Sashe 29
Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
```Masoyana na gskia da gskia wanda na sani da kuma wanda bn sani ba ina godia gareku matuqa da nuna qauna, ina roqon Allah kuma alherin Allah ya isar muku kamar yanda nike samun managartan addu'oe daga gareku kuma```. 👁🥡👁 🅿1⃣7⃣. *M* ukhtar kam sai da qyar doctor merzan ya rarrashesa tun shigowan sa shima kuwa ya iske sa halinda yake. kan dole mukhtar ya haqura ya basu d'an ya fita ya canza kayansa ya zauna nan office din doctor merzan kamar yanda ya umarcesa daya jirasa nan. babu jimawa saiga likitan ya fito yayinda firdauseey ke biye a bayansa har zuwa lokacin fiskarta share share take da hawaye. mukhtar nan shima yaji zuciyar sa ta q'ara karewa dole yasa hankicerf wannan karon yana tafiyar da hawayen nasa a cikinsa. bayan firdauseey da likitan sun zauna nan doctor merzan ya dubi mukhtar yace "ka daina saka damuwa a ranka kaji? babynka zai samu lpia insha Allah so dan yanzun haka mun kaisa can dakin da na'urorin suke mun kuma sanya sa ciki, sai dai kuma a qa'idar asibitin nan indai muka kwantas da iriyar wannan patient d'in to ba'a zama wajensa kuma adadin satikan da muka d'iba sai lokacin ake dawowa so dan hka be careful zaku iya tafiya sai nan da sati uku zaku dawo ku iske sakamakon, sannan ita kuma maman babyn munga babu wata matsala a jikinta kuna iya komawa gida yanzun tare da ita wannan shine cikakken bayanin zaku iya biyan bill namu sannan ku tafi" da kuka firdauseey tabar office d'in shi kuma mukhtar saida ya biya bill na komi sannan ya fita daqyar ya rarrasheta suka shiga mota direbansu yaja su har gida. koda suka koma gida bnda sabon kuka babu abinda firdauseey ta dasa dan gaba daya ta hayyaci kanta ta hana kanta sukuni. dole mukhtar ya kirawo mairon tsimbe tazo. tana zuwa kuwa ko sallama batai ba ta fad'o cikin falon gagaf tana fad'in "wai yaya ne mike faruwa nikejin kukn firdauseey ta?" cikin ladabi mukhtar ya fito daga bedroom din ya gaisheta ko kulasa batai ba dan ita ta 'yarta kawai take da sauri ya matsa yabata hnya ganin yanda ta cusa kai cikin bedroom din nasu har tana qoqarin turesa. firdauseey na ganin uwar tata da gudu ta miqe tsaye ta isa jikinta tana cigabada da kuka tana fadin "mama babu babyn babyna zai mutu ya barni mama? ita mero ma sai lokacin ne ta lura da babu cikin jikin firdauseey dan haka wata uwar ashariya ta ingizo tareda fadun"tooo ana wata ga wata fa, bantar ubancan,! gidan uwarwa aka kai mini jikan nawa eye? a fad'a mun inda aka saka mun jikina komuma billaheel azeem na rigizazo muku August a gidan nan" tayi maganar tana dukan qirji tareda cin d'amara da mayafinta tana duban mukhtar alamun dashi take. kasa magana yai dan baq'aramin tsoron meron tsimbe yake jiba matuqa a rayuwarsa, dan haka muryarsa na rawa rawa yace "ai...ai mama yana hospital ne.... "uban ubanmi yasa aka barosa a sosbitel d'in?, cewar meron tsimbe data katse mukhtar d'in dudda mukhtar na halin tsoro saida maganar mero taso basa dariya danjin dayai ko sunan ma hospital din takasa fad'a banda zagi babu abinda bakin ya iya da cin mutunci. kamo hannunta firdauseey tayi suka zauna gefen gado nan suka zauna firdauseey ta fad'a mata da cewa "mama babyn ne bayya da