← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 178

Sashe 32

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

👁🥡👁 🅿1⃣8⃣ *W* lh bantaba jin inda akai wannan auran ba tunda nike, ace ranar rad'in sunan jariran nan take kuma a wajen a d'aura wa jinjirai d'in aure ba! wayyoni Allah na!" zubewa q'asan wajen yayi, yayi goho yana dukan kansa da hannunsa yana mai fidda zafafan hawayen baqinciki da takaici yana cewa"firdausy zokiji d'anyen hukuncin da baffa ya yanke mana a rayuwa wanda bai gam da muba"!!!!!! tunanin kawai toshi yanzun tayaya zai jewa da firdauseey da wannan zancen wane kuma hukunci zata d'auka a kansu baffan kuma in taji?? dole ya miq'e daga wajen yabar masallacin ko ganin gabansa baiyi sosai sakamakon wani mugun jiri da yakeji a lokacin, da qyar yasamu ya isa falon gidan nasa ya zube bisa kujera yana huttai. lokacin kuwa qarfe bakwai da mintuna 50 na safiyar ranar. gida yan suna suna waje sai ida hada delicious na abuncika akeyi da drinks kala kala. mai jegon ce ta sauko daga benan jikinta sanye da wani swice lace kaida ginensa kuwa kasan nera basai an tabbayeta ba gu siyensa, awarwaron mnyan zinarai ne sanye da hannuwan ta sai kunnen ta da wuyanta suma sun shaida nasu golds d'in kuwa. har kusa da mukhtar firdauseey ta zauna sai baza qamshi take ko ina. "yalla6ai yabaka shirya ba? ai yakamata kaje kai wanka ka shirya sosai inda an gama zanen sunan ko? dubnta kawai yake da kansa dake barazanar fashewa, shin tayaya zai iya dubn qwayayan idanunta yace an d'aurawa jaririnta aure da jaririyar 'yar abokin gabansu ne abin q'insu kuma mawai tukun? runtse idanunsa yayi bayan yasa hannuwansa ya shafo tundaga saman kansa har zuwa fuskarsa da wuyansa sannan ya sake dubnta daqyar ya iya furta "akwai matsala firdauseey" arazane ta dubesa, haba ba banza ba takejin faduwan gaba tun dazun kam, cikin tsurewa da faduwan gaba gamida rudewa tace "mi... Mmm. mim. mine ya faru kuma? dan Allah yi maza sanar dani wlh daman sai faduwan gaba nikeji ba kad'an ba" Saida ya qara sauke qarfaffan ajiyar zuciya, ransa bnda tuquqin baqinciki babu abinda yakeji, shifa jiyake daman mutuwa yayi ya huta dayasan zaiga wannan baqar ranar da har baffa zai iya jefa d'ansa gidan matsiyatan nan dan sake hada wata sabuwar dangan takar data wartsake kuma da jimawa ma. muryan firdauseey ta katsesa inda yaji tana fadin "haba mukhtar kawa girman Allah da manzonsa ka fad'a mun abinda ke faruwa danni ka barni a duhu babu kyau iriyar hakan fa" "baffa ya yanke mana mummunan hukunci yau firdauseey inda ya had'a auren khaleepa da 'yar tsinannen yaron nan isma'il yanzun nan bada jimawa ba a masallacin anguwar nan bayan gama rad'in sunan su" wata mummunan hantsilawa firdauseey tayi wajen miqewa wanda har kallabin dake kanta wanda tayi coge dashi wato wanda ake kira tunkud'esa kaga tsiya yana fad'owa qasa amman kota hakan bata biba dan kwanyarta ma ta daina aiki na wucin gadi jin maganar tai mata dirar mikiya a gaggauce kamar ana faffaska mata tafi takeji a kunci. bayan dawowarta hayyacinta tace "wai tukunna madai wane khaleepa din kake magana ne mukhtar???!! khaleepa na fa? " shi kansa abin mamaki yake basa dan tun sanda suka fara soyayya da firdauseey bata qara kiran sunnsa ba gatsal amman yau gashi sai maimaita mukhtar take a bakinta batareda taji ko d'ar