ajiye suka tashi suka bar wajen da tafiya da jan qugu kamar yanda marakusa ya umarcesu dan haka yakeyiwa dud wani wanda yazo kuwa wajensa indai zai tafi to saiya nad'e buje dajan qugu yake varin wurin dud nisansa kuwa gashi kuma wajen da qayoyin gaske shiyasa dud saida suka jimasu ciwo musamma ma firdauseey da batta iya d'aga jikinta sosai sakamakon cikin dake jikinta. haka suka fito waje suka iso har inda motar taxi dinnan tasu take suka shiga daqyar suka d'osa na dan duwawukan dud sun farfashe musu a hanya dan azaba. kai tsaye gidan mlm zayyanu mai taxi din nn ya tsaya sakamakon gwada masa matsaya da meron tayi nan suka biyasa suka wuce cikin gidan. mlm zayyanu yana salla nn waje suka wucesa kawai suka qarasa cikin gidan. dasauri firdauseey ta dauki bokitin ruwa da kwandon sabulu tayi bayi dan qyanqyamin daudar da ta kwaso takeji a jikinta. maman zainab ce dake sanwa tsakar gida ta lura da yanda zanen mero ya 6aci da jini daidai inda qayoyin nn suka sossoke mata d'uwayyu tace "yaya meri jini a jikinki kije ki gyara knki" dan ita harga AllAh maman zainab tasa jinin al'ada ne mero keyi basaan na masifa bane kuwa. dan haka mero tace a fusace''emhem to 'yar sa ido bazan gyaran ba, nace bazan gyaran ba, ah kujimin mata dan allah da kafirin sa idon tsiya, uwarwa yakai kallonki kan d'uwawukan nawa eye ma?" "Allah baki haquri" cewar Maman Zainab d'in tana ida kashe wutar girkin danya dafu dama alwala tayi tanufi d'aki dan tayi salla, aiko mero ta bita da cewa"matsitaciya ahaka dai zaki q'are wajen kinbibin tsiya, ke ni nafa lura ma da cewa tun sanda aka ce anba 'yarki kujerar mecca kike tada wa mutane hanci a gidannan to bari kiji billaheel azeem kinyi kad'an kice zaki raina mun wayau a gidan nan, ta dadin abunma a jikin sirikina meccan ta fito matsiyata kawai" itadai ko kallonta maman zainab bata sake yiba fad'i take aranta "AllAh dai shi shiryaku in masu shiryuwar ne, in kuma akasin hakan ne to AllAh yai mana maganinku ya shiga tsakanin na gari da mugu". koda firdauseey ta fito daga kewaye daqyar tana nishi ta shiga d'akin uwar ta zauna. itama mairo batayi qasa a gwiba ta shige kewayen ta gyara jikinta sannan ta fito, ta shigo d'akin ta zauna tareda fad'in "washh kai komi zaka nema a duniya saika sha azaba wlh"! firdauseey data fara samun dama dama a jikinta ta dago kai ta dubi uwar tace "bagashi mun samun ba mama, ai daman ance bayan wuta sai dad'i ay, to ynxun wuyar ta yanke dad'in ne ke zuwa mana" mero tace "hakane gaskiyarkin nan" firddausy tace "hmm wlh mama jinake uwa inje in dawo dasu nafara gudanar da aikina tun yanzun" meron ta dago daga shan ruwan faro dinda ta keyi tace "tukunna tukun dai mai saurin kuka ai bazai shiga gasar shad'i ba" nan suka raba dare basuyi barci ba suna faman maganar yanda al'amarin
Chapter 19 · 0% Book details