Sashe 101
Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
👁🥡👁 🅿4⃣6⃣. *Y* ana fita tsakar gidan yai tsaye dan da sauri yakeson samun ruwan dumi a gidan. kitchen ya nufa nan ya fara dubarar qoqarin had'a itacen dafa ruwan amman sam ya kasa yanda zai jerasu dan baisan ma ta inda zai fara ba. dasauri ya bude gidan ya fita kai tsaye gidansu ya shiga yai sa'a kuwa falon ba kowa dan haka da Saurin gaske ya haye saman sa ya wuce toilet a gaggauce yayo wanka ya fito ya shimfida pray mate yai salla yana gamawa ya dauki ruwan zafin daya zuba cikin wani boket ja mai murfi yasake fita daga gidan ya koma can bayan ya dauki abinda yasan zai buqata inyaje. yanda ya barta haka ya isketa ko motsi batayi har lokacin yanda kasan matacciya haka ta koma ko hannunta ta gagara motsawa, saida ya yayyafa mata 'yan ruwa a fuska da qirji sannan ta kawo wata nannauyar ajiyar zuciya da qarfi danba shakka sumewa tai a tsawon lokuttan nan da shka shud'e. hawaye ne kawai kebin gefen fuskarta dud sun jiqe fulon da kanta ke akai. cikin tsabar tausayin ta ya daukota ya fito waje da ita sannan yad'an zaunar da ita yaje yasaka dettol a ruwan wankan nata daya kasa gida biyu sannan ya dawo ya sake daukarta ya sanyata a babban roban yana mata wanka idonta a runtse jitake datana iko data turesa daga gareta saidai ko hannunta nauyinsa takeji bare jikinta dukansa datakeji uwa ara mata shi akai ba nata bane tsabar wahalar da ita dayai. wankan tsarkin ma tanaji tana gani yai mata shi, dan nata niyya ne kawai a zuci. yana gamawa ya daura mata alwala sannan kuma ya qudundunota cikin zanen atamfarta ya kawo ta ya ajiyeta saman katifarta yayinda ya kwashe zanen dake kan katifar yai waje dashi ya nad'e qafar wandon jeans din jikinsa da dogayen hannuwan rigarsa ya wanke sa tas ya shanya kan igiya. sanda ya dawo dakin isketa yai jikinta sai rawa yake kaf kaf kaf haqoranta na had'uwa suna datse junansu saboda zafin masassarar data rufeta. wannan karon ma hawayen ma cak suka tsaya mata. da mugun sauri yake jijjigata ganin dayai tunda taja numfashi bata qara maidosa ba alamun ta qara sumewa. babu zato yaji hawaye akan fuskarsa na saukowa najinzafin number daya matsa mata lokacin datake Neman agaji naya rage mata girman number amman did baiji ba gashi ya kwantas musu da 'ya lokacin da mahaifinta ke tsaka da buqatar kulawarta ta hidima dasu itada Wanda yake jinya. daurewa yai ya cije ya jawo jikkarsa ya bude tareda dauko wani farin roba qarami ya bude sannan ya fiddo wata farar qanqara babba guda daya ya daura mata a saman goshinta ya dinga d'an dandan na mata kusan minti 15 sannan yaji ta fara motsa yatsanta babu jimawa ta fara qoqarin bude idanunta da qyar saboda nauyi da sukai mata na tsaban kukan data sha,,, dai dai tana budesu shi kuma digon hawayensa na zubowa cikin qwayar idanun nata da sauri ta qara runtse idanun nata wani hawayen nata tareda qwallar nasa idanun ta matsosu suka yo waje, kuka take wanda babu sauti a cikinsa kokadan dan muryarta ta dushe. bai matsa daga nan ba ya sake fiddo sirinji a jikkar sa tareda wasu fararen kwalba qanana guda hud'u, ya soka siringin a ciki dud a cikin kowane ya tsotso yan qalilan ruwan dake cikin kwalaban tanaji tana gani dud yanda takeda tsoron allura amman