← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 178

Sashe 65

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

na lips din junansu har yana mamakin kaddai itama dai headache 'yar luv ce duba da yanda take masa a bakinsa cikin nutsuwa mai gigita tunanun wanda akewa. jin jikinsa yafara canjawa hakan yasashi shirin zame bakinsa a nata amman tace inaaaaa wannan kam bazai kasantu ba, wuyansa ta saqalo hannuwanta akai ta ida janyosa cikin qirjinta taci gaba da kamo bakinsa tana tura masa nata a ciki idanunta arufen su still. baqaramin juriyar barin jikinta yai ba tareda saurin sa hannuwansa ya kamo damatsen hannuwanta ya jijjigata da qarfi tareda fadin ke?! ke?! ke headache bazaki tashi bawai koko? zumbur ta miqe zaune tareda waro idanunta waje tana dubansa da mamakin yaushe tai barci kuma yaushe ne ya dawo motar, jitai jikinta ya sauya duba da kalar halin data tsinci qasan ta a ciki. dubnsa tai sosai ganin jan bakinta babu inda bai kama ba a cikin fuskarsa hakane kuma ya tabbatar mata da abunda ya faru ba a mafarki bane kamar yanda ta zata, ganin yanda yawani sha murr ita sai abinma ya bata daria ya iya lallabawa da wayau da dubara yai romance da ita amman sai ya samu yanda yakeso kuma zai yana basarwa. itako yau bazata taba cewa ya goge ba fatama take Allah sa wani yaga fuskar tasa koyaji kunya. gani tai ya d'aura mata takeaway dinta a saman cinyoyinta shima ya dauki yughurt dinsa yana sha ko magana bai sake mata ba. sosai takejin yunwa dan haka bata wani yi jinkiri ba ta fara cin shawarma din daidai nan yaiwa motar key suka bar wajen bayan yasaka wani music a motar. saida taji ta qoshi sosai sannan ta barsa. kwanar anguwarsu taga ya shiga, satar hararasa tai a ranta tace "d'an kaga dama da miyasa ka dawon. satar kallon agogon hannunsa tai da hannunsa me mirza styarin motar tasa wanda gashi ne kwance lub lub akai nan taga 9 da 22. dai dai qofar gidansu yai horn baba sani yai saurin bude musu gate yaje parking motors ya kashe motar tareda juyowa ya dubeta itama dubnsa take da tunanin miye haka kuma gidan nasu ma bazai bari ta koma ba ne koko? kibiyoni ki dauki tsumman rubands dinki Wanda kika yarda mun a daki rannan, dan inna shiga gida bawai sake fitowa zanyi ba, kuma dan haka ke baki isa sani qara fitowa ba" tun kafin ma ta basa amsa yunus ne ya shigo gidan har bakin motar ya iso daidai lokacin sunfito cikin motar hannu yabasa suka tafa yunus yace "kai ya inata magana yanzun baka jiba? khaleepa yace"Sry friend banji bane nadawo ne dud nagaji, murmushi yunus yai ya dubi heenduh dake tuquburi da gunguni ciki ciki yace "headache barka da aiki fa sannu?yayi mgnr yana dariya,,ta lura da abinda yunus yakewa dariya wato jambakin fuskar khaleepan da lebunansa itama dariyar taji tai saurin barin wajen tai gaba ta tabarsu nan batareda tace komi ba tai shiga gidan tai sa'a kuwa babu kowa falon dan tai saurin hayewa samnsa danta dauko bands din kamar yanda yace taje ta dauko kayantan. a can waje ko dariya sosai yunus ya tusa doctor din gaba yanai masa hardai ya qulu yace "wannan dariyar haukan fa yunus anya kuwa brain dinka na lau? daqyar yunus ya tsaigata dariyar tasa yace"Amman kai mugun dan iska ne wlh wato mune kake rainawa wayau da cewa ba soyayya CE tsakaninku da headache bako? Ai ga