← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 134 OF 178

Sashe 134

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

*zakuji ni shiru sisters kwana biyu, uzuri ne yataso mun sai kuma Allah ya sake sadamu da alherinsa a qarshen sabon satin nan dazai kama insha Allah.*

daga maison ganin farincikin ku

*Xexen Fasaha*. Ce
[3/30, 7:15 AM] Xainab Documen: 👁👁
🥡🥡
👁👁
*DA SAURAN KALLO*!!!

Story and writing by Xayyneb💤💤

Fasaha online writers.

*🌳Imparting valuable knowledge and intertaiment is our concern🌳*.

~dedicated to my mom Sadeeq hauwas~.

👁🥡👁
🅿5⃣7⃣.
*D* wani mugun sauri 'yan smogal din suka take burkin motar amman dudda haka saida suka dan taba jikin mama Zainab din yayinda motar tasu ta d'aga ta baya sannan ta dawo qasa har wasu daga cikin buhunnan shinkafar da suka lallodo suka zube qasan titin.
amman ita dukkan wannan tashin hankalin da mama Zainab ta qara rizqar kanta a ciki bata jishi ba dan kunnenta tsam ya dauko mata qarar da heenduh tai sau daya bata qaraba.
Allah sarki 'ya da uwa sai Allah, sai gashi dud kalar hushin da Maman tai da ita hango ta datai kwance warwas qasa hakan yasa da sauri tayi saurin komawa zuwa wajen da heenduhn take ta durqusa gabanta tana Dan tattaba jikinta, jin datai babu inda ke motsawa ne a jikin heenduhn yasata dan girgiza ta tareda fadin
''heenduh??! ke heenduh ki tashi nace ko?" jin babu wani bayani hakan yasa tai saurin miqewa ta isa wajen wani yaro mai saida pure water nan bakin gate din hospital din ta sayi guda daya tadawo ta sake zuqunnawa gaban heendun ta fasa ruwan tana zubasu a cikin tafin hannunta na dama tana shafawa a fuskar heendun wanda batadau tsawon minti uku ba kuwa heenduh ta farko cikin subbatu tana fadin"a'a dan Allah kada Ku kasheman mamana wayyo mamana,,,"!
sai dud mama Zainab kuma taji ta tsargu da kallon mutanen wajen dasuke giftawa yanzun kuma jefi jefi ciki hadda nurse dinda takaiwa likitan nan result din su suna kallonsu.
cikin takaicin surutan da taji heenduhn na mata yasa ta d'aga hannu ta buge bakin nata dashi, cikin tsananin azabar zafi heenduh tai saurin bude idanunta tareda dawowa cikin nutsuwarta lokaci daya kuma.
wani farinciki heenduh taji ya sauka aranta sa'ilin datai arba da mamanta tsaye lapian Allah a gabanta,ko zafin bakinta ma bataji a Inda jini ya dan futo daga gefen bakin nata ba sam sam ata sanadiyyar bugesan da Maman tayi.
Allah sarki da gudu ta miqe ta rungume mama Zainab din tana cigaba da kuka tama kasa cewa komi.
tureta daga jikinta mama Zainab tai tayi gaba tasake Barin asibitin a karo na biyu, dasauri heendu tabiyo bayanta kuwa, lokacin da mama Zainab ta isa titin har 'Yan smogal din sun gama kwashe buhunnan sun mayar zasu tafi, har kusa dasu mama Zainab ta isa tabasu haquri tareda cewan bata hankalinta ne taratso titi sbd patient dinta da ta baro cikin asibitin.
sun nuna mata babu komi tareda mata fatan samun lpia wa patient din tata sannan suka wuce.
kusan lokaci daya mama Zainab suka isa gidan kaka jameela din kuwa, mama Zainab najin takun sawun heenduh a bayanta aiko a fusace ta juyo tareda nuna heenduh da yatsanta manuni tace"kull kada ki kuskura ki ida qaraso mun da qafarki cikin gidan nan wlh kuwa heenduh, inko bahaka ranki zai sake mummunan 6aci kinjima na fada miki ko? tokiyi maza maza ki koma gidan mahaifinki tunkan dare yai miki"
sulalewa heenduh tai daga jikin bangon zauren datake raku6e, ta durqushe saman gwiwowinta tana sake sakin wani zazzafan kuka danji take gaba daya duniyar tai mata zafi da baqiqqirin battajin dadin komi kuwa a cikinta daidai da qwayar zarra kuwa.
banda harararta babu abinda mama Zainab keyi tana sake jin wani tuququn zafin ciwon abinda heenduh taje ta aikata da aurenta wanda batasan hakan ba ita , wato tanada auren akan NATA.
