← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 166 OF 178

Sashe 166

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

bunsuru biyar shima, Snn akayi aikin wanda aikin anyisa ne Dan dud wata qaddarar taka na gajeta na mallake ta, kuma hakan akayi,, kuma musabbabin abinda yaje famu cikin wannan tashin hankalin ayau bakomai bane face kai heenduh da iyayenta da kuma dud wani wanda keda saka hannunsa a lamarin auranta da khaleepa da'a kaudasa, haka muka fadawa mlm lamma kuma ya'amunce yabamu magani da gargadin cewa kada a samu kurkure wajen aiki da maganin dan indai aka samu akasi khaleepa bai qetare maganin ba har wani ya qetara to zamu shiga taskun bala'e da musifa kamar yanda shi mlm d'in ya fada,, to munsan tabbas zarah tasaka maganin a ba daidai ba shiyasa hakan ta faru damu, Dan Allah alhj ku yafe mana koma samu sa'ida a jikinmu dan munsan alhakinku ne ke bibiyar mu..wayyo Allah,, suka sake fasa wani ihun nan take" alhj Bala da tun sanda yaji hjy hadiza na wannan maganganun jikinsa yadunga rawa da karkarwar cin amanar da hjy hadiza tai masa a rayuwa, amman shine dan bata da kunya take neman gafararsa,,,, aida gudu sukaga alhj Bala ya fuzgo hjy hadeeza yadunga bugata da bango yana nanata da qasa tana ihun neman ceto, wanda nanma zarah ta miqe babu zato sukaga taje gaban uwar ta danneta tareda shaqota daga kwancen da alhj Bala ya kaita wanda daqyar su dady mukhtar suka janyesa dan makasarta kawai sukaga yana bid'a . zarah maye gurbin alhj Bala tayi ta sake shaqe uwar tana kuka take cewa "kincuceni kin batan rayuwa, ashe dama ni ba 'yar dady bace shegiya ce? wlh to nice ajalinku daga ke har tsinannen bokan mahaifin nawa dakikayo cikina wajensa,,, ganin da sukai tana niyyar qarasa uwar da shaqar mata maqoshi datai ne da zaqa zaqan akaifanta dahar tafara fasawa uwar wuyanta dasu, hakan ne yasa su dady sales saurin janye zarah daga jikin uwar tata wacce idanuwan hjy hadeeza sunfito luhu luhu tana tari tul tul tul na azababban zafin dake ratsata kota 'ina a jikinta kuwa,,,, zarah ko sai kuka take tana darjewa da cewa ita a suketa saitaga bayan uwar,,, hjy furdauseyy kuwa dud abinnan da akeyi ta makure kanta waje daya tana kuka sbd yanda takejin cikinta kamar ana faffaska mata 'yan hanji ana karkatsesu,, gashi ko motsi ta kasayi sbd jikanta babu Inda babu karaya a cikinsa,jiyowa sukai hjy furdausey na cewa daqyar cikin kuka "toke hjy hadeeza mima kika aikata? komi kika aikata bai kamo koda qafa qafar nawa wajen muni ba, nida har kisa saida na aikata....... laifuka munana babu wanda ban aikata ba, babu shakka inaji a jikina babu ni ba samun rahman ubangiji Allah domin wadanda na zalinta basu duniyar ma gaba daya,, wayyo kaicona ni furdauseey, nasani babu wanda ya jefani a wannan mummunan hanyar bayaga mahaifiyata kanta rasu,, ina roqon mata Allah daya qara mata nauyin qasa...... fashewa tai da kuka wiwi takasa ma cigaba da mgnr. dasauri baba yawale yace"kashh subhanillah,,, furdausey ai komi mahaifiyarki ta aikata baici kimata wannan mummunan fatan ba ay, cikin kuka sosai hjy fursausey tace "nayi mata d'in yawale,, narantse da Allah bazan mata addua ba, Dan bata cancanceta ba, baka san abinda tayi a duniyar taba ne shiyasa kake cewa na daina mata wannan fatan,,,, kamar abin hauka sai kawai sukaga kukan hjy fursausey ya koma wata