alamun rashin so din nan mun gani a fuskarka duba madubi kaga", gaban khaleepa yaji ya bada dammm!!! damm!! sanda yaga fuskarsa dud shaitin bbki ne akai, ya rasa abunda zaicewa yunus saida qyar yace''dalla mlm dakata wannan bakin baby girl din wani abokina ce da muka hade dasu ynxun dudufa babyn bama ta wuce 7 years ba kake mun mummunan zato dan iska kawai" dariya yunus yaqarayi bayan ya zari key din wata mota daga cikin keys din motocin gdn dake jikin key din motar da khaleepan suka dawo yanzun. dubn khakeepa din yai yace''oh koba baby girl ba nixaka rainawa hnkali knn, hm ga baby can ai headache malam" yayi mgnr yanai masa dariya sannan ya dauki motar ya fuce. dasauri khaleepa ya dauko hankicerp dinsa ya goggoge fuskar yana zagin yunus a ransa a cewarsa bai fada masa tun wuri ba kn heenduh ta lura baisan itace ma first ba wajen ganin inda itace tasa. maida hankicerp din yai aljihu sannan ya shiga falon tareda hayewa saman sa aiko suka gabza karo da heenduh da tazo fitowa, sosai taji zafin karon takuwa wage baki knn zata fasa qara aiko yai saurin ida baya da ita zuwa cikin dakin tareda rufe mata baki ya fizgota zuwa cikin wasu Cotton's din dogayen labulayen dake jikin bangon dakin nasa suka lafe a ciki saka makom muryar momyn tasa da sukaji itada Hjy Hadeeza sun shigo dakin. cikin dabara ya saka wayarsa silent daidai lokacin ne Hjy firdausey tace "aaha kingamin ikon Allah badai bai shigo dakinba?, Hjy hadeeza tace''ah bayanzun yashigo da motar saba lokacin muna garden ba? "to babu shakka fita yasakeyi ko a qafa inda dai bainan" cewar Hjy Firdausi din bayan ta bude qofar toilet taga bai ciki. zama sukai bisa gefen Mirrow Hjy Hadeeza tace"wlh inci gaba da gaya miki aminiyas bakiga yanda yaron nan ke dafifun shiga gidan matsiyatan mutanen can ba danko dazun tare na gansu da ita yarinyar nan heenduh, hmm wlh kuwa aminiyas kisan matakin da zaki sake dauka kan lamarin nan danda alama yanda yake manne mata da ace yasan cewa yarnyar nan matarsa ce ita Allah kuwa ina mai tabbatar miki dasai dai kiyi haquri dan gaba daya janye masa hankali zatayi da wannan shegem Iyayen nata na kankanba itaga mai miji" Hjy Firdausi tace''aiko billahel azeem uban kuturu ma yai kadan dan su Kansu iyayenta da suka San da auren nasu basu gigin fara fallasa shi duba ga yanda aka tsoratasu ga lamarun dazai faru dasu da kuma 'yar tasu gaba daya bare wannan shauran mutuwar yawale in aka masa qagen b'ata yaran mutane ai baqinciki ne zai ida qarasa shi koya kikace? snn itakuma yar banzar yarinyar hmmn barshi dai nafads miki plane din" dariyar mugunta Hjy Hadeeza ta saki sannan tace "wlh Shiyasa nikesonki aminiyas bani mu khashe nan suka tafa sannan Hjy Firdausi tace"muje can dakin nawa sbd my ida tsara yanda zakije wa maraqusa da saqon nawa inda kinga gobe ne tafiyar kada a tsara komi a lokaci qurarre asamu matsala dan nafison alhajina na dawowa asaka ranar auren zarah da maitsada na kinga shiknn mun ida zama daya daku zumunci babu kan gobe" ahaka suka bar dakin baccin sun rufe qofar. Zufa sharkafffff sukayi baccin sun fito daga inda suka lafe jin abun suke kamar almara wai suna nufin sud'in ma'aurata ne koko ya'abun yake? tabbas haka sike nufi inda har gashi suna mgnr da ace sunsan sunada auren junan su....cabb dijam danqari