← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 178

Sashe 16

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

👁🥡👁 🅿1⃣1⃣ *W* asa wasa yau kimanin wata uku knn da fara aikin mukhtar, buhunnan shinkafa dasu kuskus macroni superghety indomi sha'er da dai sauransu haka mukhtar ya cikawa su baffa d'aki dashi,kuma haka shima yaje gidan ismail ya cike masa waje ma'ajiyar abincinsa dasu taff, hatta abokan baffa su baba yawale saida suka shaida da arziq'in mukhtar dan saida yayi musu kyauta suma, kan kace mi tuni anguwar ta dauka labarin cewar mukhtar yayi kudi, alherin mukhtar bai yankewa ga jama'a shiyasa kowa zakaji yanda yake yabon kirkinsa a anguwar sukance sam baida qyamar marassa shi kamar yanda sauran masu kud'i sukeyi,, tuni mukhtar ya sabarwa kansa dud ranar juma'a bayan antaso masallaci zakiga ya zauna a qofar gidansu shida ismail yana bada sadaqar Dari biyar biyar yayinda ismail din ke tayasa,, bazai bar wajen ba har sai ya tabbatar da kowa kuwa ya samu sanna. salis yaji dadi qwarai da arziq'in abokinsa da Allah ya basa shi a cikin dare daya shiyasa shima mukhtar yaso salis din yabar aikin da yake yazo nan ya basa wani aiki ya dungayi a ma'aikatarsu amman sam salis yaqi yarda danshi a ganinsa mutane zasuyi surutu gameda hkn shi bama wannan ba yafiso ya samu aiki da qashin kansa kamar yanda shi mukhtar din ya samu kunga kowa saiya tsaya kan qafafunsa, dan salis yana tsoron ai masa alafama gudun juyin rayuwa iriyar na mutumin yau. shima yasan bai fidda rai ba, inda shima ay ya bada takardunsa tuntuni cigiyar aiki gun wani qanen mmnsa dake bauci shima ma'aikacin government ne, danma ya riga bayarda cigiyar aikin nasa akan mukhtar daya bayar daga baya, mukhtar kuwa ganin salis yaqi amince wa hakan ne ya sashi haq'ura dole amman kam yana masa kyaututtuka matuqa dan kaf fadin garin kaduna baida babban aboki sama da salis. yau lahadi ta kama weekend kowa yana gida babu fita, mukhtar ya na zaune a dakinsa yana faman cike wasu daga cikin takardunsa n office, dan kam gaba daya hankalinsa ya tafi ga wajen lissafin abubuwan da yakeyi, saiga firdauseey ta fito daga quryan daki jikinta sanye da wata atamfa super English ta zauna kusa dashi fuskarta ahad'e ta dubesa tace "yalla6ai ina son magana dakai" bai dago kai ya dubeta ba saida ya ida had'e dukkan calculating din sannan ya kauda document din gefe ya juyo y zuba mata idanunsa yana kallonta cikin wani murmishi, hannunsa yasa ya kamo nata yace "ehm emmm to sarauniyar mata, amman kafin nan wai miye sirrin ne? nike ta jinki zam zam haka kwanan nan?, gashi kuma kin d'anyi haske dudda kalarki choculate color ne amman ta q'ara smooth fa sosai, kodai da ajiyar baby nane anan?" yayi maganar yana goga kuncinsa a saman cikin nata cikin wata fara'a. ture kansa tayi tace "nidai ba wannan ba dan Allah ka saurareni dan maganar nada muhimmaci sosai,, tuni ya maida nutsuwarsa gaba daya gareta yace " to ina sauraranki" saida ta qara bata fuska tace "yanzu dan Allah yalla6ai dud iriyar wannan arziq'in da Allah yai mana yanzu mu ba abin kunya bane aganmu cikin iriyar kalar wannan dandaqaqqen gidan ba? dud gurori a cikin wajensa? kuma gaskia byn haka ma gidan nan yayi kadan dan inna haihu taya mutane zasu wala a cikinsa ma tukunna