mahaukaciyar dariya, dariya take sosai kalar ta fitar imanin nan kuwa, nan take kuwa cikin haukar dariyar tata tahau watsa musu jimammen boyayyen sirrinta na munanan gsken kuwa, tundaga farkon zuwansu wajen marakusa itada uwarta sbd raba mukhtar da kowa nasa har kawo kisan da taiwa su baffa da inno ta hanyar guba data saka musu a abunci har kawo dai yau da dubunsu ta cika, tana gama fadan hakan tasake sakin ihun sbd yanda taji ciwukan jikanta ke mata wani mummunan addababben zunga da rad'ad'i. daga baffa dake babbansu a wajen har kawo khaleepa dake qaraminsu Suman wucin gadi sukai dan tsakanin mamakin daya kashe su najin abinda hjy fusrdaseey ta gama furtawa,, su daga kan daddy mukhtar har kawo baba isma'il da baba yawale babu abinda sukafi jin shigarsa jikinsu fiyeda yanda ta furta kisan su baffa, babu wanda ya ankara da ganin tashin dady mukhtar saidai ganin sa sukai ya dawo da wata sharbebiyar wuqa ya nufo hjy furdausey da'ita a guje,,,,, wani mugun ihun hjy fursausey ta saki dan ita kadai taga ya nufo da wuqar tsirara, tabbas tasan tata tazo qarshe yau dan abinda ta jima tanata shukuwa shine yake tanbayar ta yau haiqan,, gashi bazata iya ko motsawa daga Inda take ba bare ta samu matsera, dasauri su dady sales da baba yawale gamida khaleepa suka daddafe dady mukhtar din da jikinsa ke ciri yana fidda gumi gamida zubar da hawaye sharr sharrr,,, kamar yaro dady mukhtar ya dinga kuka riris yana fadin "innalillahee wainnailaihirraji'un,, haqiqa kin cuci rayuwa ta furdausey,kinmin tabon dabazai taba gogewa ba a zuciya, kin rabani da dan uwa na na tsawon shekaru amman dud wannan bai miki ba saida kika dan gana da kashe mun iyayena ta hanyar zuba musu guba a cikin abinci... wani kuka ya fashe dashi tareda isa gaban baba isma'il ya riqesa da qarfi yana cigaba da kuka uwa lokacin yaji mutuwar nahaifansu, dan abun sabo fil ya zo musu,dan shima baba isma'il banda kukan babu abinda yake cuzga,,, hakama mama zainab data tuno zaman dad'in da sukai dasu inno,,, cikin rawar murya dady mukhtar yake cewa "wlh qanena bazan taba yafe haqqin su baffa fa koda dukiya ta zata qare gaba daya sainaga an zartarwa da furdausey hukuncin kisa itama sannan hankalina zai kwanta,, bazan yafe miki ba fursausey dan haka mataki na farko dazan dauka a kanki shine kije na sakeki saki uku...."!!! ai wani kuka mai qarar gske hjy furdausey tasaki tareda fadin '' tashiga ukkunta ta lalace, Allah tofin Allah wadai da rayuwarta,, haka take fad'a. tuni khaleepa ya duqe qasa tareda dafe kansa yana kuka sosai, ko a mafarki bai taba tunanin mahaifiyarsa ce keda wannan munanan halayen ba, gaba daya jiyai duniyar tayi masa mummunan duhu,, banda dokawa babu abinda zuciyar sa ke ya matuqa gaya a lokacin jiyake kmr zaibar duniya ne sbd tsantsan tashin hankali .... wani qatuwar murya suka juyo awaje tareda bankado gate din gidan an shigo,,, kamun suyi wani motsi sai ganin mlm lamma sukayi dudus ya fado falon daga shi sai dan tohi a jikinsa,, hjy hadeeza na ganinsa tuni haukan ta yaqara tuburewa ta miqe tsaye tana qyalqyata dariya tana nuna mlm lamma tana cewa "hhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhh zarah ga ubanki nan yazo zai tafi dake wajensa,,, katsewa mgnr tata tayi babu shuri, sanda taji mlm lamma d'in ya kwatsatsa wani uban ihun tareda Buda hannuwansa sama yana