← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 174 OF 178

Sashe 174

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

👁🥡👁 🅿7⃣0⃣. *K* ai tsaye khaleepa gate d'in gidansu yaiwa tsinke, saidai ya samu gidan datse, babu bata lokaci cikin kasala da mutuwar jiki yajuya kan motor xuwa gidan mlm zayyanu mijin mahaifiyarta in Baku mnta ba, umarnin baba yawale knn daya cewa khaleepa aje da gawar can,,, sosai mlm zayyanu da mama jameela suka girgiza da ganin kalar da mutuwar fursaurseey tai mai kamanceceniya data uwarta,, Allah shi jiqan rai abinda sukace knn. shidai khaleepa yana jingine da kansa jikin hjy furdauseey jiyayi kukan ma ko dad'i baya masa, shiyasa banda faman had'iyar zuciya dayake bayya komi, ga kansa daya kaji uwa zaibar gangar jikinsa tsabar ciwo da yake masa,, daga nan su baba yawale suka koma gidan baba isma'il wanda anan suka iske daddy mukhtar d'in shida baba isma'il, kaida ganinsu kasan maganar jiya ta marigayya hjy furdaurseey bata sake suba, hatta heenduh datazo gidan a safiyar yau a gigice sakamon baba dahara dataje ta tafo da'ita saida ta tausayawa doctor din nata ganin kallon datai masa harya rame sosai tsakanin jiya da yau kamar wanda yayi rashin lpia,, kara kwanciya tai bisa qafar mama zainab tana zubar da qwallan tausayin khaleepa, musamman ma dataji su baba yawale na shaida musu mutuwar hjy furdauseey d'in, amman ko gezau daga dady mukhtar har baba isma'il babu wanda yayi, bare suyi yunqurin shirin karbar taaziyarta,, saida baba yawale ya kwatanta musu da cewa duniya sai Ana haqure mata,har yaci gaba da nusar dasu harda dan nuna musu bacin ransa sannan fa suka yarda aka fara sanarwa da jama'a jana'izar..... qarfe d'aya na rana dai dai aka dawo daga kai hjy furdauseey makwancinta, mutane sai qushin qushin ake na yanda wajen saka hjy furdauseey cikin qabarinta saida aka sha dagar duniya sannan gawar tata ta zauna daidai. ko zama ta'axiyar ma saidan saboda baba yawale yasa su dady mukhtar suka zauna suna amsa gaisuwa, wanda a haka suka share tsawon sati d'aya sannan aka daina zaman kowa ya kama gabansa. wasa wasa saida khaleepa da heenduh suka kwashe wajen wata daya a gidan mama zainab, dan cewar da baba isma'il yayi da khaleepa d'in daya zauna nan wajen nasu kan jikinsa ya qara dayayewa sakamon rashin lafiya ta tashin hankalin dole data durar masa, dan tuni dady mukhtar da baba isma'il da dady salis suka juma da komawa a bakin aikinsu. a daren yau ta kama juma'a, heenduh na zaune cikin dakinta nada wato na gidansu, tana hada 'yan kayanta tana sawa a cikin akwati dan gobe ne khaleepa yace ta shirya zasu koma gidansu. tana tsaka da zuge zip d'in jikkar ne taji motsin shigowar khaleepa d'in, ya tsaya nan waje yana gaisar da mama zainab, da saurin ta ida miqewa tsaye tana qoqarin fita wajen itama, to anan sukaci Karo da juna har tana fadawa cikin qirjinsa, tallafota yayi ya dawo da'ita cikin dakin ya zaunar da'ita a gefe gadon shi kuma ya kwanta a gadon tareda daura kansa saman k'afafunta dake zube a qasa,, kallon sa kawai take dan har ynxun tana ganin alamun damuwa a tattare dashi, ga alama har yanzun rashin mahaifiyarsa dayai baibar jikinsa ba, sosai take qara fahimtar hakan dan rashin son maganar sa yaqara nunkuwa akan da nunkin banunkin kuwa, qara zuba masa fararen idanunta dasuka qara haske sosai yanzun tayi, cikin