dai wai?" sai lokacin ya yi saurin cewa " oh my god,, are you pregnant my Queen? kinada ciki ne daman baki gaya munba?, yayi maganar cikin mamaki,, wani dan murmushi tayi tace "jia munje asibiti nida mamana sakamakon zuwa danai gida daga naci abinci naita amai kamar zan mutu wlh lokacin shiyasa hankalin maman ya tashi tasa mukaje asibiti a lokacin anan doctor ya min gwaje gwaje har suka tabbar da ciki ne a jikina d'an kimanin wata shida da kwana hud'u" da sauri mukhtar ya rungume ta yana firda qwallan dad'i tareda godia g Allah da sauri ya ruq'o ta jikinsa yana fadin "firdy na mikeso na miki wanda zaisa kiji dadi dan wannan kyakkyawan albishir da kika zomun dashi?" cikin kwarkwasa firdauseey ta wani karkace kai tace "nidai kawai inason mubar ckn anguwar talakawan nan mu koma layout da zama inda bb hayaniya can bare su hanani renon baby na cikin pic nutsuwa" sakato mukhtar yayi kawai yana kallonta yace cikin tsabar takaici "inbar iyayen nawa ina da d'an uwa na to inna bar anguwar?, look bari kiji inke baki son zama kusa da iyayen ki da 'yan uwanki toni inso domin hakan shine bugun numfashi na, kuma wannan gidan da kike cewa bakkya sonsa toni bnda kamarsa a abinso na gida inda kudin mahaifina ya zuba a ciki ya siyamun ba kudi na ba gashi kuma har kin rayu cikinsa dan haka ina alfari da kyautar mahaifa na kima sani i don't go anywhere I swear"! yayi maganar ransa a d'an bace. tuni firdauseey tafara matsar kwalla tace "hmn ai nasan daman haka zaka ce kai kenn da an yi maka magana zakace iyaye d'an uwa towaye baida sune?" nan taci gabs da kukanta, wanda a zahiri ba kukan amsar daya bata takeba kukan tsabar baq'inciki take yanda yadamu da iyayensa da d'an uwansa bisaga ita matarsa shine kawai fa faman cin ranta. "kiyi haquri fiedy na, bawai gidan bane bazan fad'ada saba na gyara no oready dmn na yi magana da masu qaton filin nan na kusa damu akan zan siya kinga saina qara fadada mana gidan namu amman gskia na fad'a miki bazan tashi daga anguwar nan ba, danko wajen aikinmu da sukace munaso a bamu d'aya daga cikin gidajen government mu zauna da fami namu ko kudin mukeso, tonidai gskia kudin na buqata kuma suka turan a account dan nikm bazan bar mahaifata ba ina nan da'iman hayat" kamar tai kukan baqinciki najin wai anbasa kyautar aljannar duniyar gida amman sabida wannan gajarabils d'in tsoffin ya qiya, q'utawa tayi ta danne 6acin ranta sumburo baki tayi tace "naji to ammanfa to gskia inka tashi gyara mana gdn harda fa benaye nakeso aimana ciki a ko'ina?" yayi wani guntun murmushi yace "kada kidamu komi za'ayi dan so nike nasa ayi gyaran dasu baffa ne da Ismail suma a fad'ad'a musu gidajen nasu amasu gyaran zamani suma" tuni wani gululun baqinciki ya sake tokarewa firdauseey maqoshi a karo na barkatai har batasan sanda ta fashe da kuka ba, da gudu tabar wajen ta koma d'aki. binta yayi ya zauna gefenta yace "mike kuma ske faruwa ne haka wai firdy na?" sam taqi mgn dud nacinsa haka ya haqura ya bar d'akin kai tsaye waje ya fito ya nufi gidansu tun a hnya mutane suketa miqa masa qoqon bararsa mabuqata, yakance musu su bari saiya fito daga gidansu sannan, yana isa kuwa qofar gidansu ya zaro wayarsa jikin aljihu ya kira ismail babu jimawa ya daga yace "q'anena kana mainhouse namu