Sashe 132
Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
khaleepan tariqe gam tace "amman shine bai kira ni yafara myn surprise dinba?'' tayi mgnr tana wage baki. "Sryy momy yace ai yaita kiranki dazun baki holding ba" dasauri ta zage jikkarta ta fiddo wayarta ta duba nan take kuwa taga har 8 missed cull na Alhj mukhtar din. nan tace''aikam dai gashi yakira kuwa Ashe,,shiru tai tana tunanin ina zataji Qarar wata wayarsa tana can tana shan duka ga qaton Allah ta'ala cin tuwon qauye. Hjy Hadeeza ma cikin zuciyarta sosai tayi farincikin jin Alhj mukhtar zai dawo Nigeria koba komi tafara sunsuno qamshin auren zarah da khaleepa knn kamar yanda Hjy firdauseey ta maganta mata mgnr auren wato inya dawo. miqewa khaleepa yai zai fita nan tayi saurin cewa "mai tsada ina buqatar magani" dan dakatawa yai tareda juyowa yace "Momy na jia fa dana kawo miki?, koba su kike so ba ne?" kai tsaye ta lauye mgnr da cewa bayan qarasowa har gabansa datai "kagane ko maitsada na wata qawarmu ce jia wani qaton gabjejen mahaukaci ya shiga gidanta ya zaneta ram daqyar jama'a suka kawo mata dauki aka fiddasa a gidan to shinefa fatar jikinta did ta d'addaye ga jini, to kuma saidai jinin ya tsaya yanzun" sauke ajiyar zuciya yai yace"to Momy zaifi kyau tazo hospital adubata daganan kinga sai abata magun daya dace m... katsesa tai da cewan "a'a maitsada na munrigaya da munyi mgn da'ita naimata alqawalin zan tambayeka inda wani maganin dazata ringa shafawa ciwukan su warke to saika bani nakai mata kawai,," bai son cika doguwar mgn shiyasa yace"ok akwai wani cream lotion zai mata amfani ciwukan suyi saurin qamewa in tana shafasa, inzan dawo gida zan shigo miki dashi sai abata ta dunga gogawa saman ciwukan dan fita zanyi yanzun zamuje wani waje da yunus''. "to shiknn saika dawo amman kada fa kamanta katafo dashi dan Allah dan tanada tsananin buqatarsa a yau ne". "OK Momy" abinda yace knn yashige motarsa yabar gidan. duban Hjy Hadeeza Hjy firdauseey tai ta zauna daqyar sannan tace "da zarar alhji na yadawo shiknn ai biki yataso a tsakanin zarah da maitsada" washe baki Hjy Hadeeza tai tace"aikam dai qwamma ayi a ture ay" "Shidinne ay" cewar Hjy firdauseey din tana faman sosa bayanta. miqewa Hjy Hadeeza tai tace "Zan shiga gida na kwanta nad'an huta hjyta" "To shiknn saina kawo miki maganin knn" cewar Hjy firdauseey. "eh ina saurarenki inda tsinannun mutanen nan sun daura mana ciwon dole, dan nikam har abada aibazan manta da mutuwar marakusa ba dud in naga ciwon nn a jikina" Hjy firdauseey tace"qyale matsiyata Allah Isar mana dai inda bugu ne sun rigaya dasun buga tsinannun" ahaka har suka rabu suna tsinewa su fillo gambo sanna tafice daga gidan itama Hjy firdauseey din tadawo cikin gidan tareda qara nufar bayi danta qara was jikinta wani sabbin gashin ruwan zafin. misalin qarfe 8:35 pm dady salis ne shida baba Ismail zaune a sitroom din dady salis din Suna total na kudaden ribar masana'antar tasu da yaketa faman qara hauhawa. bayan sun gama komi ne baba Ismail ya miqe dan shirin tafiya gida anan dady salis ya gyara zama yace "dawo ka zauna qanena zamuyi mgn" "to yah salis" cewar baba Ismail din bayan ya dawo ya zauna inda yatashi tareda bismilla. sake qara zamansa dady salis yai yace "tunda na dawo daga dubiyan kawuna ko yau kimanin kusan wata 2 kenan cikin ikon Allah kamun natafo