← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 178

Sashe 38

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

to zata sallama masa ita dan wanna ba wai baq'on abu bane a gareta lura da yanda suke qazamtacciyar soyayyarsu da samarinsu na school kises in every were are her body and hugs wanna ba wani baq'on abu bane a gareta ba muddin zai nema a shirye take data sallama masa knta indai zaiyi farinciki harya kulata dai dai na munti daya cikin sakin fuska ba wannan fuskar shanun da yake ba kullum, shiyasa ake tunanin jawo hankalin khaleepa ta wanna hanyar amman sam ko fuskar haka ta gagara samu a wajensa bare ta cimma burinta dan a haqiqanin gskia tana masifar son jin yanda zumarsa take danda gani zakin mazaje ne a iriyar kalar k'irarsa zai 6atawa mace tunaninta ta yai mata formating nasa gaba daya indai ta wannan fannin ne komin jarumrarta kuwa, shiyasa kawai ta shagala da kallon qirarsa dudda tsoron da takeji na kallon banza da take samu daga garesa ga kuma tsabar qwarjininsa dake kada hanjin kowace mace kuwa data yarda har ya saka mata kalar idanunsa cikin nata idanun. anasa 6angaren kuwa dubnta yake sam ya tsani mace marar kamun kai a rayuwar sa, bare ita daya sha ganinta da 'yan iskn samarinta suna yanda sukeso kuma dud halinda ta ke ciki yasan tabbas mamanta tana sane ammam sabida tsabar son da take nuna mata ya hanata katsa mata, kuma shi koda habitat nata masu kyau ne sam batta daga cikin kalar suffar halittar macen da yakeso matarsa ta kasance dasu na jiki, ko daya batada shi amman sbd tsabar ta rainasa har take iya shigo dakinsa ta dunga ya mutsa sa ma knn, amman taci sa'a ta kuma godewa Allah dabata mallaki surar dirin kalar matar da yakeda buqata bane da saita raina kanta yau yau dinnan a hannunsa tabbas, dan a yanda yasan kansa baida excuse ga dud macen data shiga hannunsa, shiyasa bai cika son shiga harkar matan ba dan kiyaye kansa daga abunda ke sake girmama a jikinsa tabbas tabbas tabbas shi yasan yanada sha'awa bata wasa ba, hakan yasa yake dauke kai ga dud wata mace gudun kada ta rusa masa budget dinsa dan ya d'aukarwa kansa alqawali zai zama virginity shima kamar yanda zai karbi na matarsa shima zata kar6i nasa a ranan zata fara sanin sa itama, hmmm kunji fa, shiyasa ya qudurta worning zai bige wa zarah kan zuwan masa d'aki dan ko muddin ta ci gaba da taba masa jiki da wannan qazamin hannun nata wlh sai jikinta ya gaya mata, dan haka nn take ya q'ara fiddo idanunsa waje gaba daya tareda daka mata wata tsawa sai kuwa gata bakin qofar futa daga dakin yace "ubanmi ya kawoki d'aki na? yayi maganar yana mai zazzaro mata idanunsa waje, jikinta na buga rawa ta fara magana murya na sarkewa "ww.. wlh yaya khaleepa momynka ne tace nazo naga in kana ciki,, "ok dan ina ciki shine akace in kinzo ki dinga shafa ni ke qaramar 'yar iska ko? yana maganar ne yana q'oqarin kwanto belt d'in jeans d'insa aida sauri ta sauka q'asa batareda ta q'ara cewa uffan ba. wani dogon tsoki yaja tareda wurgar da belt d'in tsakar d'akin ya koma ya zauna bakin gadon nasa ya sa yatsun sa cikin sumar kansa ya dunga yamutsata sosai idanunsa a lumshe sam ya tsani yawan magana yanzun kwaratsin da ta sanyasa ji yake gefen kana na buga masa d'al d'al d'al ciki ciki, shifa harda haka ne yasa sam ya tsani harkar mata shiyasa babu shiri ya miq'e zuwa ma'ajiyar magun gunan sa ya d'auko na ciwon kai babba guda daya ya tura a baki tareda daura kofin ruwa akai ya hadiye maganin ya ajiye cup din cikin deep freezer dinsa sake kwance wajen, cire kayansa yai ya daura towel a iya qugunsa nan