← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 178

Sashe 5

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

yasan yanda suke da salis abikinsa ne na qut qut kuma yasan salis din na aron yan kudade a wajen yayan nasa in yana dasu shima kuma haka salis din yana arawa abokin nasa mukhtar kudin dud in buqatar hakan ta taso kuwa, to yanzun dai a haqiqanin gskia babu wasu kud'i da yake bin salis saima shi salis din da yake binsa dubu day'a daya karba jia yayo cefanen sati day'a yakai gida, dan yasan kafin nan da sati day'a za'a basu kudin aikinsu dubu uku da dari biyar da ake basu dud qarshen wata, kuma tabbas da ismail yasan aron kudin zaiyi wajen salis din dasai ya hanasa danba da san ransa yake amsar bashin ba, shima kuma dole tasa yake karbar bashin sbd ciyar da iyayen nasa tunda yanzun baffa bayya wata sana'a qarfi ya fara tafiya. koda yaje wajen aikin nasu nan ya iske salis da sauran abokan aikin nasu suka gaisa nan ya fara cigaba da aikinsa wnda yatashi akai jia na gyaran wata mota ta shinkafa,, har sai wajen la'asar sannan yasamu ya ida gyara motar ya koma qasan wata bishiya ya kwanta yana maida numfashi danba qaramin gajiya yai ba, salis ya ajiye sukuddireba din hannunsa bayan ya zauna gefen mukhatar din yace "yadai abokina yau naga kayi weak fa da yawa tun zuwanka naga kamar kana cikin damuwa, mike faruwa ne? tashi zaune mukhtar yayi yace "so nike in siyawa ismail wasu handout salis guda 2 dubu biyar suke kuma wlh gashi ko sisi bnda... nn mukhtar ya fad'a ma salis din yanda ismail yai masa bayanin exam din akan books din kmr ynda yai masa, shiru salis yayi yace"kashh kuma wlh abokina ni kaina yau bayaga naira dari hudu da hamsin dinnan bana maganin ko sisi a aljihun nan nawa" ya qarashe maganar yana mai zarowa mukhtar din kudin yana mai nuna masa , sannan yaci gaba da cewa suma yanzun nike jira mai abincin nan ta kawo na sai mana muci, in kuma kanada buqatarsu gasu saika cika saimu haqura da abincin inmun koma gida maci inda yiwa kaine za'ayi ko? cikin fara'a mukhtar yace "haqiqa salis kacika amini na qwarai ngd da kulawar da kk mana, amman ka riqe kudin nan ai mutum bazai rayu babu abunci ba, kuma bnda kud'i a jikina duka nera dari da hamsin ne bare nace na amsa na cika na siya masa books din, dana yanke shawara naje wajen oga Daniel ya temaka yabani aron kud'in in yaso in anyi albashi wannan watan da wata mai zuwa saiya fidda kudinsa saiya bani kingin cikin kaima na baka dubunka kingin sainai cefane nakai gida kaga shiknn ay,, kallonsa kawai salis yake cikeda mamakin yanda ashe har yanzun akwai 'yan uwa masu qaunar junansu haka? kalli dai yanzun shi ko tunanin kansa baiyi na buqatar rayuwa na iyayensa da kuma d'an uwansa kawai yake danya faranta musu, shiyasa bai qyashin bashi rancen kud'i dan yasan a hanyar daya dace yake biyar dasu kuma dud mai tallafawa zumuncin Allah bazai ta6a neman alfarma a duniyar nan ya rasa ba koda bai samu wani wajen ba to sai Allah ya buda masa ya samu tawani 6angaren, dubnsa salis yayi sosai yace "gskia abokina bn tunanin oga daniel zai maka wannan alfarma d'in nan kuwa yanda yake da shegen masifar son kud'in tsiyan nan, kasan fa yare da mugun son kud'i abokina wlh?" shiru mukhtar yayi yana nazari zuwa can ya miqe tsaye yana kakka6e rigarsa yace "bari naje dai,, 'yar dariya salees yayi yace "Allah a dace abokina daman sai an gwada ay ake sanin na qwarai, jeka ina nan har ka dawo kuma inai maka fatan sa'a" daga haka bai sake cewa komi ba ya dauki haki qasa yana zane dashi a qasa rairayin wajen, da "amimm mukhtar ya amsa ya wuce,, saman wata mota marar body ya iske oga din yana qilga wasu kud'ade. ya matsa kusa dashi yace "oga barka da hutawa,, ai danial na ganin mukhtar yayi wuf ya cusa kud'in qasan dam6areriyar cinyarsa guda day'a yace cikin hausarsa mai gargada" yaye ankaye mukhter kabalo aicinka kajo nan wulina kuma yanju?" mukhtar yace yana d'an shafa sumar kansa ta fulani "am oga dama cewa nayi ka ara mani 5000 thousand a cikin kud'in albashina na wata 2 in yaso in wata 2n ya cika saika fudda kudinka ka bani sauran canjin please oga a temaka ina cikin buqata ne" fiddo idanuwa waje daniel yayi yace da qarfi " wooooo 5000 k? kana nema wulina yanjun? "eh oga help me please help me "!! shiru oga Daniel yayi zuwa can yace "ok na yalda jan baka kutin ammannnn da sharad'i,, cikin tsananin farinciki na muhktar jin oga ya amince babu gargada yace "to oga sharadimmi?" oga daniel ya d'aga cinyar nn tasa ya fuddo kud'in ya qirgo 5k din ya riqesu a hannunsa ya maida sauran aljihu sannan ya dubi mukhtar yace "inka yalda kingin canjin albashinka na wata 2n wato dubu biyuh jan liqesu a macayin baci da luwa? zaro idanuwa mukhtar yayi tabbas inyayi haka yasan zai cutu, dami zai biya salis dubunsa day'a? dakuma mi zai riqe a hannunsa na amfanin gidansu? batareda 6ata lokaci ba yace "a'a abarsa ma kawai na haqura" oga daniel yace ''ok no problem go, go,mukhtaro" haka ya koma ya fadawa salis komi, salis yace " hmm nasan ai za'a rina dadai ba oga daniel bane, amman ka shawara man abokina mizai hana muje kasa wayarka kasuwa ka siyar in yaso saika siya masa handout din kaga nan gaba in kasamu wasu kud'in kasayi wata koya kace? shiru mukhtar yayi dan babu wanda ya fad'o masa arai face masoyiyarsa fiddausi yanzun idan ya saida wayar shiknn bazasu sake firan dare ba na free cull wanda suka sabawa juna dashi kullu? wata zuciyar tace qanen fa to yaya knn? tuni kwanyarsa ta cakude yarasa matsaya ta shawara, ana haka kuwa saiga kiran fiddausi a wayar tasa ta shigo, kam ya d'aga harta katse, ganewa yayi plashing knn tai masa, jiki a sanyaye ya runtse idanunsa dudda kwad'ayin son jin muryar tata da yakeyi amman hakanan ya runtse idanunsa ya zare batir din wayar ya fiddo sim dinsa yasa aljihu ya maida murfin nokia din wayar tasa ya rufe yana binta da kallo a haka ya miq'e tsaye ya dubi salis yace "muje ka rakani to kasuwar saina siyar na siyo masa handout d'in daga nan, kan salis yace wani oga daniel ya qwallawa salis d'in kira akan cewa yazo ya gwada inda ya ajiye tayar Pejo din motar da aka kawo gyara d'azun, haka ya wuce yabar mukhtar a nan gun tsaye zuciyarsa na masa saqe saqe akan shin ya saida wayar nan dai koko. dai???...
Chapter 5 · 0% Book details