cewar heenduh bayan ta dubi sa tace"taya ne muka aurun ne?? wai suna nufin kai d'in miji na ne knn yanzun? kwata kwata kasa mgn yai banda hautsinawa da brain dinsa keyi dn tsabar mamaki bayajin komi,, tsam yamiqe tareda kamo hannunta da qarfi, cikin mamaki take binsa da kallon yanda yake jan hannunta. har suka bar dakin suka kuma bar gidan gaba daya babu inda ya tsaya face gaban baba yawale dake kan buzunsa yana jan cazbi. durqushewa gabansa khaleepa yai bayan ya ruqo hannunsa cikin rawar murya mai shaking yace"baba yawale da gaske heendatu *matata ce*??????????,, wani farinciki ne ya rufe baba yawale har yana cewa a ransa dad'ina da gobe saurin zuwa. kabbara yayi a fili cikin fara'a wacce rabonsa da ita tun da ran su baffa. take yayi salati 100 a cikon zagayen carbin nasa sannan ya daga hannuwan sa biyu Sama a fili ya dinga addu'oen godia ga ubangiji tareda fad'in "Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulilla ya ubangiji Allah nagode maka da baka dauki raina ba kamar yanda Nike roqonka harsai na bayyana gskiar lamarun nan ga yara, Alhandulillah Allah koyau ka d'auki raina farinciki zanyi,,,, Alhamdulilka Allah mungode maka yau gashi jariran nan da aka auras sune suka girma har suka zo da batun mgnr da'aka binne shekara da shekaru ubabhiji Allah shi qarawa annabunka darajha da buwaya ubabgiji,, subhan@ kallahumma wabi hamdik nashhadu anla ilaha illah wa'natubu alaik" baba yawale na kaiwa nan suka shafa gaba dayansu. sannan baba yawale ya dubesu daya bayan daya sannan yace "tabbas ku d'in nan mata da miji ne kuma an d'aura muku aure ne a sa'ilin da kuna jinjirai" mamaki muraran a fuskarsu har suna saurin cewa "auren jarirai baba yawale? "kamar yaya? Inji heenduh da knta yakusan fashewa tsabar mmki takejin abun kamar mafarki nema. baba yawale yace "qwarai ko baruma kuji ynda abun yk. batareda b'ata lokaci ba baba yawale ya fed'e musu biri har wutsiya na labarin ynda akai aurensu. harkawo yau kuma. yaci gaba da cewa dan haka kuna mazaunin maaurata saiku guji mummunan furuci wa juna kuma inda kunsan matsayin junanku kuma kunada ikon yin komi na mata da miji dan ba haram bane nan baba yawale yaiwa hnduh nasihar bin miji da haqqinsa wajen matarsa, nanma kma yaiwa khaleepa nasiha akan sauke dud wani haqqi daya rataya knsa na matarsa. sunyi shiru sungaza cewa komi khaleepa ne yai qarfin halun cewa "amman baba yawale zamu iya shaidawa iyayenmu cewar munji batun?! "kull! kull! kull!! karma ka soma,, kabari harsai ka girbe gonarka tayi yabanya yanda babu Wanda zai komarda ita kamar da lokacin da aka fara girbin, to ina mai tavvatar maka cewa dasunga hakan a jkin gonar taka zasu nemi jin ba'asin taya kasan gonar nan takace bare ka cimmata har tai yabanya?? Fatan ka gane bayani na likita? cewar baba yawale yana murmushi. Wani murmushi khaleepa yai wnda bai taba yinsaba sannan yace ''na gane d'an tsoho. dariya baba yawale yai yace masha Allah, kuje to Allah shi muku albarka" heenduh kan binsu kawai take da kallo dan bata fahimci cakwakiyar maganar da baba yawale sukeyi da khaleepa ba. dan haka Suna shirun fita baba yawale ya tsokanota da cewa "Matas anyi Sabon miji an yarda tsohon ko? turo baki tai ta ko kwasa da gudu tai gida. dariya baba yawale sukai mata shida
Chapter 65 · 0% Book details