← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 178

Sashe 37

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

👁🥡👁 🅿2⃣2⃣. *Z* ama sukai nan kan buzunsa. baba isma'il cikin maganarsa yanda bazai takura baba yawale dake halin sallar ba ya dubi heenduh yace "heenduh gskia kam haruna yaron kirkine dubi fa dan AllAh iriyar alheran magunguna daya bamu haka d yawa batareda ya kar6i ko sule namu ba" baba isma'il yayi maganar yana mai cigaba da duba sunan magunguna, itako heenduh ta6e 'yan red lips d'inta tayi tace"baba dan ya bamu wannan 'yan magunguna din, shi yaga dama ya bayar ai ba wai dole mukai masa ba, to dan haka ni banga abin a jinjina masa ba inda dai shi yaga daman badawa ba kuma uzzurasa mukai ba ko babana?" d'agowa baba isma'il yayi ya dubeta ya girgiza kansa kawai yayi murmushi, sam shikam wnn halayen n heenduh wani zubin yakan kasa fassara mata su da awane matsayi ta dauki kanta?, yanaga heenduh data fito tsatson masu arziq'ina iyaye to daba haka ba, shikam ya godewa Allah dabai basa mahaukatan kud'i ba da zaisa 'yarsa tana jin ita watace wataqil har hakan yasata yaga jama'ar annabi danya kula diyar tasa akwai son taq'ama kalar ta 'ya'yan manya na masu dashi, banda haka har yausher wanda yai maka abun arziq'i ita a nufinta abun yayi qanqanta da agode masa knn koko?, murmushi ya sakeyi yace a ransa ''heenduh wannan halin dai naki ba nawa bane bana mamanki bane heenduh,, hmm rigimammiya ta, yarinta ne kawai ke d'awainiya dake nasan wataran zaki yi hnkali ki daina dud randa kikaje dakin mijinki zaman aure har kika fara hayyafa, ina roqon Allah daya bani qarfin gwiwar ciyar daku da tufatar daku batareda gajiyawa ba har na gaza ya rabbu nakaiga sarewa ba amimn, hmmm rayuwa knn, lokacin daya tuno su baffa da inno da kuma abubuwan da sukaita faruwa na lokuttan farinciki da iyayensa da yayansa mukhtar amman yanzun gashi yazamo kmr ba aiba sam, Allah ya kawo mana qarshen abin. "aminn babana" cewar heenduh baisan addu'ar tasa ta fito fili ba. sauke qarfaffan ajiyar zuciya yayi sannan ya dubeta heenduh yace "q'warai kuwa heenduh haruna ya cancanci godiya matuqa nidai a wajena, dan dayace kud'i zai kar6a da bansan yanda zanyi ba inda bani da isassu na siyan adadin yawan iya magungunan daya bani dan dud nayo siyayya da kud'in a kasuwa, duka duka a cikin aljihun nan nawa in q'ididdige kud'in ma zanyi sam bazasu gaza naira d'ari biyu da saba'en ba, to ki gayamun d'ari biyu da saba'en zata saimun maganin ne har haka kala shida fa heenduh na? kan heenduh ta ce wani abun sai sukaji muryan baba yawale na furta cewa "assha ya ilahi isma'il rauni kaji haka dayawa ne a q'afa?, juyowa baba isma'il yayi cikin q'ara sakin fuskarsa yace "wlh kuwa baba abinma yazo cikin sauq'i kuma, na fad'a rami mai kwata ne batareda na nasan dashi ba a wajen" baba yawale yace "ayya Allah kyauta gaba to" "amunn baba, daman munje dreesing ne nida heenduh ta raka ni to shine nace bari na daure na shigo na gaisheka daman naga ban shigo gaishen ka ba yau sammakon zuwa kasuwa saro kayan miyar da nayi" baba yawale yace "ai daka ma zaman ka isma'il dan ciwo ai ya kauda komi ko" murmushi baba isma'il kawai yai baice komi ba, baba yawale yakai dubansa ga heenduh dake 6oyewa bayan