← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 145 OF 178

Sashe 145

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*I heart you mom Ahmed*. 👁🥡👁 🅿6⃣0⃣. *R* untse idanunta tayi katamau hannunta dafe da cikinta tahau cije baki wanda har lokacin cikin bai lafa ba, babu shiri ta fara kamo sunayen Allah kala daban daban dan neman rangwame. tadauki kusan munti 15 a hakan tana hadawa da addu'oe sannan taji kamar d'aukewan ruwan sama ciwon ya tafi lokaci daya kamar ba'ita bace take murqususu ba. wani sanyayyen numfashi ta saki bayan tayi wani tunani sai kawai ma ta yakice hijab din bayan cire takalmn nata datai takoma bakin gado ta zuba tagumi still hawayen zafin kishi basu tsagaita daga tsattsafowa ta cikin idanunta suna sauka saman fuskar taba tareda radadin zafin da zuciyar ta ke mata. muryan mama Zainab taji bakin qofan kamin ta'ida shigowa d'akin ta zauna tana kallon fuskan heenduh dahar lokacin ta gagari share hawayen nata. har aran mama Zainab taji tausayin 'yar tata wanda tasan dole kowace mace akaiwa hakan tadamu amman duniyar dole sai ana runtse mata idanu koda bakason abun kuwa to girman mutumin da matsayinsa gareka daya nemi afuwan hakan daga gareku dole ka saduda kayi mubaya'a bare wannan raya sunna ne ba wani aibu ba. bareshi mukhtar dinda keda babban matsayi garesu ai yafi gaban yanemi alfarma garesu su gagara masa. dafa heenduh tai bayan ta goge mata hawayen fuskarta cikin dauriya tace"kiyi haquri heenduh nasan kishi akwai ciwo to amman haquri zaki, inma kinyi tunani ai abokiyar zama nada dad'i ta fannoni da dama in Allah yasa kikai dace data gari, mutane basu gane bane,kinga a misali koda baki lpia miji bainan zata iya temaka miki harma da dawainiyan yaranku dasauran hidiman gida, dan haka kiyi haquri Inda bawai saman ki zata zauna ba kuma ba kanki aka farawa mace qarin abokiyan zama ba bare ki damu kanki, dan Allah kiyi haquri ki kwantar da hankali dan kishiya 'yar Uwa ce zakiga in kuka hada kanku mijinku shima ba qaramin jin dadi da alfaharin hakan zaiba" shiru heenduh tai tana sauraron maman aranta take cewa"kayya dai mama dud abubuwan nan da kika lissafo na tabbata zarah ko daya bazata iya ba bare aji dadin zama da'ita, amman dayake batason musawa Maman yasata cewa cikin muryan kuka"to..to mama bakomi" murmushi mama Zainab tai tana shafa kan heenduh tace"yawwa 'yata 'yar albarka naji dadin yanda kikemun biyayya akan komi na baki haquri a Kansa dama sauran wasu Abubuwan wanda da'ace haka 'ya'yan zamanin nan kewa iyayensu daba hakaba, da duniya tazauna lpia, amman ynzu lokaci yazo da iyaye zasu umarci d'a da abunda sukega sunfi qarfin samunsa garesa amman kai tsaye zai nuna bazai iya ba..amman Allah kyauta dai yakuma shurya mana zuri'a "Ameeen mama" "heenduh Kema kuma Allah baki masu miki biyayya sauda qafa kamar yanda kike mana a rayuwa" cewar baba Ismail daya shugo dakin yazauna shima. mama Zainab ta amsa da "amunn baban heenduh, Allah kuma sauketa lpia dai'' "Aminn" inji baban. har aran heenduh taji dadin addu'an iyayen nata amman yanda zuciyarta ke mata quna akan dud wai matan kirki na garin nan arasa ma wacce za'a bata a matsayin kishiya sai wannan muguwar ballagazan,, ??!sosai ta qudura a ranta dud ranar da kuwa khaleepa igiyoyin auran zarah ya yarda ya riqesu a hannunsa to wlh saiya gane wacece heenduh a ranar Inda shida bakinsa ya