ba, amman yasan dole tayi ma fiye da hakan ma a yau inda an tab'ota.. babu zato yaji ta cacumo kwalar jallabiyarsa tana girgiza wa da qarfi idanunta sun yi jajir hawaye na fita ta gefensu tana cewa"wadannan matsiyatan za'a had'a min d'ana da 'yarsu aure? ai wlh bazan yarda ba wlh sai an raba wannan q'addararren auren ko ai kashe kashe a anguwar nan" ran mukhtar a matuq'ar 6ace wannan karon ya fizge hannun firdauseey daga kwalan sa data shaqa, ransa ya b'aci da abinda tai masa matuqa dan yaso lallashenta amman jakin dinsa datai yasa yaji bama zaiba kuma bazai biye mata ba tsinuwar iyayensa tabisa ba a banza a wofi, dan haka ya dubeta idanunsa sun sake kad'awa sunyi jajir yace '' kije kiyi komi ma zakiyi nidai bazan bijirewa umarnin mahaifina ba inda harya tsine mun akan indai nasa aka raba auren nan" yana gama fadin hakan ya haura samansa ya wuce d'aki ya barta nn tana haukan 6a6atu, data gaji zubewa tayi wajen ta d'aura hannunta bisa kai tahau kururuwa tana fadin a ceceta dan gaba d'aya q'arar ihun kuknta ya cika falon gidan, aiko saiga mata 'yan suna wanda suka fara shigowa lokacin suka baro dayan falon da gudu suka shigo babban falon gidan suka isketa baje qasa dutta tuttuje kwalliyar jikinta ta yar qasa hatta dankunnen kunnenta shima bai tsira ba, ta 6alle zanen jikinta sai undie dogo kawai ta bari, ta koma kamar mahaukaciya dan yanda ta dinga kuka da hawaye shate shate gashi sai dukan knta take tana fizgar gashin knta dan azaba ko zafin hkn bataji ihu kawai take tana tsinewa su baffa tana sake cewa Allah ya tsine muku wlh, bazan yarda ba shegunayen mutane kawai wlh saina dauki mummunan fansa akanku gamida abinda kukai mini matsiyatan banza makwadaita, daqyar hajiya Hadeeza aminiyar firdauseey ta kori sauran jama'ar wajen ganin yanda sukewa firdauseey kallon mahaukaciya, suna fita tasamu ta kulle musu qofan falon ta dawo ta zauna kusada firdauseey bayan ta, samu ta rarrasheta tayi shiru daga haukan kukn nata da takeyi takoma zubda zallar hawaye kamar fanfo dankuwa banda zunga da zugugin ciwo babu abinda zuciyar take mata hatta kejin ma inazata ma iya hadiyan zuciya ta mace kota huta tunanin wannan mummunan qaddarar data samesu yau. Hjy Hadeeza tace "haba aminiyar miyasaki haka har kika janyo hankalin mutane kanki? dan AllAh kiyi haquri inma wani abinne ke damunki fad'a mun yanzun nan zami samu mafitarsa(hajeeya Hadeeza wata sabuwar aminiyar firdauseey ce wacce basu jima da dawowa daga anguwar ba dan itama tanada hali kamar nasu firdauseey din bata da son dangin miji bare iyayensa dan tsakanin ta dasu sai wulaqanci da fad'a kaca kaca kuma ta zagesu tas shiyasa batada farin jinin su kokadan gashi kuma ta hana dan uwan nasu qara aure dud tabi tayi kane da dukiyarsa sai fantamawa take da ita son ranta, daman ance sai hali yazo sannan ake mummunan abota gashi kuwa dan gaba daya sunsan sirrin junansu kaf hatta da mugun asirin da sikaiwa mukhtar na rabasa da iyayensa da d'an uwansa saida firdauseey ta fadawa Hadeeza, kuma itama Hadeeza ta fad'a mata tariga ta gama da mijinta alhaji bala, shiyasa yanzun kansu a hade yake battada amiyar data wuce ta itama haka. Kuma itama hajeeya Hadeezar ko kwana goma batai ba da haihuwa itama yanzun haka wannan kenan). dan haka firdauseey tana hawaye take cewa"masifa ta saukar min a wannan rana aminiyar