fadin"dan tsito ka sauqaqamun wannan bala'en da kk mun a jiki,,, waiiiii huhuhuhu waiiiii huhuhuhu, tuni sukaga an daga mlm lamma an bugasa da qasa tareda curesa aka kanannad'esa waje guda jini na fito masa ta baka ta hanci ta kunne, dan wannan faduwan da baqaqen aljannun sukai dashi qasa harsun fasa masa qwalwan kai,,,, kowa ja da baya yayi a wajen ganin yanda wuta ta fara cin jikin mlm lamma,, da gudu sukaga mlm lamma ya miqe yana qwala ihu yake cewa "narantse da ubangiji Allah mai gaskiya bazan mutu a wukaqance nid'ai ba,,, babu zato kawai sukaga ya kwashi hjy hadeeza da zarah yafuce waje dasu a kafada a guje kuwa,suko ihu kawai suke suna neman barin jikinsa amman yariqesu gammm kmr danko, da yake mlm lamma sangama sangaman mutanen nan ne,, to ganin haka yasa su dady mukhtar suka yo waje da gudu suka biyo su,, saidai ina gudu ba daya ba bare gudu kalar na turin iska, shiyasa nan da nan kankace qyat har mlm lamma yayi wankan tsarki ya afka dasu hjy hadeeza da zarah dashi kansa zuwa wata tsohuwar rijiya mai zurfin gaske dake can tsakiyar anguwar tasu dady mukhtar, wacce babu komi a rijiyar face gama gaman duwatsu dake cikinta, dudda an rufe rijiyar ne da wani qarfe amman zuwan mlm lamma d'in duka daya da yayi mata da qafa yasa murfun ya 6alle har sukayi nasarar ruftawa ciki, wanda qara daya su hjy hadeeza da zarah dashi mlm lamma d'in sukai a cikin rijiyar basu qara wata ba, tuni mutane suka fara taruwa a wajen ana salati,, dady sales ne yayi qoqarin fiddo wayarsa nan take ya kira fire service, 'yan kwana kwana,, babu bata lokaci kuwa saiga motor 🚑 ambulance ta' yan kwana kwanan ta shigo anguwar a guje tana jiniya,, kankace MI har an saka qugiya da fitilu an shiga an fiddosu dukknsu an kwantar nan qasa, gaba daya jikinsu ya ratattake har kwakwalan kansu sun zazzalo waje,, rai kuwa baqon duniya tuni yayi hijira daga jikinsu su ukun mlm lamma da zarah da uwarta hjy hadeeza, ganin wannan tashin hankalin ne na ganin yanda gawarwakin su hjy hadeeza cakud'e waje daya uwa sunyi hatsari mota ta murjesu ko fuskokinsu ba'a ganewa kuwa sun daddame, jini sai malala yake wajen, hakan ne yasa wasu daga cikin mutanen wajen suka dinga yanke jiki suna fad'uwa qasa a sume sbd tsabar furguci da tsoron ubangiji Allah dake qara ratsa zuqatan su. yayinda wasu daga cikin mutanen kuma suka dinga guduwa sbd gigicewa.. ganin babu yanda za'ayi a kwashe su daga wajen ba tareda anbar wani 6angare ba na jikinsu yasa cikin dauriya baba yawale da sauran tsiraran mutanen wajen suka hada gawarwakin namomun su hjy hadeeza suka tattara waje daya sukai alwala, nan take sukai musu salla sannan aka haqa rami mai zurfi a wajen aka zubasu tareda maida qasa aka rufe su ruf iyakar ta tasu knn. abinda yabawa mutane mamaki shine yanda qiri qiri alhj Bala yaqi shiga sallatar gawarwakin kuwa,,, haka dai kowa ya kama gabnsa suna mgn wacce ba'a rasa ba ga mutane ta cancanin miye musabbabun mutuwar tasu ma haka katsam. su khaleepa wajen hjy furdausey suka koma, khaleepa na kuka yake fada Mata mutuwar su hjy hadeeza, ai tuni hjy furdausey taqara zarewa babu arziqi khaleepa da dady sales da baba yawale suka nufi asibitin su khaleepa da'ita dan qiri qiri kuwa dady mukhtar ya hanasu baba isma'il binsu shima yaqi zuwa kuma, Dan a duniya bayada maqiyi babban gske na
Chapter 166 · 0% Book details