furta mata baison zarah, todanmi kuma zataji haka daga Sama nawai auransu katsam? to knn ma da saninsa da amincewarsa hakan zai faru itace zai maida shashasha ma? wani mugun haushinsa daqin son ganin koda fuskarsa ne sbd kishi daya rufe mata ido taji ya kamata. daurewa kawai tai taci gaba da sauraran nasihohin da iyayen nata ke qara mata Wanda gaba daya bama cikin nutsuwarta take ba lokacin dan tunanunta yai nisa na qudurinta dake ranta. bayan fitar baba Ismail da bama tasan ya fita ba taji mama Zainab tace"wai nikam heenduh wanne kayane can kiketa faman rufewa da bargo tunsanda nadawo daga Zaria fa na lura dasu a dakin nan?" dasauri heenduh takai dubanta ga manyan jikkunan nan dasuka amso kayan d'inkin da khaleepa na kayan daya siya matan ne wanda har yanzun ko daya tagaza fuddowa tasa sbd gudun tambayar Maman a lokacin shiyasa taketa faman rufesu. amman yanzun datasan cewa maman tasan da mgnr su ta auren da khaleepa fili yasata sauke ajiyan zuciya tareda miqewa tsaye batace komiba takamo hannun mama Zainab suka isa ga jikkan ta yaye bargon saiga d'ika d'ikan ghana mst go dinnan cikeda kayan. daqyar tasake duban mama Zainab tace"doctor ne ya kawon su sanda kina Zaria , ni ko daya banma gwada sawa a jikina ba, tayi mgnr tana hararan jikkunan kamar khaleepa ne akan nasu sbd haushinsa dake qara nanuqar mata zuciyarta saitakeji Uwa ta qona kayan ma kotai sadaqa dasu tadaina ganinsu kwata kwata. cikin fadada murmushi mama Zainab tace''ina ruwan khaleepa baigajiya ay" tana mgnr ne tana duba kayan bayan zuge zip din jikkunan datai,, sosai mama Zainab tayi mamakin dumbin kayan nan da khaleepa ya kashi kudi haka Kansu, duban heenduh tai tace"kuma heenduh bakice yarage siyan kayan ba sainikega kmr anyi barnar kudi da yawa, wannan kaya haka da yawan gaske na kanti dana dinkawa uwa dai lefen mace guda goma kokuma ince na 'yar shugaban qasa?" cikin duban Maman heenduh tace"nace masa yarage daukan kayan mama amman saiya nuna a'a. shiru mama Zainab tai tace"dudda kike matarsa komi Allah yabasa iko zai miki ammn kayan nan da yawa fa heenduh gwanin tsoro, ga tsadan gske kuma dan dud supopi ne atamfofin hakama lace da material da kayan kantin nan akwai kudi sosai, gskia kam qwamma da baki fara saka kayan nan ba zaifi kyau inkin tare gidansa kmr yanda aka tsara nanda sati2 kyasa kayan acan karki jawomana mgn aga kinasaka wannan manyan kayan kinsan mutane da zargi zasuyi zaton babanki na kwasan kudin inda yasamu aiki yana kashe mamu, dan haka barima kigani kamamun jikkunan mukai d'akuna can qarqashin gado na ajiye su...dole kuwa takamawa Maman sukakai kayan can duka sannan fa tadawo dakinta ta kwanta tana ganin kiran wayan khaleepa Amman saidai tai tsoki ta latse koren kiran ya katse..dataga bai daina kiran ba saima ta kashe wayar gaba daya tai kwanciyarta tana tunanukan takaici hardaga qarshe tasamu barci ya dauketa. a marecen ranar ne dady mukhtar sukai mgn da baban zarah akan mgnr zuwa Neman auren zarah wa yaronsa khaleepa saigashi nan danan baban ya amunce da cewa yabasa auren zarah ga khaleepa, dan har aran baban zarah yayi matuqar farinciki da hakan kamar ya zuba ruwa a qasa yasha yakeji dankoba komi rufin asirinsa ne in zarah tai aure koya samu tadaina ja masa mgn da zund'ensa ga mutane idan yafita da surutunsu nacewa gidansa yafi qarfinsa matarsa da 'yarsa _ke mulkasa. wanda