← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 178

Sashe 105

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

dakin saikuma ya juyo wannan karon har hada idanunsu sukai sannan yace "ammm kada kindamu da kai abincin su baffa dan nakai musu tun dazun kuma nizanci gaba dakai musu har kokacin da kika samu isasshen sauqi dan nasheda wa baba baki lpia kuma yana gaisheki da jiki sosai,so kada kidamu ta wannan fannin danna dauki dawainiyar hakan" yana gama fadan hakan yajuya ya fice daga gidan gaba d'ayansa ma. rufe idanunta tai saikuma taji hawaye sun zubo mata nanta fara ganun laifinta akan miysa ma zata daddatsa masa maganganu ne haka ma ? Mijinta nefa yanada damar yin komi da ita koda bada amincewarta ba, hasalima koda bata yarda ba ta amince masa ba muddin yazo mata da buqatarsa tabbas tasan zata kwana ne cikin fushin Allah da mala'iku, to gashi shi yama nemi izininta amman kan kuskusren sa dabata d'auka ba ysata masa rashin kunys gashi haryayi fushi ma yatafi, dudda d'awainiyar daya furta zaiwa mahaifinta da baba yawale amman sakayyar da zatai masa kenan na godia? sanin kantane kuma da'ce yabiyo halin mahaifansa ko kallo ma bazasu ishesa ba arayuwa amman shine taimasa hakan kuma tasa qafa ta doke dukkan alheransa garesu?! wata zuciyar taji tsce''yo miye aiba roqonsa kukaiba shiyaga dama kuma yaji zai iya din haryai mukun. jin bata yabawa tunanin wannan zuciyar datai mata mgn yanzun ba hkn yasa ta kwantar da fuskarta qasan sallayar dan kokad'an taji zuciyarta batai mata dad'i saima zafi datakeji. hannunta tasa saman shafaffen cikinta tana shafarsa jin yanda yaketa mata kukan yinwa gashi am bazata iya zuwa girka wani abunba bare tagirka taci. haka taqara lafewa jikin dardumar Uwa mai barci nanko yunwa CE kawai ta qara nauyayar mata da jikin Nata. lumshe idanuwa tai kawai tana fitarda numfsshi. khaleepa na isa gida ya iske har momyn tasa ta had'a musu abinci a colors, d'aya Kular soyayyen doyace da dankali da sukaji qwai saikma yenbolls da egg into egg da shimfidaddiyar wainar qwai guda Biyar akai manya manya. sai d'ayar kular farfesun kaza ne da dankali gamida tsokokin mama zubu zubu a ciki. sai jug na tea shima dakayan shansa a had'e. sosai yaji dadin hakan danhar rungume momyn tasa yai sannan ya kwashi kayan ya fito harabar gidan. nanko yaci karo da zarah tana qoqarin shigowa gidan cikin jar motarta.. dasauri takashe motar ta fito tari gabansa da sauri tace "hmn laaa yayana inazaka ne haka da kaya?" wata muguwar harara ya jefa mata fuska a d'aure yace "Inda kika aikeni naje to can zanje" "aaaaa to Allan baka haquri yayana daga tambaya dai?" tsoki yaja yafice daga gidan ganin zata 6ata masa lokaci da useless talks nata maras ma'ana, nan tabisa da kallon so Uwa ta bisa ta rungume takeji dan wani annurin kyau taga yake sake futarwa ma yau. ajiyar zuciya ta sauke tareda cewa "kakusan zamowa nawan ni d'aya dan haka dud wani dizginka zan cigaba da juresa harka zamo mallakin zarah yaya khaleepa" tayi mgnr cikin murmushi tareda shigewa cikin gidan tana karkada key din motarta da yatsunta. kai tsaye gidan khaleepa ya sake nufa sanin dayai dole ta buqaci abunci kada tai zaman yinwa yasashi shiga dakin da basket din a hannunsa. har kusada ita yaje ganin kamar tana barci hakan yasa yarasa ma wai ta ina zaima fara tashinta taci abincin ne gudun kada yunwa ta wahalar da ita, dudda shima baici kominba amman Sam bai damu da kansa ba shidai kawai burinsa taci ta qoshi kodako shi baici d'inba. magungunan saka kuzarin jiki da qarfinsa Wanda ya tafo mata dasu ya ajiye yana dan karkad'asu setin kunnenta danta farka amman saima motsawa dayaga tayi tasake gyara kwanciyar barcinta bayan ta fuskan cesa yaga busassun hawaye kwance ma a saman fuskarta. tsaf yake cigaba da kallon fuskarta ganin tana murmura idanuwa