← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 178

Sashe 30

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

inno da suke tattauna maganar da baffa da ismail. dan yanzun harsun manta ma su rabonda dasusa mukhtar idanunsu dama basusa aka ba bare abun yadamesu, danma musamma ma inno dake da hawan jini, takan qara da cewa "inda ya zabi mace akanmu ai shiknn haka duniyar take ay ba kanta farau ba haifarwa mace namiji tana masa fatan shirya dai. suma kuwa abun Allah a ranar ne bayan gama sallar isha'e Zainab ta suntulo musu kyakkawar d'iyarsu mace barikallahu Masha AllAh, su baffa baqaramin dadi sukaji ba da Allah ya nuna musu d'an isma'il wanda bai yarda suba, shiyasa har nafila sukai ta godia ga Ubangiji,, ranar kam sunyi kwanan farinciki, danko washe gari aka farfado haihuwar maqota akaita shigowa kuwa tayasu murna dasa albarka kowa ya amshi jinjirar nan kuwa kamar karya badata yakeji dan yanda kasan zubin larabawa haka Allah ya basu ita. mutane basu katsewa zuwa gidan kuwa kullum saboda sake ganin jinjirar zainab, dan kuwa wasuma dawowarsu ganin jaririyar yafi a qilga dudda sun zazzazo kuwa, mutane suknce dudda kyan da Allah ya qawata jinjirar dashi saida ya qara mata da farin jinin mutane ta ko'ina, Allah kenan buwayin sarki shi daya gagara misali, haka akaita zaman barka har yau gashi daren suna. kamar yanda shi mukhtar ya tsara haka kuwa a daren suna yazo har wajensu baffa inda suke zama da baba yawale waje sallama kawai yayi batareda ya gaishe suba face "sannynku"' da yace yana daga tsayen sa kuwa, amsa sallamar baffa yayi shima dan ya zama dole kam, amman daga haka ko kallon mukhtar din baiba yaci gaba da jan carbinsa. baba yawale yace "mukhtar kazo ganin jinjirar d'iyar qanen taka ne a fiddo ma ita ka gani? Mamaki mukhtar yayi daman har matar isma'il ta haihu bai gaya masa ba,( kujifa shi ya fad'a masa ne?)jiyayi nan take ya sake tsanar su gaba daya jiyake dazai iya raba jikinsa ya kwashe jinin jikinsa ya maida masu baffan abunsu dayayi koya huta da tunanin cewa dansu ne shi kuma shi dan uwan isma'il ne! (ya subhanalla gskia mukhtar an nemeka an samu da yawa, AllAh shi kyauta dai to). duan baba yawale mukhtar yayi jiyake kamar ya ida qarashe tsohon ta hanyar yi masa zazzafar shaqa danjin zafin mgnr dayai masa nawai yazo ganin jaririya wancen gidan da talauci da babu dake mamaye dashi. shi koda yarinyar ma ta girma kowani yaji zaima je neman auren yar Ismail gidan aisai ya zugesa yadaina zuwa. kuma ma ya d'auki alqawalin yar isma'il indai ta girma itada yin aure saidai taga mata nayi dan kuwa kowa yayi nufin aurenta zai sa mutanen sa su zugesa ne in kuma yaga mutum ya nace tofa numfashi zai gintase a rayuwar sa dan ya tsani dud wani cigaban isma'il koda na farinciki ne kuwa. gani yake inyai masa hakan wata sabuwar hanya ce wacce zaisa maza su guji yarinyar insukaji lavarin kowa yazo neman aurenta yana mutuwa kuwa. tunanin hakan dayai ne yasashi sakin murmushi ya dubi baba yawale da baffa yace "baffa damn nazo fad'a muku zanen suna d'ana ne a babban masallaci bayan gama sallar asuba" ga mamakinsa saiyaga baffa yayi murmushi yace Masha AllAh damn gobe ake rad'in sunan 'yar isma'il kaga sai ayi duka a wuce wajen, baba yawale yace "gskia ne Allah dai shi kaimu lpia, aminn cewar baffa, Juyawa mukhtar yayi yace "sai anjimanku" baba yawale ne kawai ya amsa masa baffa kuwa shiru kawai yayi yana cewa aransa "hmm ta yaro kyau take bata qarko ay." Nansu baffa sukaci gaba da firarsu har lokacin tashinsu yayi sannan kowa ya wuce