kasa motsa jikinta tai bare ta hana, tanaji tana gani ya d'age zanen ya tsira mata allurar wanda hakan yasata kama hannunsa ta riqe qam cikin wani qarfin bazata daya ratsata lokacin shigar tsinken allurar cikin qugunta ga ikon Allah. yana zare allurar taji hannunta ya koma ya kwanta qasa tana rufe idanunta Wanda daman alluran daya had'a na dawowar kuzarin jikin mutum ciki hadda ta barci shiyasa yana gama mata allurar tafara ganin biji biji na dushe dushe a cikin idanunta, amman zuciyarta naga su baba Ismail dan haka cikin magagin barcin nata muryarta ko fita battayi sosai saidai gani yai tana motsa bakinta alamun tana sonyin magana ne amman babu wadataccen voice sound a bakin nata, shiyasa yakawo kunnensa daidai bakinta wataqil ko Allah zai jisshesa abinda takeson cewa din, cikin ikon Allah kuwa yaji tana cewa a qasa qasan magagin maganarta na barci "ba....banahhh...baaaaab.kaka ya..wale m...kujirani...nn. yanzun zan kawo...oo. muku b..breakfast kada Ku..gaji da..jiranahh..bata qarasa ba bakin ya rufe yayinda barci ya d'auketa gaba d'aya tana sakin ajiyar zuciya akai akai. dafe Kansa yai dayakejin uwa zai fashe tsabar tention din dake cikinsa yasashi mantawa da small dad da kalacinsu na asubiti da za'akai, saidai ita baiwar allahn da dud halin da take ciki baisa ta mancesu ba?! runtse idanunsa yai yanajin kamar bai kyauta mata ba inda dud shine silar shigarta wannan hali, shi Kansa yarasa yanda akai ya jima kanta haka tareda mance itadin cikakkiyar new Virgin ce bawai sanin abun taiba, to duba da yanda yajita da dunbin baiwar ni'imar da Allah ta wadata ta dashi ne hakanne yasa tsananin qarfin sha'awar dake jikinsa ta kasa sauka har tsawon awonnin nan, shi kansa baisan iya inda qarfin sha'awarsa ta tuqe ba kawaidai yasan kowane bawa da kalar tasa halittar toshi yasan wannan ce kalar tasa halittar haryakeji koda zai kwana tareda ita bazai gaji ba, ganin cewa tunani bazai masa ba yasashi miqewa bayan ya gyara mata malullubin ya fita waje kai tsaye ya shige motarsa ya wuce wani qaton restaurent ya bada kulars dinda ya fito dasu aka zuba musa ferfesun 'yan ciki, d'ayar kular kuma hadaddiyar pried rice ce mai jar miya da tsokokin nama a ciki sannan aka hada masa kakkauran tea a plastic din gamida sinkin bread 3 masu kyau, nan ya biya balance sannan yasaka kayan a mota ya wuce asibitin tasu lokacin qarfe 9 saura minti 15 na safe kuwa. yana samu yana isa dakin su baba Ismail din nan ya iske baba Ismail na zaune saman kujerar dake gefen gadon baba yawale din dake barci yana karanta Al-Qur'an. yana jin sallamar khaleepa din a gefensa ya dago kansa tareda amsawa bayan ya rufe Qur'an nin. har qasa khaleepa ya rusunna ya gaisar da baba Ismail baisan miyasa kuma ya kasa jurar had'a idanuwa dashi ba yanda ya kamata. daqyar ya samu yace "am...am dama breakfast na kawo muku small dad" tambayar da baba Ismail keta son yi masa tun shigowarsa bai samu yai masa ba sai yanzun ya qara duban khaleepa din yace"Masha Allah angd sosai,amman to ita heenduh din miya hanata zuwa ta kawo da kanta saita wahalar dakai alhalin kuma akwai kudin abun hawa hannunta inma baka samu damar kawotan ba?" cikin magana Kansa na kallon gefen gadon da baba yawale ke akai yace "ta tashi bata lpia ne