← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 178

Sashe 74

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

👁🥡👁 🅿3⃣4⃣. *Z* aro idanuwanta heenduh tayi tace "a'a miye abun talla ma ga wannan masifaffen auren kamar yanda mijin ya zamemun masifa? haba wlh yaya khaleepa mugun qulataccen jarababben mutum ne kamar kansa farau aure, dan haka wannan maganar ta zama sirri tsakanin mu inda baba yawale yace kada a fada kinga dole mubi maganarsa inda bamusan miyake nufi da hakan ba, ni hakan ma yamun walh hakanma yaimun dai dai da yace kada a fada kinga sai nai komi nawa cikin jin dadi da sakewa batareda an kaini gidan saba wlh daga gani kullen masifa zaiyi mutumin nan, kuma dagake bazan qara fadawa wani wannan zancen ba danko su mama na nasan basu san da mgnr ba da bazasu barni dinga fita zance ba,kuma bazan fada musu ba kada adinga mun kulle babu gaira ba sabar kema Dan na yarda dake ne bnda qawa Sama dake sa'a shiyasa n fada miki hakan dan Allah ki riqemun sirrin nan kada ki gayawa kowa shi please kinji qawas" ta ida maganar tata kai langabe ta koma kalar tausayi. kamo hannuwanta sa'a tai ta riqesu cikin nata tace"an gama qawata babu Wanda zaiji mgnr nan kamar yanda kikeso shima kuma baba yawale ya tsaran, dan yes bamusan nufin saba na hana fadan mgnr dan haka saimu kama baki mu saya shi" heenduh tace "hakan shi yafi dai" 'Yar dariya saa tai tace"Amman qawata abinda ban gane ba shine tayaya kikasan doctor jarababbe ne har kina cewa ba kansa farau aure ba anya kuwa qawata ba'a fara lasar zumar juna ba tsakanunku dan gaskia dai naga yanda kika qara kyau ashe da dalili" ta qarashe maganr cikin son tsokana. hararta heenduh tai tace "to yar sa ido in munyi haram ko halak? ba mijina bane? dariya sosai saa take snn tace "gskia ne masu aure kuyi komi ba komi ay keda habybyn naki nasan yanzun kukanki ya qare ko inda kin samu cikon burin naki sai a daina mun kuka..... duka heenduh ta kawowa sa'a tai saurin kaucewa tana dariya tareda fadin"gskia ne ay" murmushi kawai heenduh tai dan tabbas haka batun sa'a yake dan tun randa ta san kalar matsayinta gunsa komi na damuwa ya yaye koda ace bai sonta zadai taita ganinsa kullum tana jin dadi koda kuwa babu abinda zaiyana faruwa a tsakaninsu na fannin mata da miji dan jitake ganin sama ya isar mata da komi na rayuwa. tare suka kama hannun juna itada sa'a suka dawo tsakar gida cikin sauran 'yan matan amarya ana maida yanda akai tareda yin shewowinsu. khaleepa kuwa sanda suka isa dakinsa shida yunus saman gadonsa ya zube yana mai cigaba da dafe cikinsa jin ynda komi ya qara tasowa na ciwon nasa a yanzun. dud tausayinsa ya kama yunus dan daman Indai yaga khaleepa na wannan murde murden ciwon cikin nasa yasan komi ke nan,, dan haka da kansa ya dauko masa maganinsa yasha bayan ya zauna gefensa ya dubesa ganin yanda yaketa kwararo gumi kota ina a cikin jikinsa ga alama sauqin yazo dan yanda yaga sosai khaleepa din ya dawo hayyacinsa sakamakon maganin daya fara masa aiki take, dan maganin qarfi ne dashi sosai. yunus yace"haba friend doctor wai tayaya zakaita zama da lalura a jiki Amman kayi aure danka samu isasshiyar lpia ka qiya? gskia kasan abinyi dan nan gaba kada ka kasa control dun