← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 178

Sashe 104

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

👁🥡👁 🅿4⃣7⃣. *A* hankali ya dago da fuskarsa yana kallonta har baisan sanda bakinsa ya su6uce yai mata sabon suna nan take ya kirata da"lollipop d"ina" ba'a bayyane tareda kissing din gashin kanta daya sake kwantowa a ta gefen wuyanta. yanayin shigar deep kissing din dataji har saida tad'an motsa sannan ta koma taci gaba da barcin wuyar wahalar nan tana cigaba sauke ajiyar zuciya akai akai, qirjinta sai sama da qasa suke a hankali yakejin hakan a qirjin sa dake saman nata har wani tsigar jikinsa ta fara tashi a lokacin yakeji. lumshe idanunsa yayi sannan yasake warasu a saman 'yar baby cut face dinta yana kallonta ko qyaftawa baiyi. saida ya kwashi tsawon mintuna 15 a jikinta yana faman kallonta dan sam bai gajiya da kallonta haka yakeji. jin wayarsa na ringing ne yasashi datse kallon nata dayakeyi badan ya soba yana dan tsoki ya maida idanunsa saman screen na wayar dan ganin mai kiran. "dady na" abinda ya furta kenan can qasan lips dinsa yana sakin wani dan murmushi a taqaice sannan ya daga wayar. dady mukhtar ne ya fara amsa gaisuwar da sukaiwa junansu wacce suka saba kalarta sannan yazarce da fadin "my boy ango ansha qamshi ake cewa ango koko mema? daramm!!! khaleepa yaji qirjinsa ya buga da sauri ya qara gyara zamansa sosai yai facing din fuskar heenduh yana kallo da tunanin kodai dadyn nasa duba ya koyi yine bai sani ba? "my boy kana kan layi kuwa?" cewar dady mukhtar din. gyara murya khaleepa yai jin tana shirin sarqe masa maganar. "dady wane ango kuma kake fad'a?" yayi maganar yana d'ari d'arin jin amsar dayake zata daga dadyn nasa kuma. "hmmm my boy kenan daman kun sasanta kanku da zarah ashe shine banji labari daga gareka ba sai yanzun da mukai waya da momynka take fada mun hakan?, hartana cewa ka matsa asa muku ma rana tun kan na dawo ko? hmn my boy kenan yanzun bazaka iya jira na dawo ayi engagement din dani ba kenan?,,,, da sauri khaleepa ya toshe speaker din wayar tareda dan janyeta daga kunnensa ganin heenduh ta farka shi kawai take kallo kamar maijin abinda ake cewa a wayar. da sauri ya miqe yadan fita nan tsakar gida murya qasa qasa yace"no dady ba haka bane" dady mukhtar yace "my son ba haka bane kamar Yaya? kanason kace mun ne maganar da momyn ka ta gayamun ba gaskia bane koko?" runtse idanuwa khaleepa yayi tareda jinginar da bayansa a bangon dakin mama Zainab. tunani yake Yaya zaiyi ya fahimtar da ita momynsa ne waishi baison qaunar auren zarah ne a rayiwarsa datake son qaqaba masa ita dan Allah? gashi kuma sam baida tsarin sha'awar auren Mace sama da daya gudun hayagaga a kansa na qananun maganganu na mata. shi bama haka ba sam ya manta sunyi mgnr zai amince in dadyn ya kirasa kan mgnr auren zarah din kamar yanda yaiwa momyn tasa alqawali, kuma gashi dadyn yaimasa yanada damar qaryata masa zancen momyn ne? a'a. shi yazata bama yanxun ba sai gashi kuma lokaci qanqani maganar ta bujiro masa a bagagatan hayqan. yanzun ya isa ne ya qaryata maganar momyn tasa wajen dadynsa? ina hakan bazai yiyuba. wata zuciyar kenan ta CE masa hakan. shikam Kansa ya rigaya daya fara daukan charge babba dan haka danne kansa yai da hannunsa guda daya yayinda dayan ke riqe da waya a kunne yanajin dadyn