tsabar tausayin sa tasaka hannunta a fuskarsa tana shafa sajensa cikin sigar rarrashi. sake rufe idanunsa yai yana sakin ajiyar zuciya kamun ya bud'e baki daqyar yafara da cewa "har yanzun abun na ta6amun zuciya lollipop, dud inna tuna da halayan da mahaifiyata ta gabatar dasu a cikin rayuwar ta, bud'e idanunsa yayi sosai ya zubesu ana heenduh yaci gaba da cewa" dawane kallo mutane ynxun zasu dinga yiwa family namu ynxun? zasuyi mana kallo ne na cewa mahaifiyata ta aikata munanan shukakkun abubuwane a cikin rayuwar ta data gabata ko?, girgiza kai yayi snn yace "wlh a halin ynxun lollipop natsani shiga cikin jama'a dan bansan wanne kallo zasu dinga yimun ba" yaqarashe yin mgnr cikin qunar zuciya tareda fitowar wani zazzafan hawaye daga idonsa na dama ba tareda da ya ankara ba,,, sosai taji idanunta itama sun cicciko da qwalla taf, amman dan ta kwantar masa da hankali nan tayi dubarar maidasu ciki taci gaba da shasshafa sajensa cikin dauriya tace "kadaina saka damuwan hakan doctor a ranka kada kakamu da wani ciwon kuma please, dan wlh inada tabbacin a mutanen waje babu wanda yasan da sirrin nan naku bare kuma a bibiyeku, namu dai shine mu dinga musu addu'a Allah ya rahamshesu cikin yafiyarsa da rahman sa" dudda zuciyar sa babu dad'i amman kalaman dayaji heenduh tayi masa saida suka sanyaya masa zuciya harya saki wani d'an murmushi kuwa, wanda rabon sa da koda murmushi ne kuwa tun da rasuwar mahaifiyar tasa. dan haka cikin sanyayyen murmushin sa gareta yake cewa "madalla da mata ta gari mai share hawayen mijinta tareda kore masa dud wata kalar damuwa data addabesa, Allah shi miki albarka matata" cikin murmushi tace "aminn mijina" a hankali kuma sai ta sunkuyo da fuskarta a saman tasa, anan tasa harshenta tana shanye masa qwallan gefen idon nasa, cikin mutuwar jiki ya lumshe idanunsa yana sakin wani ni'imtaccen murmushi kamun yamiqa hannuwansa yana shirin dannota cikin jikinsa knn suka jiyo muryar mama zainab a qofar dakin heenduhn tace "heenduh kuzo keda khaleepa ga baba yawale nan ya shigo yace yana son mgn damu dukkanmu, dan hatta su babanku yaya mukhtar suna can sit room ku kad'ai ake jira, kuyi maza ku tafo dan Allah" dasauri khaleepa ya watsattsake tareda saurin miqewa daga jikin heenduh snn yace "to mama gamu nan tafe ynxun muma insha Allah" mama zainab na wucewa itama heenduh tataso suka nufi sit room d'in baba isma'il itada khaleepa suna tafe jere da juna sai haskawa suke uwa zara da wata. suna shiga falon da sallama anan suka samu dady mukhtar da baba isma'il gamida dady sales sai kuma baba dahara dake gefen mama zainab, heenduh da khaleepa suna ganin taron saida gabansu ya fad'i dan basusan taron akanmi zaiyi mgn ba, wannan taron da suka gani babu abinda ya fad'o musu arai sai taron da akayi sanda shi khaleepa d'in ya dawo da heenduh daga gidan sa'a, dan haka kuwa jikinsu a sanyaye suka zauna bayan gaishe da iyayen nasu da sukayi. saida kowa ya d'an natsa ne sannan sukaga baba yawale ya d'ago yana sake kallon kowa na wajen fuskarsa cike da *Alhini* kamin yace "haqiqa nasan in kukaji abunda zai fito daga bakin nan nawa zakuyi mamakinsa qwarai haqqun, to saidai ba abin mmki bane rayuwa ce data gaji haka, babu kuma wanda na taba gayawa hakan bayaga aminina baffanku da matarsa inno, Allah jiqansu da rahman sa kuma aminn, kallon sa kawai