lpia dana haifosa kuma.... nan ta kwashe komi ta fad'a ma uwar ta qarashe da matse qwalla tana cewa "wlh mama bakiga kyakkyawan babyn ba, AllAh kuwa mama inna rasa sa kema zaki rasani ne" kama hab'a mero tayi dayake zuciyar ta ta jima da qeqashewa shiyasa bataji ko d'ar na tausayin firdauseey dawani jinjirin ba, kawai fizgo hannun firdauseey tayi ta girgiza tace "toke dan ubanki uwar waye yace baki fad'a mun ta waya ba nazo munje asibitin tare? kuma uban waye yace kitashan abin sanyin ne eye bare kizo kifasawa mutane makoki?, to wlh can saman kanki kuma marmaza kije ki d'umma jikinki da ruwan zafi dan maijego batta zama babu gashi" haka firdauseey ta miqe ta nufi toilet amman gaba daya zuciyarta naga babynta, mero ta miqe tace "naga sanya kikewa batun bari kiga in shigo kewayen in gasaki da kaina dan ban yarda da kiyi ke kad'ai ba dan wannan in aka barki zaki lalata kanki ki zama maras amfani fanko ga miji saidai yaje ya nemi wata kokuma ya aura kinaji kuwa kina gani kin zama foto a cikin gida bayanda zakiyi" haka mairo taita sakin magana ko kunyar mukhtar dake wajen batayi ba harta bi firdauseey toilet din ta maido kofar ta rufe. zama mukhtar yayi gefen gado tareda dafe kansa yarasa yanda akayi son babyn nn yai masa wawan kamu, zumbur kuma sai ya miq'e tsaye ya koma falo ya d'auko wayarsa yahau kallon foton babyn bai aune ba sai yaji hawayen sa na d'iga bisa screen touch din wayar. yajima a haka sannan yayi shirin office akan dole sakamakon wayar da aketa masa tun dazun akan zuwan wasu baqinsu haka yahau mota jikinsa a mace yabar gidan. A can toilet kuwa kukan da firdauseey take tana kiran babynta kada ya mutu shine ya hassala meron tsimbe ta kufula tace "tace ke dan kan mataccen tsohonki kukan nn ya isheni haka, haba anyi d'iya sai shegen naci? kuma madai naga yaron nn bai mutu ba bare kita asarar hawayenki ko?, to inma ya mutu q'asanki amfanin ubanmi yake miki dabazaki qara iya daukar wani cikin ba ki haife?,, shiru firdauseey tayi amman sai faman gunguni takewa uwar qasa qasa tareda satar hararata, basu baro kewayen ba saida meron tsimbe ta gashe firdauseey fiyeda qema ta qara shan wata azabar kuwa saida ta bud'e sabon famfan kuka sannan uwar ta barta. haka ya kasance kullum mero ke kulaw da firdauseey kuma basu fad'awa kowa haihuwar ba dan a cewarsu sai sati ukun sun cika sun koma asibiti suga yanda lpiar yaron take ko akasin haka. cikin ikon Allah kuwa yau Monday yacika sati uku knn da haihuwar firdauseey kuma yaune suke shirin komawa asibiti dan meron tsimbe saboda zumud'in ganin jikan nata datazo jia nan ta kwana gidan firdauseey kuma a bisa gadonta tayi shame shame a bisa uwa saniya wanda hakan tasa mukhtar dole barar musu d'akin ya kowa d'aya daga cikin d'akunan saman benen, dayake babu abinda babu a d'akunan dudda ba zamnsu ake ba. 6:22pm a hospital din tai musu suna nn zaune har saida lokacin yad'anja wajen 8 da wani abu sannan fa manyan likitocin suka fara shigowa asibitin cikin motocinsu, suna a haka saiga doctor sera ta shigo wato mamar yarinyar nan baturiya wacce ta rarrashe mukhtar jia dayaita faman sakin sambatukan kukan nn. Still 'yar tata raja tana biye da ita, raja iriyan matan nan masu 'yan mnyn shekaru