← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 178

Sashe 107

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

👁🥡👁 🅿4⃣8⃣. zama yayi gefen katifarsa tareda janyo ledar daya shigo da ita ya bud'e. naman kaza ne ciki yankakke dai dai ci a baki batareda ka gutsura ba ya zuba a kowane plate biyu daya dauko wato daya nasa daya nata. Sanin dayai tana matuqar son ice cream shiyasa ya siyo mata roba guda, gudun dayai kada ya siyo mata da yawa kuma babu fridge a gidan kenan bazai shawu ta dadiba inya sire. miq'ewa yai riqeda plate da kuma robar ice cream din ya isa gabanta ya ajiye mata tareda d'an girgiza blanket din jikinta. a hankali kuwa ta dinga acting din mushau mushau da idanuwa alamun zata tashi kamar mai barcin gsken dama can.. shiknsa yasan bata isa fara barci ba adai shigowarsa gidan yanzun, yadai share ne kawai dan baison sake jan doguwar magana tsakaninsu gudun kada hakan ya jaza karyewar alwashinsa wanda ya dauka gameda ita. "kitashi kici abinci gashi nan" abinda taji yace kenan ya miqe ya koma tasa Katifar ya zauna yana cin namansa bayan bata baya dayai. harya gama ci ya ture kingin gefe bata fara cin komi ba hannunta dai na riqeda robar ice cream din sai faman jujjuyata takeyi. gani tai ya dauki kayansa da brush da maclean ya fice waje tabisa da kallo ahankali bayan dago kanta datai daga kwancen datake. sauke ajiyar zuciya tai tareda maido hankalinta ga plate din naman dake gabanta, miqewa tayi zaune ta dauko plate din nan tadan fara cin naman sama sama. taci da dan yawa sannan ta tashi ta ajiye masa shi kusada kingin nasa bayan ta hadesu waje daya ta rufe wato plate dinta kife kan nasa. burinta kawai taji ta fara shan ice cream din nan dan haka tana komawa shimfidarta abinda ta fara yi kenan wato bude robar ice cream din tana sha tareda tandar lips. shiko yana gama wanka tun acan bayin ya tsane jikinsa tareda shafa body lotions dinsa ya saka kayan barcinsa sannan ya dauko kayan dayai amfani dasu ya shigo dakin. zuwa lokacin takusan shanye robar icecream din nan kuwa tassss. yana shigowa ko qwayar idanunsu suka had'u waje daya yai saurin dauke Kansa ya nufi katifarsa sannan ya nunke towel din da kayan daya cire ya koma ya zauna, sai lokacin ya lura da plate din nata wanda yasa mata nama kife akan nasa. matsowa yayi tareda bud'awa, gani yai bawani na kirki taci ba inda shi dai yasan iya adadin tsokar namansa daya rage baifi tsoka biyar ba amman yazo ya iske nama kusan cikon plate din nasa. juyowa yai saitin ta ya d'an saci kallonta yaga lokacin harta ida shanye ice cream d'in tana ajiye robar qasan gefen katifarta. sannan kuma yaga ta miqe ta nufi waje hannunta riqe da brush nd maclean. binta yai da kallo tareda ta6e lips a fili yace "cikin kine ai" haka ya kwanta ya bawa katifarta baya tareda jawo filo ya d'aura kansa a kai, sannan ya rufe jikinsa iya wuya da blanket ya fiddo wayarsa yana dannawa. babu jimawa itama ta dawo dakin ta kwanta a katifarta tareda juya masa baya itama ta lullube jikinta tareda lumshe idanunta hankalinta kwance bacci yai gaba da ita batareda damuwar komi ba. saida asuba sannan ta farka, ga mamakinta hangosa tai gefen katifarsa yana zaune saman pray mate ga alama sallah ya gama yake hailala da yatsunsa na hannu. tsoki tai ciki ciki ta yaye bargon jikinta tareda zuro qafafunta qasa aciki ciki