wasu zafafan hawaye mama Zainab taketa sharewa na baqinciki da takaici da tunanun yaya zatayi kenan ita ne.
daidai nan kaka jamila(Maman mama Zainab)
ta fito daga bayi tana fadin "kai maganganun wa nikeji haka kuma tareda futar sautin kakkarfan wannan kuka.... katse mgnr tai tareda ajiye butar taqaraso gaban heenduh ta kamota zuwa jikinta suka shigo tsakar gidan tareda zama saman tabarma kan tai mgn saiga daya daga cikin almajiran Mlm zayyan ya shigo gidan kansa daukeda buhun gero ya yi sallama mm jamila ta amsa masa sannan ya shigo ya dure buhun a runbun hatsi yagaidasu sannan yace "baba gashi inji Mlm daga gona"
kaka Jameela tace"Mlm din yanzu yana gona kenan?"
ya amsa da fadin
"Eh baba aikin girbi akeyi ne shiyasa yace nafara kawo wannan buhun inyaso saimu qarasa aikin idan na koma, dayake su musa da lurwan da garbate dud tare muke aikin suna can, kuma yace kibada furar da kika dama akai can"
"To shiknn" cewar kaka jameelan tana mai miqewa ta shiga daki, bata dau ko minti daya ba ko sai gashi ta futo daki hannunta riqe da baban qwaryar data dama furan da faifai akai gamida luddai ta miqa masa ya karba ya fita.
dawowa tai ta zauna tana sake kallon heenduh da dud tabi ta rakube jikin bango tana sakin ajiyar zuciya dan tuni kukan yaqiyi mata dadi wajenyi wanda ba arziqi tabarsa jin kanta nawani mummunan sara mata ga kuma wani murd'a ta ciwo da cikin nata keyi.
dafata kaka Jameela tai tace
"jikata heendu mike faruwa ne dan Allah?"
wani sabon kukan kuma taji heendu yazo mata wanda bata shiryaba, mgn take tana girgiza kai tana cewa"dan Allah kema kada kice zaki tsaneni ki juyamun baya akan abinda ban aikata ba bisa son kaina ba face saida tabbas...a fusace mama Zainab tace"tabbas din banzan ki dake gareki, in kuma kinada tabbas kan abunda kika je kika aikata to fad'i tabbas d'in naki...shuru tai kamar zatai wani kukan itama takeji kodan tasamu sauqin zuciyarta..cigaba tai da cewa"wlh heenduh kinban mamaki yanda har kika iya zuwa kika jawo mana fitina muna zaman mu cikin rufin asirin Allah mahalicci"
taqarashe mgnr tareda share kwallan da suka subuto mata.
cikin rashin jin dadi kaka Jameela ta dubi mama Zainab tace"zainabu kul daki daina zubdawa 'yarki hawaye dan wannan zai iya qara zama mata musifa a rayuwa, dan haka kowane laifi tai miki abinda yafi ki dinga mata addu'a kawai kekuma kidinga fadin hasbunallah dan samun sauqin zuciyarki"
cikin duban kaka Jameela din mama Zainab tace"mama wlh kukan nan zuwar min yake dan abunne yafi qarfin zuciyata, wai mama yanzun kamar heenduh duniya zata rudeta har tayi amfani da kyan da Allah ya azurta ta dashi ta dinga bin mutanen wofi har gashi yanzun tana daukeda ciki wata biyu da satitittika,
to dan girman Allah mama ki gayamun wannan tashin hankalin dami yai kama wanda har zaisakamun nutsuwa a cikin zuciyata har abada?"
salati da sallami kaka jameela takeyi gamida qarashewa da fadin"subhanalla innalillahee wa'inna ilaihirraji'u...
gaba daya heenduh taji tsikar jikinta na tashi jin salatin da kaka Jameela keyi, tuni ta qara sautin kukanta gamida girgiza kanta da gaba daya jima takeyi bakinta ya kulle, zufa kam ajikinta sharkaf daga ita har mama Zainab din.
kaka Jameela cikin tsabar mutuwar jiki ta dubi heenduh bakinta na rawa rawa tace
"haba..haba heendatuh baki rasa ci ba baki rasa sha ba a gidan iyayenki kazalika zanen d'aurawa amman miye yakaiki ga aikata wannan mummunan aikin na sabawa mahallicinki da iyayenki dakuma yiwa kanki mummunan tabo a rayuwa wanda zai dawwama har jikokinki zakiji anmusu gorin abinda kakarsu tayi a yarintar ta indai a duniyar nan tamu ce?''
gaba daya jikin heenduh yakatse da kyarma kota'ina, tama gaza dagowa da kanta bare ta dubesu..