kanka ka jefa kanka wani halin alhalin kanada mafita akai. shiru khaleepa yai tareda lumshe idanunsa ruf dan shikadai yasan miyakeji a jikinsa dud inya tuno da kyan zubin tsarin lafiyayyun wannan na shanun nata dan har wani sabon abu yakejin yana tsurga masa inya tuno su., ga yunus yanai masa batun yai aure baisan matar tasa ba ce ta jaza masa shiga wannan halin dayake yanzun a cikinsa dudda yasan yanada sha'awa ta gaske amman tayau tafi tako yaushe motsa masa kuma yasan hakan Nada nasaba da gigicewar da heenduh tasa yai sannan ta gudu ta barsa , so yake ya fadawa yunus heenduh matsayin matarsa take amman baisan yanda akai bakinsa yai nauyi kan furta batun ba dud inya tuno da fadin baba yawale nasu surranta abun, amman yasan babu yanda za ai koda ya fada ma yunus hakan waiya fadawa wani shi kuma dan yasan fiye da kowa shiyasa abotarsu tafi tafiya dai dai akan sauran abokansu. bude idanunsa yai ya zubesu a fuskar yunus din sannan ya bude bakinsa a hankali yace"zanyi barci kozaka iya yimun shiru haka nan malam zubairu (surutu)? harara yunus ya jefa masa yace "qarewar inma shiru yanzun nan ma baran maka dakin naka zanyi inyaso ka zauna buqatar taka data taso maka tai maka komi inda kai baka jin shawara" yana gama fadan masa hakan kuwa yaja kofar ya fuce abinsa zuciyarsa cikeda haushin mugun muskilancin na khaleepa da kafiya kan abu dudda shi kansa yasan yanada buqatar abun kuwa. binsa da kallo khaleepa yai sannan ya samu ya miqe zaune yad'an murtsuke fuskarsa da tafukan hannu wansa a can qasan zuciyar sa yace" tabbas zan janye miki kuwa headache na 'yan wasu lokutta danna fahimci shige mikin da nike ne yasa kike mun yanda kikeso dudda kinsan matsayina yanzun a gunki amman bakida buri sai na kiga kin b'atan rai why?! why isay why?!! yafada a fili kuma da qarfi tareda yardo wasu books dinsa dake bed side dinsa suka ko tarwatse a qasa" sosai yaja wani dogon tsoki tareda yaye bedsheet din jikinsa ya miqe tsaye tareda sakin miqa har qassan sa sukai d'an qara, toilet ya wuce dan yin wanka, yana fitowa ya sanya wasu kayan tareda daura farar rigarsu ta likitoci akai ya dauki briefcase dinsa da key din motarsa da nufin fita hospital nasu saiga momynsa Hjy firdauseey ta shigo dakin hannunta daukeda qaton plate plates na abincika akai. ganin yana shirin fita yasata cewa "mai tsadana amman dai sai kaci abinci sannan ka fita aiki ko? marairaicewa yayi yace "no momy banjin cin komi a cikin nan nawah a yanzun" "A'a mai tsada na nida kaina na shirya maka fa delicious cook din tun safe nike kicen sai yanzun na fito dud saboda kai amman zakace mun em em kuma?!. tausayin momyn nasa yaji ya saurin kamasa dan yasan momynsa bawai qaramun so take nuna masa ba da tsantsar kulawa saidai matsalar momyn tasa d'aya yanda ta tsani dangin mijin nata da hana a kyautata musu da sauran ma mabuqata bayin Allah, Sam momynsa batada jinqai bisa ga dadynsa. dubnta yai sannan ya dubi farar fatar agogon dake daure a hannunsa snn yace''momy zanyi late inna tsaya cin abincin nan dan zan duba wasu patient kamar yanda na tsara Momy kinsan banson African time kan muhimmin abun da nasan i will do it on my time so kawai momy kisamun shi a basket innaje hospital din nagama