take faffad'an qirjinsa ya bayyana mai cike da mayalwacin kwantaccen gashi sai sheq'i yake, toilet ya wuce kai tsaye bai jimaba ya fito ya shirya kansa cikin wasu qananun kayan, baqin jeans ne sai Blue din riga mai qaramin hannu rigar tabi jikinsa ta kwanta ta yanda dud wasu zubin damatsam halittar karfi ta cikakken namiji gogaggen d'an boko kuma suka bayyana a kansa, Black cambus dinsa yasa kalar na 'yan q'wallo amman su wanna new designer ne, bayan ya gama d'aure mad'auran takalman nasa ya d'auko wata farar rigarsu ta likitoci ya d'ora saman sheet din jikinsa ajiye medical glass dinsa yayi gaban aljihun rigar sannan ta fito daga dakin sa zuwa babban falon gidan nasu dake q'asa sai baza qamshin sa yake, taku yake cikin takunsa daya saba. cin karo yayo da momynsa tana qoqarin shiga kicen dan ita bama ta gansa ba, dan haka a hankali ya sad'ad'a ya lallab'a tareda kai bakinsa ta bayanta daidai saitin kunnenta yace "momyyy na!!!" da sauri ta juyo tana murmushi tace "mai tsada na ka b'oye ina ka shige yaune? tayi maganar tana kallon had'adden saurayin matashin d'an nata kwalli d'aya wanda dud sonta na rayuwa yana garesa duka, shiyasa gata na gidan duniya babu wnda khaleepa bai samu daga iyayensa cikin ma samin wasu yake, kan ya bata amsa sukajiyo muryar dadynsa mukhtar daga gefensu yana fadin "Masoyana fira kuke ne batareda an gayyace niba?" dariya sosai hjy firdauseey tayi shiko uban garin rungume dadyn nasa yai yana cewa "barka da fitowa dady, zama sukai kan kujerun falon hjy firdauseey tace "kagansa nan kyakkyawan saurayin d'an nan naka alhajina tun safe daya bar gida saifa yanzun na gansa alhalin yasan bana jure rashin ganinsa na sa'oe muddin ba yana office ba dan haka na kawo maka qararsa ya fad'a maka inda yaje dan nasan yau weekend ne babu hospital bare nace can yaje" Alhj mukhtar wani murmushi yasa ki sosai tareda dubn khaleepa dake wani langwave kai kamar maiji barci nanko tsoron klr doguwar tambayar da dadyn nasa zai fara masa ne gameda hkn gashi shi kuma ba gwanin doguwar magana ba bare ya basu amsa cikakka fatansa dai shine AllAh sa dadyn nasa ya taq'aita tambayer tasa domun yaji dadin basu qwararriyar amsa guda d'aya, shi kansa Alhj mukhtar yasan halin d'an nasa da kwaikwai wajen magana dan haka sai ya had'a masa tambayarsa waje d'aya a dunqule a sauqaqe tareda cewar " to my done boy kaji mmnka ta kawo qararka kan ka je ka dad'e a waje ina kaje amsar da take buqata knn? yaqarashe maganar cikin raha. sam bai iya qarya ba baisanma ta yanda ake yinta ba dan haka kai tsaye yace "dady momy nifa yau naje hospital bayan na tashi da safe, shine naje na yiwa wata mata ne 'yar qaramar Theatre dan ranar nai alqawalin zan mata so kuma dady bacin na dawo ne na je gidan small father (isma'il) na iske maman bata lpia shine fa na dubata tareda zuwa samo mata medicines dana futo ne kuma ina nn zaune waje nida freands nawa shinefa na shigo yanzu nai wanka zan koma hospital din na duba matar naga kota farko" gaba d'aya saida zuqatan su suka soya fuskarsu ta nuna hakan sakamakon ambatan zuwansa gidan isma'il kai tsaye da yayi dudda abinda ya faru jia kuwa dud a knsa, to amman da yake firdauseey 'yar duniyar gske ce sai tayi gaggawar q'aqaro murmushi a fuskarta danta kula dud sanda ta 6ata masa rai akan maganar gidan matsiyatan can wuni yake yi mata fushi ita kuma fushunsa quna ne mai ciwo a gareta cikin zuciyar ta. harda mukhtar ya zuciya zai balbale khaleepa nan take a wajen da fad'a da sauri firdauseey ta girgiza masa kai alamun a'a kul kada ya soma.
Chapter 38 · 0% Book details