← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 156 OF 178

Sashe 156

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

ba da fita kuwa baba isma'il yaji qarar shigowan saqo a wayarsa, sam bai duba ba har saida yasha ruwa sannan ya dauki wayar dake gefe hannun kujerar da yake zaune yafara dubawa. dasauri ya miqe tsaye yana mai qara kallon number heendun tasa da kuma text d'in data turo masa kamar haka. ~"Assalamu alaikum iyayena, dan Allah ina roqonku daku kwantar da hankalinku kan rashin ganina da kukai,ina mai tabbatar muku da cewa a'inda nike ban cikin matsi na takura ina cikin qoshin lpia kuma insha Allah zan dawo gareku nan bada jimawa ba bissalam na barku lpia saqo daga 'yarku heenduh"~° wani farinciki baba isma'il yajisa a ciki uwa kuwa ance masa yau ga heenduh ta dawo gida an ganta lokacin. nan take yabawa su dady mukhtar wayar jikinsa na rawa, suka karanta suma sunyi farin ciki matuqa sai godiya sukewa Allah, ana cikin haka kuwa saiga mama zainab ta dawo hannunta daukeda colors da plates ta ajiye tana shirin fita baba isma'il ya miqa mata saqon batace komi ba ta karba ta karanta itama, Allah sarki saiga hawaye na biyo mata a fuskarta, cikin mamaki suke kallon ta atunaninsu saima tafisu murna daganin wannan saqon amman shine take kuka kuma? baba isma'il ya amshi wayar yadubeta cikin tausayawa yake "haba zainab miyasa kuka kuma? keda zakiyi farin ciki na ganin alamun da mukayi ubangijnmu Allah ya karbi adduanmu mun fara samun bayanai a kanta" share hawaye fuskarta mama zainab tayi taqaqaro murmushi tace"haqiqa farin ciki ne yasa ni kuka amman damuwa ta shine shin baban heenduh ita heenduh wai da kanta tagujemu tabarmu ne tareda sakawa hankalinmu ya tashi haka kan wani tunani nata can na daban? shiru tai sannan taci gaba da cewa '' inko tunani na yazamo hakan wato yazamana gaskiya ne tokuwa dud sanda heenduh ta dawo zata fuskanci fushina wanda bata taba sanin ina dashi ba, shiru baba isma'il d'in yayi zuwa can yadubi mama zainab d'in shima ransa babu dad'i yace"gskia ne amman maman heenduh ban tunanin tarbiyar da mukaiwa heenduh zata sakata tayi kuma wannan gangancin, saidai kuma d'an yau baka gane masa ka haifesa ne baka haifi halin saba kuma nima banjin zan goyi bayan heenduh a wannan karon in har tunaninki yazamana gaskiya ne..... katsesa dady mukhtar yayi yace"nasan heenduh bama zata aikata mana hakan ba mudai fatanmu Allah bayyana mana inda take, dady salis yace "aminn zata dawo lpia insha Allah kudai kumuci gaba da addu'a Allah tsareta adud inda yazamana ta zamo yamaidota gida lpia kuma" da aminn suka amsa su dukknsu, fita mama zainab tayi jikinta ya mutu sosai da ganin wannan text message na heenduh gaskiya, dan ta fara tantama akan wai saceta akai ko kuma 6ata tayi sosai tasan halin heenduh da taurin kai a kusan dukkan lamari nata wanda saidaga baya tazo tanawa abun kuka kuma. qarfe 2 na washe garin ranar sa'a ta dura gida murna wajen iyayenta da 'yan uwa babu mgn kuwa, saida ta hutu knn awanshekare da safe wajen 11 sannan tayi wanka tatafi gidan su heenduh. Allah sarki sosai mama zainab taita hidima ga sa'a tun zuwanta kuwa, sa'a cikin tausayi taita satar kallon mama zainab ganin dud tayi rama wanda kallo daya zakai mata ka fuskanci tana cikin matsananciyar damuwa, haka ta daure tafara cin soyayyen plantain da mama zainab d'in ta ajiye mata. sallamar khaleepa ne yasata saurin kallo wajen, sosai ya d'an rame shima, sanye yake da baqar riga mai zanen *don't hurt me*, a gaban ta da farin rubutu , sai farin jeans d'in wando, babu fara'a kwata kwata a fuskarsa danhar yau baijin dad'i a jikin sa ko qarfin sa ma baiji sosai abinci kuwa rabon da yacisa full tun juma'a banda ruwan tea babu abinda yafiso kuwa. wasu hawayen tausayin wannan ahalin ne yatararwa sa'a a cikin idanunta, nan tayi dubarar gogesu. Karo na farko knn dataji tabar goyon bayan heenduh kan abinda tayi na barin gida. tanaji suna gaisawa shida mama zainab d'in a lokacin, itama sa'a d'in ta gaishesa ya amsa batareda ya kallo Inda take bama. jitai mama zainab tace "khaleepa bari a kawo abinci ko? gani tai ya girgiza kai a hankali ya bude baki yace" a'a mama azumi nake yi abarsa ngd yanzu ma nashigo na gaishe ki ne dan mun hadu baban dazun. " mama zainab tace"Allah sarki, Allah bada lada kuma" "amin mama" agogon hannunsa ya kalla snn ya miqe tsaye yace"zanje wani wuri mama saina dawo" mama zainab tabisa da adawo lpia harya fice idanunta na kansa banda tausayin kansu bata komi,, dasauri sa'a ta miqe tsaye tace wa mama zainab tana zuwa, a haka tafice dasauri daidai lokacin data hango khaleepa na qoqarin barin zauren gidan ta qwala masa kira da fadin "yaya khaleepa dan tsaya zan fada Maka wata mgn..... dakatawa yayi harta iso wajen, nan kuwa ya juyo fuskarsa ba walwala ko miskala zarratin amman hakan saima kyau dayaqara sawa fuskarsa tayi,jin ta tsaidasa kuma tayi shiru tana Inda indar mgn yasa yaqara watso mata dubansa tareda zuba mata idanunsa kaifafa wanda babu shiri sa'a ta dauke idanunta a nasa sakamakon wani qwarjini dataga idanun nasa suka qarayi mata yau fiyeda ko yaushe matuqa,, daqyar ta samu ta bude baki tafara da cewa"amm... immm.. yaya khaleepa daman zan shaida maka cewa ne heenduh fa tana can gida na a garin bauchi can ne taje ta 6uya.....!!!
Chapter 156 · 0% Book details