aikin sanai breakfast din. "Yawwa mai tsada na mu sauka qasa to saina saka maka a motan naka, ahaka suka jero suna tafiya har take cewa "kunyi waya da dadynka kuwa yau? dan yacemun yata kiranka baka daga ba dazun, kuma na shigo dakinka a lokacin baka ciki shiru yai danshi saima yanzun ya tuno lokacin da yake tsaka da buqatuwa da heenduh lokacin suna manne ga dazun din tabbas yaji wayarsa na qara sama sama amman Sam baida kuzarin d'agata a lokacin da hankalin sa bai kansa sosai shiyasa baima duba ba. amman a fili sai yace"ok nad'an futa ne momy a lokacin kuma nabar phone nawa d'in a d'aki shiyasa bn holding bama but innaje hospital zamuyi wayan, to shiknn mai tsadana hakanma yayi ay" saida ta shirya masa abincin cikin basket din tasa masa a back set na motar sa sannan ta ruqo hannunsa tace "amm mai tsada na abunda na furta kan heenduh ga jia din tuntuben harshene baza'a kumaba kaji" sosai yaji dadi a ransa da tunanun inama momyn tasa zata daure a hakan dayaji farinciki muddin ransa. peck yabata cikin murna tareda yace "thanks Momy my pleasure saina dawo" yana gama fadin hkn ya shige motar suna dagawa juna hannu harya bar gidan. ita kuma ta koma ciki a zuciyarta take furta cewa"hmm in kasan wata ai bakasan wata ba yaro bakuma zan taba nadama kan abunda na furta/ zanwa wannan faqiran mutanen ba, nidasu babu wata sauqaqawa muddin suka matsoni gaba kuwa nidasu har yaumul yhu nadi ranar damai kira zaisa ayi kira abusa qaho!!!!matsiyatan banza da wofi talakan iska sunga mun yaro dan caras cas suke son shanye mun tunaninsa har nace zan musu abu kk qoqarin furta cewa zaka iya kisa Kansu??? Hmnnnn bazan bari kai kisa ba saidai na canza taku akansu yanda bazaka sani ba mai maitsada na dan muddin rai na yawo a jikina bakada matar da ta wuce zarah ta. da wannan tunanin ta shige cikin gida. zarah kuwa tun bayan gama rushe rushen kayan dakin natan datai ta fadi nan wajen qasa tana munshari ba itace giyar nan ta saketa ba sai washe garin ranar da misalin qarfe 3:54 Am. zuwa lokacin kuwa Hjy hadeeza tashigo dubata yafi a qirga tana kwance shame shame a tsakar daki duttai amai sai mugun wari dakin keyi. daqyar Hjy Hadeeza tasa mai aikinta ta gyara wajen sannan yai daidai. tana farkawa ta tashi zaune dagar gar gashin attach dinda ta qwaqu bawa knta kuwa dud ya haukace shima, haka nan tatashi taje tayo wanka ta fito tahau shafe shafe ko sallolin dake dubge saman kanta na jia da yau bata damu data yisu ba dan daman bawai damuwa da tai sallar taiba dan saitaga dama takeyi inbata ga damaba saita hada ta kusan sati sannan tayi ta ranar kingun shikenan kuma sunbi sarkin shanu babu ramuwan su knn. dudda kurajen da sukaiwa fuskarta feshin ruwa baqaqe kuma Wanda da ganinsu tambarin bleaching ne dan har glass ya sakar mata a geffan idanunta amman shafa wata tsadaddiyar fowder dinta datai hakan yasa kaso hamsin cikin dari na tabbunan sun 6oye cikin fowder din. haka manyan lips dinta masu girma da tudu ta shafesu da wani dark green din jambaki. ta feshe jikinta da turare sannan ta saka wasu riga da wandon pakistan sun ko matseta ram dan zarah akwai qiba kalar wacce bata nuna sharp din mutum sannan kuma breast dunta bawasu
Chapter 74 · 0% Book details