nasa na cewa "hello my son kana kan layinka kuwa?'' Kasa amsa masa yai saiji yai d'uf dady mukhtar ya katse layin. sauke ajiyar zuciya khaleepa yai ya cira qafarsa kenan zai koma dakin sai ga wani kiran na dady mukhtar ya sake bujiro masa. "Oh my God!!!!! help me my God. abinda khaleepa yace kenan yanajin wani kalar d'aci d'aci a maqogaron sa. ya fara tafiya kenan da niyyar komawa d'aki yaga heenduh ta dafo bango ta fito daga dakin nata tana tafiya daqayar daqyar, dud tak'i daya kuwa saita tsaya ta huta sannan taci gaba da d'an takawan. da saurin takunsa ya isa gareta yana fadin"lollypop yaya kika cire drip din kuma?!" yana qoqarin riqo hannunta ne yaga ta daga masa hannu daya alaman kada ya soma kusantota. zuba mata idanuwa kawai yai cikeda tausayin ganin yanda ta dauki butar ta shiga kewaye a daddafe. babu jimawa yaga ta sake biyo bango ta fito ta zauna saman tudunkan rijiya tafara yin alwala. sosai wani tausayin ta ya qara lullubesa ganin yanda take komi a da qyar cikin dauriya. yana yunqurin tashi ne daga zuqunnin dayai yana kallonta daga kofar dakin nata kenan yaji wayarsa tasake sabon ringing a lokacin. dadynsa ne yaga ya sake Kiran sa dan haka jikinsa a sanyaye ya daga wayar tareda cewa "dady?" dady mukhtar yace "sorry muna waya my son network ya riqeni amman yanzun it's normally ne, yaci gaba da fadin cewa "ammm muna magana kan batun ka da zarah ko? to sorry my son dan nariga ya da nacewa momyn taka kuyi haquri harna dawo gida tukun ayi komi ina nan cikim family na na hidimar bikin ince dai bazaka damu ba da wannan hukuncin dana zartar?" sauke wata qarfaffan ajiyar zuciya khaleepa yai a ransa sosai yaji dadin hakan dan baisan da wane ido zai dubi lollipop dinsa ba muddin taji wai zai auri zarah danshi ma Kansa sake jin tsanar maganar ma yake a ransa dud inya tuno. a ciki ya amsa da "to dady bkm, nima zanje hospital yanzun" to shiknn my son saimun sake waya" ahaka suka ajiye wayar kusan lokaci daya. binta yaci gaba da kallo sanda yaga ta ajiye butar ta nufo daki a hankali harta shiga dakin ko kallo bai isheta bama tamfar bata sanda shi bama wajen dan ita tsoron ma kallonsa takeyi dan baqaramin hankali yai mata ba kam takega. har ranta takeson tambayarsa abincin su baffa amman ta kasa. ahaka ta shiga dakin daqyar tasamu ta sanya rigar materiyal dinta doguwa dake saman akwatinta sannan tai dirshan bisa dardumar dakin ta fuskanci alq'ibla tareda sanya hijab dan battajin ma zata iya sallar daga tsaye saboda jirin dake som daukarta. lokacin qarfe goma da minti shabiyar na safiyar. ahaka ta samu tayi sallar tareda Neman gafarar rashin yinta kan lokacin ta dubada rashin lafiyan data sarqeta. tana idarwa tai yan adduoenta ta shafa sannan ta kwantar da kanta nan bisa pray mate din ta lumshe idanunta tana sauraron zugin zafin da qasanta ke fitarwa. qamshin turarensa ne yasanar mata da shigowarsa a dakin hakan yasata sakeyin lamo uwa mai barcin gasken. gabanta ya qarasa ya hard'e qafafunsa waje daya bayan ya zauna. daramm!!! taji gabanta yana bugawa dan batasan miya zo yimata ba azaman nasa dayai gabnta. jitai yasa hannunsa yana shirin zare hijab din jikinta data qudundune jikinta da ita bayan ta cusa kanta kuma a ciki, hakan ne yasashi tunanin cewa zata takura da yawa kada kuma wuyanta yai ciwo. d'aura hannunsa keda wuya