tace "d'an mannin hauka qyashinma tadani yake nai salla nima, mtss matsalarka dan banda case dakai a yanzun" miqewa tai ta nad'e tulin gashin kanta daya warware wajen barci ta kunna 'yar hasken fitilar wayarta ta jingineta q'asa, nan kuwa dakin yasamu d'an wadattacen hasken ganin hanyar fita sakamakon nepar da aka dauke yasa dakin bada kalar duhuwa. ficewa waje tai. saida ta fara yin burush sannan tayi alwala ta dawo dakin itama ta shimfida praymate ta fara salla. harta gama bai tashi a wajen ba,hakama har tai lazummanta ta gama yana zaune a wajen ko waiwayota baiyi gigin yiba sam. kanta ta kwantas saman gefen katifar a hankali yayinda take zaune a gefen gadon bisa kan sallayarta itama. rufe idanunta tai tanason tuno abunda taji kamar yanason damun zuciyarta kuma a yanzun saidai bata samu cikakken yin tunanin ba yayinda d'an shauran baccin dake tartare da idanunta yai nasarar yin galaba da fararen idanunta. wanda itace bata farka ba saida gari ya waye tangaram gam. dasauri tamiqe zaune takai dubanta kan shimfid'arsa taga wayam babu kowa, cire hijab din jikinta tai tareda maida gashin ta baya sakamakon qin zama a daure dayake saboda sul6insa. muddin kuwa zata kwanta barci Indai har tanaso kada santsinsa ya warwaresa dole saita sanya hula mai raga ragar nan akai sannan zataji daidai bai sulluboba, to yanzun ita kanta batta ma cewa ga inda hular tata take bare. wayarta ta haska dan ganin lokaci, aiko lokaci babu qarya, lokacin ya nuna mata kansa a matsayin 9:33 na safiyar ranar asabar din. zaro fararen idanunta waje tai ganin mamakin lokacin da saurinsa. zata miqe kenan kamar ance ta kalli gefenta nanta ga dan qaramun plastic da kula tareda wata yar farar paper guntuwa kan Kular. komawa tai ta zauna tareda dauko paper ta bude. tafara karanta short note din kamar haka..... ~ga breakfast nan na ajiye miki please kici da yawa kuma ki tabbatar kinsha magungunan ki kan q'aida, nina wuce hospital kaiwasu baba nasu ki futa abinki lpia from your husband~. ajiye takardar tai tana wani murmushin jin dadin a dud sanda tatuno maganarsa ta qarshe dayace daga mijintan nan abun dadin tunosa take. a hankali ta bude cular taga ferfesun naman ganda ne sai dayan plastic din kakkauren tea ne a ciki tareda kayan shansa dangin su bread da butter a cikn ledarsu wacce take ta oasis. mamaki tahauyi a ina yasamu wannan iyayen kayan kalacin harkuma yakai asibiti?? shuru tai tana cigaba da kallon abincin da sam bai mata kama dana siyarwa ba kokad'an. wata zuciyar tace "to ko hjyrsa ce ke musu? dasauri ta kauda wannan tunanun Mara gurbi a kanta danta San kuwa ahalinsu ko mutuwa zasunayi suna dawowa Hjy firdausey bazata taba iya jin zata dafa musu qwayar gero kota shinkafa ta basu ita suci balle wannan delicious lunch haka daya fara zuwa musu tundaga ranar jia zuwa yau. tabe baki tai a fili tace "mima zaisa natsaya wani tunani ni?, indadai shi yajazamun wannan halin zaman da nike ciki, ai samo abinci kuwa ma ya Zame masa lazeem koda kuwa hajiyar tasa CE zaisa ta girka ya kawo mana muci kuma ehe" tayi maganar tareda murguda dan bakinta ta miqe tsaye ta cire kayanta ta fito waje ta kunna famfo taga ashe sun kawo ruwa, nanta tara boket ya cika ta dauka ta Shiga bayin dashi tayo wanka. harta futo ta shirya ta kira mamanta suka gaisa nanma bayan sun gama gaisawar ne takira