small dad shine yanzun dana shiga gidan na isketa kwance mafarin knn dana siyo muku kayan Karin kumallo dinnan small dad" sosai hankalin baba Ismail ya tashi har baisan yace "miya sameta? inda baba yawale na barci ko naje ne naga jikin nata? da sauri khaleepa yace"a'a small dad basai ka bar baba yawale din ba kai zamanka dan tana samun dukkanin wata wadatacciyar kulawa ta, dan yanzun ma saida na mata allura kan nazo nan din insha Allah Nike tunanin zuwa yanzun zata samu sauq'i ma" sai lokacin hankalin baba Ismail yad'an kwanta dan har a zuciyarsa yake mugun son tilo d'in 'yar tasa gaba daya. tausayinta ya mamaye zuciyarsa gashi kuma mamanta bata gida kuma yasan heenduh da lambon ciwo koyaya yake to bare kuma wannan dabaisan kalar iya adadin yawan saba ma. dan haka ya dubi khaleepa yace"to sannu da qoqari mum gode Allah saka da alheri ya bada iyali na gari d'ana" cikin ran khaleepa yace"ai small dad iyali na gari sun jima da bayyana kuma har mun qara zama ma daya da gudan jinin ka" amman a fili kuma sai yace "aminn small dad zan koma naga kota farka" baba Ismail yace "ba asibitin kazo ba knn? da dan sauri khaleepa yace"eh zan dawo yanzun amman" yayi maganar yana mai miqewa tsaye dan qagare yake dayaje yaga kota farka kada kuma tanemi temakon wani abun ta kasa inda bainan. "Kaimata ya jiki to Allah bata sauqi" "Aminn small dad" haka ya fita daga dakin nan sukai cinkaro da doctor mus'ab kuma yana qoqarin Shiga dakin jikinsa sanye da kayan likitoci complete. yana ganin khaleepa kuwa ya fad'ad'a murmushin fuskarsa yace "gaisheka nike likitan mata Allah sadai ka tafomun da tawa matar dan tun dazun Nike round na zaryar Shiga dakin dason ganinta nike iske batta nan, wlh abokina un gaya maka fa jiya wlh mafarkin hot beutufil baby dinnan one by one babu kalar da banyi ba, gaskiya na qara tarbatazwa ta zarce cikin jinin jikina tuni yarinyar nan". dubansa khaleepa yake kamar wani mad man yake ganin doctor mus'ab din danshi a taqamaimai baisan ma wacce yarinya CE yake magana akai ba, kuma koda ma yasanta shi in shine bazaita 6arar dason mace a kalar wannan zunzurutun kalaman ba dan a ganinsa qauyanci ne just zaifi in kanason mutum ka gwada masa a aikace data hanyoyi da dama bawai sai kaita zuba haka ba, shi kamarshi haka dud da dumbin sonda yakewa headache Sam bai iya nata wannan zubar gareta ba komi a davarance yake shigar mata dashi kuma take karba batareda ta ankara ba. jindayai doctor mus'ab din ya tab'osa yasashi dubansa jin dayai yace"pleass abokina ba wasa ba kazomun da ita? dan jia sister Marya tacemun kunzo tare bayan tafiya na" sosai kallon da khaleepa ke masa ya juya zuwa harara Mai zafi tartare kuma da mugun takaici dansai yanzun nema shi ya gane da headache mus'ab ke wannan maganukan nasa. ture hannun doctor mus'ab din tai daga kafadarsa sannan yasake jefa masa wani kallo a fili yace "kada ka soma gigin cigaba da raya matar aure a ranka doctor mus'ab kagane ko?" yana fada masa hakan baima saurari amsarsa ba yayi gaba yayinda doctor musab yasaki baki yana kallonsa, dasauri kuma ya sha gaban doctor khaleepa din daidai zai bude motarsa. "wai abokina mikake nufi da mgnr nan taka ne em? kana niyyar cemun ne yarinyar nan matar aure ce alhalin banga alamun hakan