da haka ne suka rabu da daddy mukhtar bayan sunyi musabuha kowa yawuce gidansa. washe gari ko kamar yanda aka Zanta da baba Ismail da dady salis da dady mukhtar din suka shirya sukaje gidansu zarah anan sitroom baban zarah da yayansa suka amshesu da karamci bayan anyi abinda yadace aka tsaida ranar daurin aure nanda sati 2 masu zuwa. dazasu tafuko har waje baban Zara yabiyosu yana fadin yafa gode yafa gode Allah saka da alheri yabar zumunci. sosai a zuqatan su dady mukhtar suka rasa godiiyar mi baban zarah yakeyi musu haka inda sunsan indai dan arziqi ne shima yanada nasa a aljuhu kuma susukaje nema aka basu...dole dai suka fudda zaton komi a ransu suka tafi. da misalun qarfe hudu na yamna zarah da mamanta Hjy Hadeeza suka fad'o falon gidan kuwa Uwa an jefosu dan sallama ma kam a janye batunta gefe dan batta cikin tsarinsu na rayuwa ga wuri in sunje bare suyi ta. anan falo suka samu Hjy furdauseey ta daura kafa daya kan daya tana kallon tibi. Aida sauri babu ko kunya zarah ta fad'a jikin Hjy furdauseey tana tsallen murna take cewa"wayyo dad'i ni zarah nanda sati 2 zanzamo mata a gidan Yaya khaleepa na kyakkyawa na, ai dole nema naware kudaden gyaran jiki dana kayan mata danya jini zamzam kota ina, ammanfa Hjy kin gyaramun zako kikiga yanda zan dunga tattalin d'anki kosau nawa ya buqaceni a rana zan basa wlh dan niko banda rowan kaina kaman yanda naji wasu matan nawa mazajensu wlh, tofa wannan shine albishir dazan miki momyna suruka ta sakamakon namijin qoqarin dakikai mun wajen sawa dady mgnr auran nan ta tabbata da shirinki na qasa ...buge mata baki Hjy Hadeeza tai tace "to marar kunyan banza uwarmi takawo mgnr raya sunna kuma anan?, bakida setin bakin iya mgn ko zarah? Ynxunfa Hjy ta zama surukanki ki daina yin abu haka sakaka na gallaqanci" tayi mgnr tana qyaftawa zaran ido a fakaice..aiko cikin fahintar mgnr da uwar tai mata da ido dayake 'yan bariki ne itada uwar harta gane nufinta, shiyasa nan danan zaran ta boye fuska Uwa gaske wai ita nan kunya takoma tazauna ta nutsu tace"sorry in law na momy tsabar d'okin murna ne wlh yasani fadan hakan ban shirya ba" tayi mgnr tareda yiwa uwarta signal da uban tayani muninta a fuska. murmushi Hjy furdayseey tai tace"tomiye na damuwa danki CE hakan? ba mijinki bane zarah 'yata?, ni fa damuwa ta shine ynx Mlm yadawo wlh kona rabasa da auran wanna n Mayyar yarinyar kokyaji dadin waqatawa ke daya a gidansa" fashewa da dariya zarah tai tace"wlh kuwa dakin kyauta" Hjy Hadeeza tace"ay dayake ma munyi waya dashi d'azun yace saura Kadan yagama aikin NASA nacan yadawo nan" Hjy furauseey na shirin mgn saiga dady mukhtar ya shigo cikin falon da sallama ga alama dawowarsa knn daga waje. dasauri zarah da Hjy Hadeeza suka gaishesa cikin girmamawan qarya, shiko ya ansa cikin fara'a sannan yawuce samansa. nan Hjy Hadeeza taiwa hjy frdauseey rad'a da cewa"sun wuce zasu dawo anjima" sannan suka fita ita kuma ta koma tazauna tana cigaba da kallon tv dan tasan wanka Alhj mukhtar zaiyi shiyasa bata bisan ba ta tsaya zamn jiran yagama ya sauko. azahari TV take kallo amman aranta wassafawa take na kalar mummunan ta'adin dazatasa mlm yaiwa heenduh muddun yadawo kuwa. wani murmushin mugunta tasaki taredata girgiza kafa a fili tace "hmnn dani kuke zance matsiyatan nan wato ma har kun mance wace Firdausyn meron tsimbe
Chapter 145 · 0% Book details