sa'a still dai wayarta akashe, ajiye wayar tai tana tunanin anya kuwa wayar sa'a lpia kwana 2 tsit? shiru tai sannan ta jawo plastic ta zuba tea din tafara sha sannan taci naman shima, saida tagama sannan ta samu sasha magungunan. tadanjima zaune sannan ta miqe tafara gyaran dakin daga kan katifarsa ta fara da nunke blanket din sannan ta gyara masa kwanciyar beedshet din yaikyau sosai kuwa tsarin datai masan. daga nan taci gaba da gyaran dakin harzuwa tsakar gida ta share sa sannan tayi dan wanke wanken dasuka tara jia. tana gamawa ta dawo cikin daki ta kwanta zuciyarta cikeda son ganin baban ta da baba yawale. haka suka kasance dai a wannan tafiyar tasu dashi har tsawon sati 2 da kimanin 'yan kwanaki. lokacin ta warke sumul sakamakon temaka matan da magungunan dayake bata sukeyi gakuma yawan S shiga ruwan d'umi da take kamar yanda shima ya umarceta..yayinda shi kuma d'an zafin kan naku iyakarsa ya ajiye mata abincin safe inya fita kuwa itada ganinsa sai lokacin barci. abincin rana ya yame mata indome da qwai danshine yafi mata sauqin dafuwa ko taliya da manja da yaji dantafi jin dad'in cinsu, a dud cikin abinci yanzun sutafi kwad'aituwa da da'ukin cinsu. tun abun bai damunta yanzun yazo yana damunta dan aduniya kam babu abinda ta tsana iriyar yanda yake shasshareta ko mgn tamasa daqyar ma yake amsata gawani matsanancin kewarsa dake addabar ta a jiki, jikinta kuma yanzun dudda daman yanada d'umi amman yanzun ya qaru d'umin nasa mai dad'i ma. kuma gashi abun haushin koda asabar da lahadi ta kama wato ranar hutun kowane ma'aikaci to baya yarda yazauna gidan saiyai ficewarsa qarshe koda tayi abincin ranar dashi sam bayyaci saidai yaje gidansu yadauki Nasu baffa yakai asibiti, dudda tace yabari zata dinga girkawa ana kaimusu asibitin. amman amsar daya bata itace "daman kekiye musu can bare?" sannan kuma tayi tayi dashi suje asibiti kai tsaye yace"baba yace kada ta zo asibitin muddin bashine yakawota ba" abun ya isheta sosai har kuka tayi. daren yaukam na asabar taci d'amarar nuna masa halin kissar mata wacce bai tab'a sanin kalarsa ba kota nan wataqil ta wahal dashi ta huce hushinta dayake qunzuma mata a cewarta, shiyasa dawuri tai wanka bayan sallar isha'e, nan kuwa ta kwanta lamo bisa katifarta, lokacin q'arfe goma saura na dare yashigo gidan ya rufe, tuni taqara lafewa tanajin yashigo dakin kuwa tafara acting din yin nishi sama sama kafin ta kwalla wata qara da fadin "wayyo Allah na cikina ciwo...!!!" tuni tafara dubarar matso kwallan q'arya a fuskarta. aiko dasauri ya jefar da blanket dinsa dake hannunsa Wanda ya daukosa ya fara warware sa da shirin kwanciya barci yanufo kanta da sauri tareda zuqunnawa gabanta yafara yunqurin ruqo hannuwanta jikinsa na rawa...sai kuma ya janye hannunsa yasake durqusawa gabanta fuskarsa a tausaye yace"mi..mike miki ciwo kikace?" juyar da fuskarta tai gefe d'aya yanda bazai fahimci wane hali fuskar tata keciki ba,dan sotake ta qyalqyace masa da dariya ganin yanda tashin farko ya rud'e sosai over. kannewa tai ta juyo fuskarta idanunta sunyi narai narai fuskarta takoma kalar tausayi takamo hanunsa tana cijjje le6enta na qasa tana nishi, tasake qasa qasa da muryarta uwa patient din gaske sannan fa tace "cikina doctor ciw...ciwo yakemun" "to kinsha magani? Ta gyada kai tace "eh
Chapter 107 · 0% Book details