a saman hijab din nanma wayarsa tasake sabon qara. janye hannunsa yai jiki a sanyaye ya d'aga wayar tareda cewa"momy?" "Mai tsadana najika shiru ne gashi kuma harna qarasa had'a muku komi oready a cikin warms colors da jug yanda bazai canza ba har dare koda kuwa kunada buqatar sake ci" "to shikenan momy gani nan nakusa isowa" "to qwamma dai kayi kazo dan kasan bazan lamunci zamanka da yunwa ba" d'an qaqalo wani murmushi yai yace "I know thanks momy" datse wayar yai tareda sakata a gefen aljihun wandonsa na jeans. harya miqe tsaye kuma saiya sake dawowa ya zuqunna tareda qoqarin warware mata hijab din babu zato yaga ta miqe zaune a fusace tareda fusge hannuwansa dake saman hijab din tana watsa masa wata fitannaniyar harara mai cikeda tsabar hushin Wanda aka baqantawa. saikuma ta rushe da kuka wiwi tana fadin"ai sai kuma ka tashi kaje inda kasamu biyan buqatar ka jeka!!jeka!!,natsani ganinka na tsani ganinka!! dud yanda nike gunjin kuka daka taimaka ka rabu dani hakan amman ka mini buris da roqona wato na mutu kona rayu wannan ba damuwar ka bane ko? ammn haka kaci gaba da zafafamun batareda kayi la'akari da bamtaba yim hknba bare kaimum kallon masabiya, daman nasan da sanin cewa albarkatun jikina kake so kuma kasamu saikaje ay" maganar take tareda qara wara saitin kukanta wanda yakejin kukan nata kamar tana soka masa allurai ne a dukkan illahirin jikinsa, shin miyasa zatai masa wannan fassarar? shin miyasa bazatayi la'akari da yawan qaunar ta dake ransa ne da gangar sukayi nasara a Kansa harya kasa barinta a lokacin datake roqonsa?, shin bazatayi la'akari da hankalinsa ne bai ga jikinsa ne shiyasa har yakasa fahimtar mitake fad'a lokacin ne? runtse idanunsa yai dan ransa wani suya yaji yana masa sanda ya tunano kalamnta datace masa badan Allah yake sonta ba saidan jikinta.!! a hankali kuma ya bude idanunsa dasukai jajur jijiyoyin Kansa harsun fara fitowa daman haka yake komawa muddin ransa ya baci a take. jikinsa na rawa ya riqo cinyoyin hannuwanta yana kallonta maqoshinsa na masa d'aci ya bude bakinsa yace"banyi hakanba saida amuncewarki, kinsan kuma da bana sonki babu yanda za'ayi na shigo cikin rayiwarki headache,,.tabbas! tabbas! tabbas! dan sha'awa inada ita wannan ma jini nace tuni batin yau ba wanda dud sanda tatasomin kwana nike dafe da marana, amman tun sanda na fara muki kallon so headache wallahil azeem sha'awarki bata rufemin ido ba yayinda sonki ya rinjayeta, tabbas sha'awa halitta ce da Allan ya halacci bayinsa da ita tsakanin jinsin maza da mata kinga kuwa kowa nada ita ....ni..,,ke... kowa da kowa ma. d'an shiru yai sannan ya janye hannunsa daga hannuwanta dataketa qoqarin qacewa tuntuni sbd zafin matsarsu dayake keta shigarta. ya miqe tsaye sam bacin rai yasa yama ksa kallonta dan dud cikin maganar ta wacce tafi tsaya masa arai itace wacce tace sha'awarta yake bawai so ba. dan haka Kansa na kallon gefe yayinda hannuwansa cushe a ajikin aljihun wandonsa ysce "amman babu komi inda kince daman sha'awarki nike bawai so ba dan haka na miki alqawalin bazan sake nemanki ba harsai sanda keda kanki kika buq'aci hakan kika gane so daban sha'awa ma daban koda kuwa ace buqatataciyar lalurata zata zama sanadin barina nan duniya kuwa naji zan daure''. yana gama fadin hakan ya juya zaibar
Chapter 104 · 0% Book details