kamar zata farka yasashi saurin matsawa daga gabanta ya miqe tsaye, daidai nan kuwa ta wara dukkanin idanunta a Kansa, fauzewa yai tareda d'auke Kansa yayi mata nuni da culars din gabanta da hannunsa yace "ga abinci nan ki zuba Wanda kikeso sauran zankai wasu baffa ne shi asibiti ynzun". wani tausayin sane taji ya ratsata batadai CE komi ba ta sauke idanunta saman basket din datini qamshin girkin ya isheta tareda taso mata da tsohuwar yunwar ta. dahar zatace kai bazakaci abincin bane sai kuma tai tunanin yanda yad'au zafin ran nan batasan kalar amsar dazata samu ba daga garesa. shiyasa kawai ta dauki platse daya daga cikin Wanda ke cikin basket din ta bude kular ta zuba doyan da sauran kayan cikinta sannan ta rufe ta tura masa basket din Kad'an da hannunta gbnsa. batareda ta bude dayar kular ba. "Ya isheki wannan kenan?" yaimata tambayar daga tsayen dayake fuskarsa babu walwala. "Eh " tabasa amsa fuskarta na kallon qasa. "OK ga magunguna nan kisha zakiji dadin jikinki gayanda ake shansu nan a jikinsu" dauka basket din yai ya fice daga gidan batareda yaqara cewa komiba. hakataci abincin sosai sannan tadawo nutsuwarta. sannan tasha magungunan babu jimawa barci yasake surarta. sai azuhur ta tashi takumaji qarfin jikinta babu laifi dan zafun qasanta shi kansa taji ya rage. inda bar wanka tai tasaka wasu kaya marassa nauyi tadawo ta zauna tareda daukar wayarta hakanan ta tsinci kanta da tunanin inama tanada pic din doctor? Lumshe idanunta tai taisaurin budewa sanda taji shigowar messege lokacin. d'an tsoki tai sanda taga musaddiq ne yaimata text na fatan tana lpia na safiyar juma'a. batai masa wani reply ba saima number mama Zainab data kira tajita a rufe dole tahaqura. haka takasance ita d'ai a gidan har akai sallar magrub akai isha'e amman shiru bataga doctor ba. tsoro taji yasoma shigarta na tunanin Yaya zata fara kwana itad'ai a gidan ne? Koko dai gidan baba dahara zata lallaba taje ta kwana dasafe saita dawo? tunowa da yanda sukai da mama Zainab ne Kn kada taje ko'ina yasata haqura dole tareda fidda rai da fitan, dayake tarigaya da tasawa kanta tsoron yasata jin kamar motsi a d'akin dudda akwai NEPA lokacin amman a d'ard'arce take. babu zato kuma taji hawaye na sauko mata na tsoron dake shigarta a hankali dudda tayi addua'n kuwa amman ko gidan tagagara tajema ta rufo. ganin har 11 saura yasata yunqurawa ta canza kayan barci Riga da wando cotton sannan ta q'ulle gashin kanta waje d'aya ta fito waje da nufin kullo gidan kawai tagansa yana turo katifar kwanciya kamar daidai girman tata. sakin baki tai tana kallonsa da tunanin maizaiyi da itato? Baice mata komi ba shima yashiga da katifar dakinta ya kwantar da ita gefen tata kad'a, sannan yakoma wajen ya dauko ledoji guda biyu sai ghana moast go ya shiga dakin dasu baccin yarufe gidan. amamakance tashiga dakin itama nan ta iske ya bude jikkar Ghana din ya fiddo filo farare guda 2 sai bedsheets biyu da blanket biyu. Nanya wara nasa ya ajiye saman katifarsa itama ya zagayo ya daura mata nata Wanda yasiyo musu tare a katifar tasa. yana gama shimfida nasa sannan taga ya nufi tsakar gida tabisa da kallo daga tsayen datake cikeda mamakin raba musu makwanci dayai kenan daman dai da gaske yake mgnr knn? tatambayi zuciyarta. aranta tace "komadai mikenan inda nasamu kadawo gidan alhamdulilla koba komi tsorona zai gudu inda nasan da mutum taredani, ta qarashe mgnr zucin tareda isa bakin tagar dakin tana leqensa ta labule ganin datai ya nufi kitchen yana dube dube. komi yake nema oho?" tatambayi kanta kuna tabawa kanta amsa. ganin ya fito daga kitchen din hannunsa riqeda plates yasata dasauri tabaro bakin qofar taisaurin hayewa katifarta tajuyawa katifarsa baya tajawo lallausan blanket din tarufe jikinta tai lamo kamar mai bacci...
Chapter 105 · 0% Book details