daman acan na jejje wajen malaman kirki da nufin su tayamu da addu'a gameda lamarin mukhtar kuma dukkansu sun tabbatar mun da insha Allah zasu tayamu da addua gamida nafilolin dare kmr ynda mukeyi muma, kuma har suka ban shawarar ma dana dinga kai alqur'anai sadaqa makarantun allo dana islamiyya da kuma masallatai dan neman sake dacewa da ba'asan ta inda Allah zai kawo taba, kuma haka akayi dan banma iya cewa ga iya adadin alq'ur anan dana babbayar dakuma sadaqoqi ba masha Allah dai, to kuma koda ma na dawo nan haka naci gaba dabada sadaqa ga malaman addini dan harga Allah banda buri a rayuwa daya wuce naga mukhtar yadawo garemu qanena, to abunda yasa ma kaji na kawo maka wannan mgnr shine yanda wani babban malami wato Mlm Abdul Kareem yace zai bani wani rubutu dud sanda mukhtar yasha rubutun to cikin ikon Allah dud wani qullin sihiri dake jikinsa inma akwaisa to dazarar yasha rubutun nan zai game ko'ina a jikinsa wanda a hankali a hankali sihirin zai narke har yabar jikinsa zai kuma dinga kasayo sa baqiqirin a cikinsa yana kuma d'oyi, kuma zaiyi rashin lafia sbd cutar datake ficcewa daga jikinsa, dud shine ya siffatamun yanda alamomin fitar sihirin zasu fito, sannan kuma yace dud dai acikin rubutun zai hada mun da rubutun maganin kariya daga kowane jifa ko sammu daza'ai masa cikin ikon Allan yagama samunsa saidai yakoma inda aka yosa inma yatafo din. nima dana buqaci yaimana rubutun sha daga cikin ayoyin qur'ani mai girma na kariyar a dukka iyalan namu yace in Allah ya yarda zaimana namu daban, to yau da kumai waya da mukhtar yake cemun gobe ko jibi yana nan dawowa Nigeria, shine kaji sanda kashigo dazun ina waya to dashi Mlm Abdul Kareem din ne nike fada masa dawowar tasa shine yace inzo gobe in amshi rubutukan namu kuma Allah yatema yabamu sa'a. yanzun gobe insha Allah zanje dasafe can gidansa a rigasa na karb'o, kuma nafada maka hakanne kaima dan kasan lamarin' qara kallon baba Ismail din yayi yace Kadaure qanena kadinga saka dan uwanka addu'a dan inada tabbacin wannan halayen dayake yi banasa bane d'aura masa akai kuma komi yazo qarshe insha Allah". sosai baba Ismail yarasa bakin shi dai dazaice ga wacce kalar godia zaiwa dady salis a rayuwa, dan ya gyara musu cikin temakon Allah matuqa, wani sabon kalar son d'an uwansa kuma yayansa mukhtar gamida tsananin kewarsa yaji yana ratsa masa dukkan illahirin jikinsa, cikin goge qwalla yace ''insha Allah Yaya salis zan cigaba dasa sa a addua fiyeda kullum ma,,Allah ubangiji yasaka maka kaima da alheransa Yaya salis, yafaranta maka fiyeda ynda kake faranta mana". cikin murmushin jin dadin adduar dady salis yadunga cewa "aminn qanena, muje nataka maka inda naga bakazo da motar kaba a qafa ka tako kazo ko?" "Aa wlh ya salis kaizamanka ngd dan gidan baba yawale zan wuce ma shiyasa" ''to shiknn qanena kagaishe mun dashi Inkaje" "to Yaya salis zaiji insha Allah" ahaka suka rabu cikin jin dadi. yaukan tun bayan sallar isha'e heenduh keta barci har khaleepa yashigo yazauna suna gaisawa, mama Zainab take CE masa''ni narasa isalin wannan barci na heenduh khaleepa datakeyi kwanan nan au dare au rana bata taba gajiya? Tun ina fadan harna ma haqura" aran khaleepa murmushi yayi danyasan wannan dud yana daga cikin laulayin heenduh amman a fili kuma saiyace"kotana yawan aiki ne mama?" mama Zainab tace"Amman khaleepa