Sashe 126
Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 1 min read
yakomawa dan uwansa. Dafe qirji Hjy firdauseey tai da hannuwa bibbiyu tace"na shiga 3 na,wlh nima nayi kalar wannan mummunan tunanin yanzun a raina,ohni in hakan tafaru ai nashiga uku na ni hjy firdauseey" Hjy Hadeeza tace"ga Shawara gobe sammako zamu d'umama muje qauyen bokanmu marakusa Mukai masa kukanmu koya kikace ne?" Hjy firdauseey tace"haka za'ayi kuwa, dole salis yaraina kansa dan kuwa wlh aiki zansa marakusa yai masa mai zafin gaske ta yanda zaiji bai ma qaunar mukhtar bare wani jinin sa, sannan shima nasa asawa mukhtar qinsa a ransa suji sun tsani junansu har abada, sannan kuma zansa wannan arziqin nasa yabi ruwa ya lallace saimuga dami zai cigaba da temakawa wadannan matsiyatan Ismail da matarsa faqat mgn taqare sai muyi zaman jiran gobe zakara kuma yabamu sa'a" wata qatuwar dariya Hjy Hadeeza ta saki tace"kai aminiyas wlh rashin imanin nan naki na matuqar burgeni fa, kuma wannan mgnr taki tayi daidai wlh, dan ina tunanin a arziqin salis fa zasiyi gogayya da mukhtar" "Shiyasa ai zanyi maganinsa dan natsani dukkaninin wani makamancin dantakara na arziqinmu akusa dani nafiso naga na kerewa kowane mahaluqi a duniyar nan insan samu na ne kuwa" a cewar Hjy firdauseey din. dariya sukayi gaba dayansu harda kashewa da tafi kamar yanda suka saba inzasuyi wani mugun qullin nasu na cutarwa kenan....