kaka jameela cikin karyewar zuciya ta juya ta dubi mama Zainab tace
"yasalamullahe!!!
innalillahe wa'inna'ilaihirraji'iunbabanta yasan da wannnan mgnr ne?"
saida mama Zainab tasake share zufar jikinta sannan tace"bazan iya tunkararsa da wannan zancen ba mama, dan dawowarmu knn ma daga asibiti kingama result din tabbatar da ciki dasuka bamu,
dan haka nina rigaya ma dana yanke Shawara bazan iya komawa gidan ba gskia"
girgiza kai mama Zainab tai tace"dole ko isma'ila yasan da wannan batun gskia, yanzun yana ina?"
"Yana wajen aikin su"
cewar mama Zainab din tanamai jin idanunta na mata zafi kamar ansa mata yaji a cikinsu.
shuru wajen yadauka fiyeda minti biyar sai faman bin heenduh da kallo suke wacce kanta ke saqe cikin cinyoyinta tana kukan bazatacciyar qaddarar data afka mata batareda shirin dasukai da doctor din ya fidda suba tunkan ma aje ko'ina knn.
sai zuwa can kaka Jameela ta bude baki cikin qarfin hali tace
"Dole kuwa yasan a wannan batun dan ba abun boyewa bane,
tashi zakiyi muje gidan gidan naku harmujira dawowarsa zansan yanda zan bullo masa da mgnr indake baki iyawa .."
Badon mama Zainab taso ba haka suka tashi ganin kaka Jameela tadauko mayafinta, nan suka fito.
saida suka iso qofar gidan nasu ne snn mama Zainab tatuna bata dauko key din qyauren wajen gidan nasu ba d'azun dan rud'u sanda zatakai heenduh asibiti, dayake jamlock ne qyauren nasu yanzu, wanda indai aka datsesa saidai abi da makullinsa a sake budesa sanann.
dole mama Zainab tafadawa kaka Jameela hakan,
kai tsaye kaka Jameela tace''kumu shiga gidan baba yawale majirasa anan din''
haka suka shiga gidan da sallama suka iskesa yana zaune da Qur'anic a hannunsa yana karantawa,ganinsu ne yasashi kawo qarshen surar dayake tareda shafa addu'a.
cikin qarfin hali suka gaggaisa dasu mama Zainab tareda masa bayanin matsalar key din da akasamu.
sosai baba yawale ya fahimci su mama Zainab nacikin damuwa musamman ma daya san dud da karadin heenduh Amman yau yajita laqwas dudda mgnr wasan dayai Mata Amman saima gani yai tana matse qwalla.
cikin mamaki ya dubeta sosai yace"to yaufa mikuma ya faru da wannan addababbr baiwar take mana matsen kukan NATA?"
yayi mgnr cikin murmushi..
kasa amsa masa sukayi dukkansu sai daga bisani sannan kaka Jameela ta janye tagumin da tayi bayan sauke wata qaqqarfan ajiyar zuciya datai sannan ta dubi heenduh kuma taqara maida kallonta ga baba yawale daqyar ta bude baki tace"mummunan al'amari ne ya tunkaromu yaukam baba yawale wanda yadagula mana gabaki dayan zuqatanmu da hankulanmu..sosai baba yawale yagyara zama cikin mamaki yace"miye wannan Abu kuwa jameelatu?''
saidaqyar da jibin goshi sannan kaka Jameela ta nuna heenduh da hannu tace"ciki tasamo sannan kuma taqi mana bayanin waye bababansa ma, kaganta nan banda kuka babu abinda takemana tun dazun"
cikin rawar murya mai gauraye da karayar zucci mama Zainab tace"wlh baba yawale bansan ta yanda babanta zai ji shigar mummunan batun
nan ba inya jisa"
shuru baba yawale yai yana kallonsu fuskarsa daukeda wani kamalallen murmushi dan har ransa yaji farinciki ya mamaya, sosai yasani daman komin daren dadewa gaskia zatayi halinta ta bayyana kamardai ranar yau data fara risqarsu.
sosai su mama Zainab sukai mamakin wannan murmushin dake fitowa daga daga fuskar kamilallen dattijon baba yawale, suda suka zata ma zai shiga tashin hankali shima.
babu zato sukaji yace"Alahamdililla gskia tayi halinta daman najima dajiran zuwan wannan rana ta samun yabanyar da aka jima shekara da shekaru da shuka irinta"
sosai mamakinsu yaqaru suka dinga binsa da kallo zuciyarsu cikeda rashin fahimtar inda zancen baba yawale din ya dosa...
Chapter 134 · 0% Book details