dan kana aiki kuma sai ace lalacin barci yasameka? kawaidai raggwanci ne yaran zamani aiki kadan dasunyi zasuta raki" murmushi kadan ya subuce masa kawai yana ayyanawa a ransa inama ace a gidansa ne lollipop take laulayin cikin nasu da shi kansa baisan iya adadin tarairaya da kulawa ba dazata samu, saidai inaaa babu wata damar nuna hakan a yanzun, har ransa yakejin rashin dadin hakan kuwa. yadan jima sannan yaiwa mama Zainab saida safe yafita gidan zuciyarsa cikeda rashin jin dadin na sugar tasa dabaisata cikin idanunsa ba dud yinin yau kuwa,, dole yahaqura da qudurin da wuri gobe zai baro asibiti inyagama aiki yazo ya ganta koyaji daidai a ransa, dayake can zai kwana yau sbd ayyukan dazaiyi na dare. da tunanin hakan ya shige motarsa yanufi hospital din. tunda hhenduh tagama sallar asuba taji wani amai nason tuqota saifaman maidasa take kuwa cikin yamutsa fuska da danne gefen cikinta dake ciwo yana katsawa mata. qarfe 9 saura na safe dauriyarta ta qare danda gudu tataso ta fito ta durqushe gaban maguji tana kakarin fiddo kumallo dan babu komi a cikin nata, sosai ta galabaita, can cikin barci mama Zainab tajiyo aman aiko cikin salati tamiqe tayo waje tasamu heenduh did tayi tubus liliss ko hanunta takasa dagawa sosai. cikin tausayin 'yar tata mama Zainab take mata sannu tareda shafa mata ruwa a fuska. harta gama tana qoqarin miqewa mama Zainab ta riqeta tace"zauna nan bari na fito, tayi mgnr tareda zaunar da ita kan tabarma. babu jimawa mama Zainab tafito cikin mayafinta ta fuce waje,, zuwa can sai gata tadawo tasake shiga dakin heenduh ta dauko mata hijab ta iso tasaka mata a jiki sannan tace "taso muje ga napek can natsaida mana" dudda tsananin ciwon kan da heenduh keyi saida ta dubi mama Zainab tace "inazamu mama?" "Asubuti kuma karki saki kice zaki misa mum tashi kawai muje dannagaji da ganinki haka heenduh kina ciwon wahala dinn kullum, haba amai badare barana Uwa wata mai yaron Ciki?, kojia cikin dare fama saida naji kina qaqarin aman nan fa a dakinki" dammm!! heenduh taji gabnta ya yanke ya fadi, jin mama Zainab takamota tamiqe tsaye babu yanda zatayi haka tabita suka tafi asubitin. sun zauna bin Layin ganin likita ahaka har layi yazo Kansu suka shiga, mama Zainab dakanta tadinga ma likitan bayani gamsasshe nan yayi wani rubutu yabasu yace sukai wajen 'yan awo.. babu bata lokaci sunakai takardar sai kuma aka kaisu wani dan daki nan wata nurse tace heenduh tayo fyyy tabata. atsorace tayo firsarin tabata zuciyarta sai faman tsinkewa takeyi dan tsoro sanin datai khaleepa ta kalar wnn binciken ne yagano cikin jikinta. sunjima zaune saiga nurse dun tadawo tace "kutaso muje" binta sukai nan sukaga sun sake shiga office din likitan nan daya rubuta musu awon. "Doctor ga result din mun fiddo" cewar nurse din gamida ajiye masa result din a teburin gabansa. likitan wanda shekarunsa aqalla zasukai 57 yadauki result din yana dubawa yace "weldone Sera zaki iya tafiya" "OK sir" abinda tace knn ta fice. saida doctor ladan yagama duba result dinn sannan yadago yadubi mama Zainab sannan yamaida dubnsa kacokan a heenduh wacce kamar zata narke dan firgici takeji. duban mama Zainab doctor ladan ya koma yi sannan yace"munduba komi kuma gameda bayanan da kikai man to wannan bakomi bane yake jazawa yarinyar haka ba face cikin dake jikinta d'an kimanin wata biyu da