ne koko? daga can ismail yace "a'a wlh yaya na muna kan hanyar dawowa nema daga hospital yanzun ma haka" da sauri mukhtar yace "subhanalla waye babu lpia?, baki har kunne Ismail yaketa dariya yace "Zainab ce mukaje anso result wajen doctor yayana" "result nami knn?, cikin kunya yace "ay ciki ne gareta yaya, da sauri ya kashe wayar waishi kunya, murmushi kawai mukhtar yasaki yarasa yanda akai dud alherin daya samu d'an uwan d'aya to shima dayan babu shakka zai samu kwatan kwacinsa alherin Allah kenan hakan. cikin gidan nasu ya shiga ya zauna gefen baffa dake kishingid'e a bisan tabarmar kabarsa yana sauraron radio dinsa. baffa ya amsa gaisuwar inno ta fito daga d'aki ta zauna saman kujerar qarfe 'yar tsugunno bayan ya gaisheta yace "baffa magana nike so muyi,, baffa yace "to shiknn mukhtar ina sauraron ka" yace "baffa daman in bazaku damu ba zan yi muku gyaran gidannan ne dana Ismail amman baffa nayi magana da mai shagon nan nakusa da gidan namu akan zai siyar mun dashi sai a rushe ginun gidan ayi muku sabon gini na zamani asamu foundation sosai" kan baffa yace wani abu saiga Ismail ya shigo gidan da sallama Zainab na biye a bayansa, bayan sun zauna suka gaisheda su baffa sannan Zainab ta koma dakin inno ta zauna, btatare da yn qasa a gwiwa ba mukhtar ya sake maimaita wa Ismail maganar rusau na gidajen nasu da yake shirin yi, baffa yace "mu wane gini zaka sake yi mana kuma mukhtar bayan wannan? kai dai Allah shiyi albarka kaji ko? tsufanmu da wannan gidan ya dace" yayi maganar cikin fara'a, inno tace gskia dai kam kadai gyarawa dan uwanka danshine d'an zamani mu kuma muna kurkusa da q'abari tsufa ya kawo jiki inamu ina wani kayan qawa na duniya,, hidimar da kake damu ma mun gode Ubangiji Allah shi sanya alheri a arziq'in mai amfani gaku da kuma jama'ar annabi Muhammad SAW ya qara muku bud'i na alheri kuma" dukkansu suka amsa da "aminn mukhtar ya kalli inno yace "dan Allah inno to koda baku yarda na siyi shagon nanba na hade muku dashi to ku bari na gyara muku gidan asa tayils da esi da sauran kayan more rayuwa a ciki dan Allah baffa,, da sauri Ismail yace "hakane dan Allah su baffa ku amince ma burin yaya in bai muku ba a duniyar kukaji dad'i miye amfanin samuwar kud'in?, dan Allah mun roq'eku ku amsa masa da to kada kuce masa a'a karo na biyu"👏🏻 ya qarshe maganar tasa yana mai hada hannuwansa biyu alamun roqonsu. sauke ajiyar zuciya baffa yayi ya dubi inno tai masa alamun ya karb'a musun, gyaran murya yayi yace "to madalla mungode Allah saka muku da alheransa" cikin jin dad'i q'warai suke amsawa da "Aminn baffa" inno ko murmushi kawai takeyi daga nan kuma mukhtar yasake gyara zama yace "kuma baffa hajjin bana hardaku za'aje insha Allah, dan na tsara mana tafiyar ne kaida inno, Ismail da matarsa sai kuma nida firdauseey insha Allah, tuni fara'ar dake fiskar iyayen nasu ta qara qaruwa sukaita zuba musu addua kamar ba gobe, baffa da inno harda qwallan farinciki suka share na ganin cewa ashe sunada rabon taka qasa mai tsarki ta sanadiyyar yaransa lallaikam haka abun yake zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana muzuru ana shaho sai yayi. ai ismail rungume yayansa kawai yayi yana faman kuka kashirb'an yana cewa "dukiyarka kada ta
Chapter 16 · 0% Book details