dukkan mutanen wajen keyi na tunanin to wannan wanne kalar abu ne dazasuji daga bakin sa. murmushi baba yawale yayi snn yaci gaba da cewa "sama da shekaru 30 kenan rabona da garinmu mahaifata da kuma iyaye na da 'yan uwa gamida dangina" mamaki matuqa ya qara shiga zuqatan su, dan ko kusa koda wasa basu tab'a tsammanin cewa baba yawale nada *Ahali* ba, tun tashin su na quruciya kuwa, iyaka matarsa data rasu dashi kansa baba yawale d'in kawai suka saba gani batareda wani mutum koda guda daya yazo ba wajen su da sunan d'an uwa, abinda dady mukhtar da baba isma'il gamida dady sales knn suke saqawa cikin ransu, yayinda 'su mama zainab da khaleepa gamida heenduh abin yayi matuqar d'aure musu kai dan ko kurkusa basuyi tsammanin hakan ba kuwa suma. ji suka baba yawalen yaci gaba da cewa "bawani abu ya raboni da mahaifata ba dake qauyen rugar fulanin sule ta jihar jihar adamawa ba face sharrin matar baba na ard'o a lokacin, abinda ya faru kuwa shine..... alhalin mu ahali ne mai tattare da zaman lpia da qaunar juna, hakama a wajen mahaifina ard'o wato mai garin rugar ba qaramin sona baba na yake yiba, da yake nida qanena muntari kawai ne mahaifiyar mu ta haifa, to cikin ikon Allah kuma dare daya ciwon ajali ya kama mahaifiyarmu inna wuro, kamin gari ya waye har ubangiji Allah Ya yakarbi ranta, munsha kuka sosai, dan mahaifinmu kuwa kusan zaucewa yayi sakamakon sunyi zama na haqiqa da mahaifiyar mu, saida qyar mlm imbo wato qanen mahaifina ya dinga rufutowa mahaifina rubutu na dangana snn mahaifina ya fara haqura,, tsawon sama da shekara mahaifina yaqi yayi aure dan acewarsa nida qanena muntari mun ishesa farin cikin rayuwa, amman inaaa mahaifina jamaa saida suka takura masa da mgnr cewa ta yaya yana mazaunanin mai gari guda snn ace baida mata..... daqyar da zufar goshi dai a lokacin sukasa mahaifina ya auri wata bazawara dake rugar tamu wai ita shatu. daga farko tafara tattalina nida qanena mukhtar kamar gske dan har mahaifina yafara murna da farin ciki na yayi sa'a ta matar arziqi kuwa mai kulawa da 'ya'yansa, wanda dama hakan na daga cikin abinda ya hanasa son sake wani auran, wato gudun kada ya auro wacce zata tsani 'yayan nasa, ana haka ne har mahaifina yayi mana aure nida qanena muka zauna nan cikin gidan, lokacin har ita ma goggo shatu matar mahaifina ta haifi d'a na miji shima ya girma, har matar muntari ta haihu mace, wacce aka sawa sali amman nida matata har lokacin Allah bai babu haihuwa ba, haka muka kasance muna rayuwa dai, toshi qanena muntari ba mazauni bane zuwa yake kiwon shanu da cinikayyarsu koda yaushe daga naqautan rugarmu, to mafarin knn da mahaifina ya tattara yan uwansa dana mahaifiyar tawa yace musu ko bayan ransa to babu wanda zaihau kujerarsa ta mulki bayaga ni... wannan abin ashe ba qaramin k'onawa goggo shatu ran ta yayi ba, dan ita taso ace d'anta kabeey shine zaihau mulki, ahaka taita shige da fuce tana samo asirika tana sawa a abincin baffanmu dan nida kaina nasha kamata tana sawa amman bata san na gani ba,. ana haka katsam aka wayi gari mahaifina ya kirawoni a gaban mutanensa yace nabar masa gari nida matata kada na kuskura nasake waiwayosu sai nan da wani dogon qarni, acewarsa haka nan yaji yatsani ganina bare kuma tarayya dani, dudda haquri da mutanen fadarsa ke basa amman yakafe, inaji ina
Chapter 174 · 0% Book details