a fuska amman jikinta ya b'oye mata hkn danko mama bata dasu yanda ya dace shiyasa ake kllonta qaramar yarinyane. bayan sun gaisa ne mmnta take cewa "kuna jiran doctor mezan ne ko?" "eh cewar mero data riga kowa harshen mgn a wajen, sai tace "ok to ku qara haquri nan da mintuna 10 zaku gansa" "ok ba matsala doctor thanks" cewar mukhtar su juya suka wuce yayinda meron tsimbe tabi 'yar baturiyan nan wato raja da kallo aiko saita bushe da dariya tana fadin 'o'o ni Allah mai halitta ita wannan jibeta da fuskar manya amman dubi qirjin kamar anyi shafen suminti akai... kanta qara cewa wani abu saiga doctor merzan yashigo aikuwa da sauri mukhtar da firdauseey suka miqe daidai nn doctor d'in ya iso garesu suka gaisa yajasu office dinsa ya aijye brifcase dinsa a side tareda zama kan kujera ya dubesu cikin fara'a yace"congrats ina tayaku murnar babynku ya samu lpia jia muka fiddasa a engies d'in yanzun kam bayada matsalar komi numfashinsa it's very very normal dan yanzun haka ma zamu iya zuwa ku d'auki babynku" tuni suka hau murnar gasken gaske kuwa sai hamdala mukhtar yake haka doctor merzan ya kaisu dakin da babyn yake ai mero na arba da tsantsar kyawun yaron saita dubi firdauseey tace" 'yar banza dole ki haukace kan jinjirin nn ashe? yaro kamar yasha hatimin annabi yusuf shima dai? itadai firdauseey batabi ta kanta ba shayarda yaronta kawai take kamar yanda doctor ya bata izini. sai kallon yaron suke Itada mukhtar sai wutsil wutail dinsa yake na jarirai cikin kayansa an kuma nadesa a showel kaida ganin babyn kasan lafiyayyen baby ne, yanda kasan ka tabasa jini yai tsartuwa haka yake, danba qaramin kyau ya qara ba akanma wanda aka haifesa dashi d'in . basu jimaba aka basu sallama da yake ranar suka kar6o babyn dan haka sai aka maida rad'in sunan yaron da kuma bikin sunansa rana ita yau watau Monday mai zuwa, tuni mero ta dunga fadawa yanuwa da aminan arziq'in haihuwar firdauseey kankace miye mutane sukaita shigowa ganin jariri kuma dud wacce tazo abunci da namomi da juice s saita ture kuwa dan masu aiki har uku mukhtar ya zube musu sannan dud wacce zata tafi sai an mata kyautar 1k sannan. aIkuwa shiyasa a ranar mutane basu katsewa zuwa gidan danjin labarin kud'in da ake badawa wane yaji ga wane knn, kai baka bayarba kaje an baka tomiyafi wannan dadi cewar mutane. koda wasa mukhtar bai taka q'afarsa yaje yafad'awa su baffa haihuwar ba dan tsanar sa da ismail bazai bari yaje gidan nasa ba, suma su baffan ya runtse idone kawai haryayi tunanin gaya musun bawai dan matsayinsu yakai ba na sujin a cewarsa, amman ya yanke hukuncin a ranar daren suna zai je wajenda su baffan ke firar dare saiya fad'a masa faqat yarage ruwansa yaje zanen rad'in suna ko kar yaje shidai yafita haqqi a ganinsa. saidai abinda bai saniba har su baffa ma sunji haihuwar saidai sukayi shiru abinsu batareda sunyi gigin tunkararsa da wani abu wai shi barka ansa mu qaruwa ba,suna masa adduar Allah raya. to mutumin dayace babu kai babu shi babu ahalinsa babu naku kuma ya hanaka taka gidansa tomi zakaje kayo? suna matsa yin iyayensa aisu yakamata yabi basu su bishi ba kodan gobensa tai kyau, dan haka inda bai zo ya fad'a da kansa ba ai huta roro waken gizo yayi 'ya'ya cewar