babanta dan tasan tsiyar data zo ta shuka ma baba yawale din d'azun bawai mntawa yayi ba, dan hk ya d'aga carbinsa kamar gaske zai shauda mata aiko ta fasa q'ara ta ida shigewa jikin baba isma'il tana fadin "wayyo mairan qarfe kayi haquri,(sunan da take kiran baba yawale dashi knn) baba isma'il najin hakan yasan da abinda tai masa kuwa sababbar, dan haka saiya fara dariya yana qoqarin rabata da jikinsa ya nufi miqawa baba yawale d'in ita amman taqi yarda da hkn, jiyayi baba yawale yace ''kaji ja'ira 'yar albarkar yarinyar nan isma'il d'azun waini zata firgita batasan indai wannan tsoron ne ni maraba nike dashi ba konaje na tadda abokina ba dahar gobe rashinsa baibar bimin jiki naba (baffa marigayi), miq'o mun ita na tsautsaula mata carbin nan inda ta maisheni kakanta na rugar su, wai fa in gaya ma isma'il yarinyar nan kawai tazo lafemun a cikin quryan daki ta sake maq'e waccen qaramin muryar tata wai itace mutuwa idan na shirya yanzun zata d'aukeni sauri take dan akwai sauran wujajen da zata je amman nine na farkon ziyara shiyasa tafara yowa nan wai na jima ban tafi ba yanzun lokaci na yayi... haba baba isma'il dariyar abun kawai yake da gudu heenduh ta hantsala ta miqe tsaye ta nufi q'ofa tana haki ta tsaya ta juyo ta dubi baba yawale tace cikin qyalqyatawan dariya wacce har fararen haqoranta suka fito reras dasu gwanin burgewa "cab kujimin tsohon nan nizai daka da wannan dogon carbin yasamun ya fasan jiki ya cuci masoyina ta66 walle kam Yaseen bazan tsaya ba wlh kuwa,, mairan qarfe naso ka tsorata ka gudu insha dariya a d'azun din nan ay" girgiza kai baba yawale kawai yayi yace"hmm kedai kika sani ay da shirmenki zan kuma riqeki da hannuna in saki mari sai maaoyin naki yazo belinki kinga daman sai ingansa inda daman rowarsa ake mana,dariya heenduh tai tace "ko aiko indai masoyina na haqiqa zaka gani kenan kana da sauran kallo a gaba dan ni kaina ban sansa ba bare na sanarwa wani dashi shi" yatsina fuska baba yawale yai yace "zancen 6ur knn, ashe abunma dud wobuwa ce da hayaniya, inda dai bakida saurayin kizo na taimaka miki mu qulla auran nan namun nan" turo baki tayi tareda juya fuska gefe bayan ta kaso kallabinta har goshi sannan taxe ''ta6 Saidai na had'a ka da goggo dahara( wata tsohuwa ce nan maqotan su heenduh dun take mai saida zogale da kuli kuli da man gyad'a kuma, batada miji danta daya kuma ya rasu ita kadai ce zaune a gidan sau tari sa'a da heenduh can suke zamansu na fira dan sun saba da ita sosai. qyaleta baba yawale yai yadanyi murmushi tareda duban isma'il din yace "yarona isma'il tashi jeka gida haka ka huta rabu da shirmen heenduh, Ubangiji Allah ya sawwaqa kaji" "aminn baba'' cewar baba isma'il yana mai miqewa tsaye a hankali da qafar tasa, saida ya fita sannan heenduh ta juyo ta kalli baba yawale ta kashe masa ido guda d'aya na tsokana tace ''byeee mai ran qarfe sai gani na uku ko wajen kawo sabuwar ziyara dan nasan ka tsorata kadai mazge ne ka b'oye walle kuwa" yunq'urowa baba yawale taga yayi kamar zai nufota da doguwar carbin nan nasa aiko ta d'age siket dinta na atamfar nan sai kusada babanta dayake gabda shiga gida ta dura, dariya kawai take tuntsurawa dan matuqa takejin farinciki dud intana wajen baba yawale, wataran suyi firar arziq'i abinsu hankali kwance, intaja ruwa kuma nan take firar tasu zatai kwab'a ya korota gida. suna shiga gida suka iske mama zainab zaune nan inda suka barta tana q'oqarin tashi zaune ne da sauri heenduh ta q'arasa ta riq'eta tace "sannu mama jikin yayi sauq'i dai ko? "yaya jikin naka mlm?"