babbama kuwa, gashi kuma mama mero taje qauye yau da sassafe dan kaka musa baida lpia bare na fad'a mata musan mafita dan Wlh bazan bar abinda akaimun ba, tab!!!!! Inkuwa har harma na barsu kenan ma sunshani a basilla" Hajeya Hadeeza tace ''nifa kin sani a duhu ki famitar dani man kona fahimta" Saida firdauseey taqara matse hawayen ta sannan tace "wannan mugun tsohon ne man baban mukhtar yatashi ya had'a d'ana aure da 'yar qanensa" zaro idanuwa hjy Hadeeza tai gaba d'aya sannan ta dafe qirji tace "badai isma'il ba teacher din nan?" "shifa wlh" "tab lallai kam indai hakane qawata an cutar mana yaro wlh, nida naso insun girma a hada su aure da 'yata zarah dan koba komi nera zata gogi nera" cikin quta qatuwa firdauseey tace "hmm gidan matsiyata? marassa shi?! masu jiran albashi sannan suci abinci?! nan aka bawa dana 'ya?! aka cusa masa?! yaron da baisanma uwar mi ke duniyar ba amman dayake jahilai ne q'auyawa shine sukai mana wannan yankan q'aunar" to wallahil azeem bazan haqura ba, qawata ki bani shawara, ko mubari mama mero ta dawo ne saimu makasu wajen boka marakusa aiki da cikawa? dan wlh shine kawai zai mana maganinsu" hjy Hadeeza tace "haba qawata kina dani fa a hannu kokin mnta ne? wannan tsoffin kingin mutuwa har sai mun wani sha wuyan zuwa wajen boka a kansu? ai wanna aikin naki ne ke zaki yisa da knki" cikin mugu mugun mamaki firdauseey tace "kamarya kenan aminiyar kefa bom ce wlh" hjy Hadeeza tace "hmm kawo kunnen ki kiji aminiyar " nan take kuwa firdauseey ta miqa mata kunnen ita kuma tafara d'ura mata mungun nufinsu akansu baffa. tana gama fad'a mata kuwa suka kashe da tafi firdauseey tace"kai naji dadin wannan zazzaqar shawarar wlh kuwa" hjy Hadeeza ta karkace baki tace "hm in kikai hakan sai muga tayaya zasu qara ganinsa bare har su sashi wani abu makamancin haka, ahto yanzun kuma dai aiki ya rage naki sai yaushe zaki qaddamar musu dashi ne?" firdauseey tace "a daran nan danma wannan jama'ar da ke gidann da yanzun zanje na gama aikin aminiyar sake tafawa sukayi hjy Hadeeza tace "hknm yayi abarsa a daren dan zaifi sirri, amman da har zaki wani tsaya b'ata mana ranki akan wasu banzaye qananun qwari, sannan kuma kada ki manta kiwa Alhj mukhtar managar danai miki" babu matsala qawa kedai Allah barmu tare kodan shawarki mai wuta. dariya suka qarayi nan sukaje daki ta qara shiryawa kamar ba itace ta gama borin ihun kuka ba, dan haka koda suka isa cikin jama'a kowa ya tambayeta abinda ya sata ihu haka d'azun amsar da hjy Hadeeza ke basu qadangare ne ya shigo falon ya firgita ta,sudai jinta kawai sukai dnbasu yarda ba. ahaka akaci gaba da buduri da bured'e d'e na suna awunin ranar. hankalin firdauseey kwance danta gama samun matsaya ta ramuwa da maganinsu baffa. baffa kuwa koda ya koma gida nan yatarasu isma'il da zainab harda inno zaune a wajen ya fad'a musu auren daya daura tsakanun jikokin nasa dan qarfafa zumunci, matuqa gaya inno taji dadin hakan har taita sanya albarka ga auren jariran kuwa harma tarasa inda zata tsoma ranta dan murna nan take taje tai alwala ta bada nafila dan nuna jin dadinta ga faruwam hakan. yanzun tunaninta ya tsaya cak na cewa zumuncin mukhtar da d'an uwansa yanzun ma aka farasa kenan, bisa ga da datai tunanin zumunci ya datse ganin mugun halin da mukhtar din ke tsurowa
Chapter 32 · 0% Book details