← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 122 OF 178

Sashe 122

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

lollipop samun fitsarinki anan" zatai mgn yace "please kada kice komi bani kawai." dole ta zuqunna tai firsarin tabasa, dasauri yafuto suka koma daki ya sanya kayansa tana kallonsa harya fice. gidansu yashiga nan yanufu side dinda yakeda kayan aikinsa na asibiti yafara aune aune kan fitsarin, sosai yayi nisa a zurfafa bincikensa wani tsallen murna yadaka uwa yaro, dasauri yafita yakoma gidan yasameta tsaye gaban mirrow tasaka doguwar atanfar riga tana daura kallabinta. baijira komi ba yasureta yanata zagaya dakin da'ita dansam batada nauyi sai afkin kugu da gaba. saida yagaji da tambayar datake masa snn ya ajiyeta samn katifarsu cikin wata dariyar farinciki datai mamakin ganinta a fuskarsa taji yana cewa" lollipop nakusan zama dadyn baby,,? "bangane ba hearty?" cikin tsantsar Myrna yace"lollipop gwajin danai na fitsarinki yasake tabbatar man da kokonto na yakoma gskia, lollipop kina daukeda cikina a jikinki na tsawon sati 4 da kwana 4" aibatasan sanda ta fada jikinsa ta qanqamesa tana qyalqtata dariyar murna ba,, rungume juna sukai suna hamdala,, "Nakusan samun baby girl yanzun hearty?" "insha Allah lollipop na" cikin wani zillon dadi akaro na farko data hade bakinsu waje daya tana masa kalar wani zazzafan Sumb'a harsaida suka kaiga yin da'id'aya a wajen cikin wani sabon sha'awar shauqin juna, daga nan Abu ya zarce suna sake farantawa juna rai tahanyar jiyar da junansu mugun dadin murnar farincikin dasuke ciki. dukkansu babu wanda bai dauki burinso na gidan duniya ya azawa dan matashin cikin nan ba lokaci 1. daqyar suka sararawa juna sukayo wani sabon wankan suka qara shirya wa. daqyar tasamu o yabarta kuwa yatafi asibuti dauko su baba yawale. koda yadaukosu basu jimaba sukai wanka suka shirya suma gudun qurewar lokaci, inda lokacin sha biyu ne na rana. heendu hijab tasa har gwiwa tareda niqab dinta. a mota tana kusa da baba dahara yayinda babanta ke gefenta kenan sun sata tsaka, sai baba yawale dake kusada doctor ahaka suka dauki hanyar Zaria wanda Kadan2 zasu faki idanunsu baba Ismail su had'a ido ata cikin glass din saman motar su sakarwa juna kuma sanyayyen murmushi. harsuka isa Zaria hannun heenduh nakan cikinta tana shafa babyn girl nata wacce taiwa laqani da baby Neylar a zciyarta, dan qagare take taga sun kebe da khaleepan yaji sunan dataiwa babyn tasu takeji. qarfe 2 suka isa Zaria, sosai aka karrama su dan mama Zainab kam tayi mamakin ganinsu dan bama rabon susha banban dama sun shirya da mamanta jamila yau zasu koma Kd gida suma. heenduh kuwa daman da tunda taga mamanta take lafe cikin jikinta uwa mage abinka gamai son jiki daman, mama Zainab kuwa sai kallon 'yar tata take da mamakin cikarta da canzawarta take. saida sukaci abinci bayan gaisuwar dasukai. sundan jima a garin dan saida suka yi sallar la'asar sannan dukkansu hardasu mama Zainab da maman ta suka dauko hanyan dawowa kaduna. dayake motar jeep ce qatuwa shiyasa ta amshesu babu takurar komi. gabda magrib suka iso gida, mama jamila aka fara saukewa sannan baba dahara. sai baba yawale da baba Ismail dashi khaleepan suka shiga masallaci danbin jam'en sallar da aka fara sakamakon kiran sallar da akayi. sukuma mama Zainab da heendu suka shiga gida. su baba yawale basu suka shigo gidan ba saida sukai sallar isha'e sannan suka dawo. saida mama Zainab taqara yiwa baba yawale ya jiki sannan akadanci abunci inda baba Ismail yaso kwana gidan baba yawale din da nufin koya yatemaka masa dawani abun inyana buqata amman Sam baba yawale yaqi acewarsa ladan ya'isa shima yazauna cikin iyalansa ya huta. dudda haka da baba yawale sukai bankwana dasu mama Zainab saida baba Ismail yatafi masa rakiya zuwa gida. suna fita heendu na futowa daga daki sakamakon saurin zuwa datai had'a 'yan kayan doctor dake cikin dakin nata dabasufi kala 5 ba ta boye su cikin kayanta. dai dai lokacin data zauna kusada mama Zainab shi kuma khaleepa na miqewa tsaye yadubi mama Zainab yace "natafi...! nima zan wuce mama saida safe,yayi mgnr cikin tsabar dauriyan zuciya na ganin shikenan kwanansu waje daya shida lollipop dinsa yaqare dan yanzun. kamar ya'aza dukkn hannuwansa saman kai yakeji ya fashe da kuka sanda yaji mama Zainab na cewa"to Allah yatashemu lpia khaleepa mungode qwarai da abun arxiqin dakai ta mana na hidima, Allah biya dai" kasa amsawa yai danjidayai jikinsa har wani rawa rawa yake sanda yakai dubansa ga lollipop dinsa tana share hawayen fuskarta a b'oye, dasauri yasa qafa yabar gidan dan baijin zai juri ganin halin damuwar data shiga kalar tasa, wanda yakejin damuwar sa ta nunka tata, kawai qarfin zuciya ne kalar tasu ta maza akan tasu zuciyar ta mata masu rauni da saurin karayar .. itama mama Zainab miqewa tai dantayi salla. buta ta dauka tashiga bayi. heenduh ko tana ganin fitarsa da saurin gudu gudu tamiqe tashige dakinta ganitai dakin yayi mata fadi saidai qamshinsa nanan still uwa yana cikin dakin ne lokacin. babu shiri ta zube bisa katifarsu setin da suke kwanciya ta jawo fulonsa ta rufe bakinta dashi dan hana fitowar sautin wani qaqqarfen kukanta dayayo waje,,, kuka takeyi tana qarawa babu wanda zaignta lokacin bai zubda mata hawayen tausayi ba, rabuwa da masoyi masifa ne kammadai kuna tsaka da sabantuwa mai qarfi a tsakani. haka zuciyarta ke rayawa. sosai taji masassara na shirin kamata, kanta jitake uwa zai fad'o qasa tsabar sarawa dayake mata da qarfin gaske. gefe daya ga kuma wayarta datakejin tana ringing, amman lokacin nema taji wani mugun sabon kukan yakutto mata kalar mai saka mad'aciyar nan a maqoshi.. abun kam yaci tura izuwa yanzun dan ko tuni taji jikinta yahau rawa kab! kab! kab! babu tsahirtawa ko kad'an . jan sunayen Allah kawai takeyi da salati acikin magagin zafin ciwon nata dake cikin kwanyarta da kuma sassan jikinta....
Chapter 122 · 0% Book details