! tambayar da mama taiwa baba isma'il knn dan sam ita tafi damuwa da nasa ciwon akan nata. ''da sauqi zainabu dan wajenma da akai dreesing ya rage ciwon ba kamar d'azun ba da jinin ke zubowa" cewar baba isma'il din. sosai mama zainab taji dad'i dan ya q'ara kwantar musu da hankalin da kansa ya tashi yaje ya d'auko musu zazafen tuwonsu na jiya wanda heenduh ta d'umama masa d'azun. saida ya matsa sannan suka sa hannu sukaci dan mama Zainab baifi datai ci biyar ba taji cikinta na zafi dole ya haqura ya barta tad'an kwanta nan babu jimawa barci ya kwasheta sakamakon magungunan ta data sha wanda khaleepa ya bata. bayan baba isma'il ya wanko hannunsa ya dawo ya zauna nan kan tabarmar ya dubi heenduh dake gyarawa mama Zainab lullu6in zanen data yane jikinta dashi yace"heendatu yau bakije school bane banga kinje ba?" saida ta d'an lawangwa6e kai sannan tace "eh baba bamuda lecture ne yau sai gobe sanna" sauke ajiyar zuciya baba isma'il yayi yace "to shiknn Allah shi kaimu lpia" "amunn baba, kaima ya kamata ai kaje ka huta kan akira la'asar, tayi maganar tana duban qafar tasa. miqewa tsaye yayi yace "hakane heenduh na bari na shiga d'aki to na d'an runtsa dan na gaji sosai" "to babana afuta lpia saika fito" daga haka ya wuce ita kuma taje ta kai kayan gwarin baba ma'ajiyarsu daga saman hnya data d'auke su, tana gamawa ta dawo ta d'an kwanta nan q'asan wajen tabarmar da mamar ta ke akai tana danna 'yar q'aramar gwaramar wayar nan tata tna tunanin miya hana sa'a kuma zuwa ne har yanzun?". Khaleepa kuwa suna barin gidan saida ya jima nan zaune q'ofar gidan su shida su yunus sannan ya kwashi laptop d'insa da jikkarsa ya wuce cikin gida. main falour nasu ya wuce kai tsaye saman dakinsa ya haura ya zube saman mahehen gadonsa laptop d'in na saman q'irjinsa idanunsa lumshe sai dan ya matuqar gajiya yau da aiki dudda ya kama ranar weekend ne kuwa amman saida ya fita aiki tun safe. wanka kawai yake son yayi koya samu jikin nasa ya warware masa gajiyar daya kwasa, bazato bare tsammani sai jiyai kawai ana shafa masa gefen kwantaccen sajen fuskarsa zuwa sumar kansa wacce ke kwance lub lub a saman kansa baq'a q'irin da ita kuwa wanda kaida gainta kasan ba qaramin kashe mata kud'i guy d'in yake yiba wajen gyaranta, jin abun yaqi qarewa yasa da sauri ya bud'e idanunsu amma still yanadaga kwancen sa bai miq'e ba, caraff suka had'a ido da zarah 'yar hjy Hadeeza aminiyar firdauseey. sosai ya tamq'e fuskarsa bayan ya miq'e tsaye ya zuba mata idanunsa fess bumisa fuskarta a kausashe, tuni jikinta ya fara shaking dan ganin mummunan kallon da yake binta dashi, wai ita yaya zatayi da son khaleepa ne a rayuwar ta? tana tsoron fa kada hakan ya illata mata zuciya da yawan tunanin da zuciyarta takeyi na kaikawo a kansa, har jitake a iriyar sonda take masa babu abinda zai nema a gareta ta kasa mallaka masa shi koda kuwa gangar jikinta ne ya nema ta tabbatas
Chapter 37 · 0% Book details