gida danya kwanta. ana gama sallar asuba kuwa akai sanarwa a masallacin na zanen suna inda d'an mukhtar yaci sunan khaleepa, 'yar isma'il kuma taci sunan heenduh haka aka yi addu'a mutane suka fara fita yarage daga baffan sai baba yawale sai kuma mukhtar da baffan yace ya tsaya kada ya tafi, ala dole ya tsaya kuwa yana tunanin mi baffa zaice masa a masallacin bayan ko jia sun had'u?. babu zato yaga baffa ya miqa masa hannun damarsa yace bani nan mukhtar?" cikin mamaki mukhtar ya dubi baffan nasa yace "baffa mizan baka, dan jikinsa harya soma rawa ganin yanda fuskar baffa ta koma babu alamun wasa a cikinta ko masassaqo. baffa ya qara tamqe fuskar sa yace"dud abunda ya sawwaqa cikin aljihunka indai kud'i ne su nikeson ka bani banson wani ja'inja bani kawai kayi abinda nace" mukhtar bai sake cewa komi ba ya tura hannunsa aljihu yaji babu wasu kudi komi face takardar dubu daya dan jallabiya ce kawai ya fito da ita a jikinsa, haka ya miqawa baffa. baffa ya kar6a yace Allah sanya alheri cikin ta dan mafi qanqantar sadaqi yana habbaka albarka ta aure ai daman fiye da mai yawan ma, juyawa baffa yayi ya miqawa baba yawale dubu dayan shima baffan ya fiddo dubu daya cikin aljuhunsa ya riqe kowa sai binsa da kallo yake tsakanin baba yawale da mukhtar din dan basusan manufar maganar baffan fa, baffa yace "yawwa yawale inason kai ka zama waliyin jinjirin mukhtar wato dansa khaleepa . ni kuma zanzama waliyin heenduh yar isma'il yanzun nan basai an matsa ba za'a daura wa jariran aure dan bazan juri ganin tarwatsewar zumunci tsakanin yayana ba ina raye ban mutu ba, kaga innai ma yaran aure tun yanzun kaga zumunci bai kauba dan zuri'ar mu zata qara yawa" ya juya ya dubi mukhtar daya daskare jin abunda baffan yace gaba daya jikinsa ya kab'e da kyarma ko motsi ya gagara yi, baffa yace "yawale kazama shaida ko bayan raina wallahi tallahi narantse da izzar mulkin Ubangiji Allah kuwa muddin mukhtar yasa d'ansa kaleepa ya saki heenduh yar isma'il dan wargajewar zumunci na har abada kamar yanda yk fata to wlh mukhtar kaji da kunnen ka indai ka kuskura kai hakan Allah ya isa! Allah ya Allah isa!! Allah ya isa!!! tsakanina dakai dan haka ka kiyaye wannan umarni nike baka bawai shawaraba" mukhtar yanaji yana gani a haka kuwa nan take baffa da baba yawale suka daura auren jariran da basusan abunda ke cikin duniyar ba, suna gamawa suka tashi suka fice daga masallacin suka bar mukhtar nan wanda yayi qaramar suma zaune awajen yanaji kamar bugun zuciya zata kashesa a wajen jin yanda zuciyarsa ke bugawa fat! fat! fat! zai iya rantsewa da Allah inda wani zaizo kusa dashi tofa zaiji sautin bugun zuciyarsa a wajen. wannan aishi ake kira a mareka a hanaka kuka kuma, rasa abinda zaiyi yayi yaji dadi koya samu zuciyarsa ta daina bugawa kawai saiya daura hannunsa 2 aka ya fashe da kukan baqinciki na auren dansa da heenduh yar maqiyinsa, Mukhtar cewa kawai yake tsakaninada ismail Allah ya isa nasan shi zaisa baffa yaimum hkn, haba baffa miyasa? wlh bntaba jin inda akai wannan auran ba tunda nike ace ranar rad'in suna jarirai nan take kuma a wajen a daura wa jinjirai d'in aure ba,! wayyo ni Allah na zubewa qasan wajen yayi, yayi goho yana dukan knsa da hannun sa yanamai fidda zafafan hawayen baqinciki da takaici yana cewa "firdauseey zokiji danyen hukuncin da baffa ya yanke mana a rayuwa wanda bai gamda muba"!!!!!!!!!!!!!, tunanin kawai toshi yanzun tayaya zaijewa da firdauseey da wannan zancen wane kuma hukunci zata dauka akansu baffa kuma intaji???
Chapter 30 · 0% Book details