← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 178

Sashe 17

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

zamo tamu yaya dan Allah ka tsahirta haka" mukhtar ya goge qwallar farinciki shima na ganin yanda yasa iyayensa da d'an uwansa kukan dad'i, shima yace "dukiya ta takuce qanena har abada dan haka koda ran rasata rankatakaf d'inta sabida kyautata muku billaheel azeem bazanji komi ba, dankune raina farinciki na da kuma bugun numfashi da farincikinku nike rayuwa mai dad'i q'anena dan haka kada kadamu,. kasa mgn Ismail kawai yayi sai dariyar dadi kawai take yana godiya ga Allah haka suma iyayen sukaita godia ga mai sama daya azaurtasu da 'ya'ya masu jinqai. koda su ismail suka fita daga gidan sakamakon jawo hannun sa da mukhtar yayi inno komawa tai d'aki wajen Zainab shi kuma baffa buta ya dauka ya shiga bayi. suna fitowa kuwa mukhtar ya iske mutane dafifi qofar gidansu mutane sama da 30 dud mabuqata kuwa, nan ya fiddo bandir na yan dubu dubu ya baiwa Ismail danya tayasa kason, haka suka dinga raba musu kudaden nan wani ya samu dubi biyar wani bakwai wasu takwas har goma in Allah yaci dakai samu zakayi wajen kuwa, mukhtar baibar wajenba saida ya tabbatas da kowa na wajen yasamu sannan. mutane saisa masu albarka suke daga nan kowa ya kama gabansa aljihunsa na nishi na marowa da yayi a iriyar wannan lokaci da aljihun mutane ke rama aisu kam sun godewa allah Allah shi qara bud'a masa, abinda kowa ke fad'a knn. ashe lokacin da mukhtar suke tsaka da rabon kudin nan meron tsimbe ta wuce zuwa gidan 'yar tata amman sam basu lura da ita ba, dan sabida jama'ar da suka rurrufesu bazai basu damar ganin wanda ya wuce ta hnyar ba, haka mero ta wuce ta isa gidan tana cijen leb'e zuciyarta a hasale cikeda baqincin yanda taga mukhtar ke rabawa al'umma kudade haka kamar bayyaso. Koda suka bar wajen gidansu salis suka wuce nan mamarsu salis ke cewa ai jia kawunsa wato qanenta dake bauci yakirasa akan maganar aikin daya samar masa amman zai dawo cikin kwanan nan, nanma mukhtar saida ya cikata da kudi taitamurna kuwa dasa alheri daganan suka wuce cikin gari kuma. Meron tsimbe kuwa a fusace ta bankada qyauren gidan mukhtar ta shiga tana faman qwallawa firdauseey kira da cewa "ke firdauseey ke fiddau kina inane maza fito, ta zauna saman kujerar falon gidan himmm da ita uwa saniya sai bud'a hancina take tana numfarfashi. da sauri kuma ta miqe jin kakarin da firdauseey keyi daga kewayen waje, can ta nufa kai tsaye kuwa, taraswa tayi firdauseey nata sheqa amai kamar zata amayo da 'yan cikinta a waje saida ta gama tsab sannan suka dawo suka zauna, dubnta mama mero tace "kedai wannan jarababben cikin bnda azabtar dake babu abinda yake, in bazaki iyaba zan kawo miki magani kisha saikiga ya fita salun alin babu wata sauran wahala kuma gareki" yamutsa fuskarta tai tace" kai ina wlh bazai yiyuba mama inason cikin nan kamar raina dan haka kibar zancen baras da shi. tave baki mero tayi tace" saikije kita kaya ay, ... ta canza salon maganar da cewa koda yake wannan d'an shine arziq'in mu, inda Allah ya kawosa cikin daula da jin dad'i kinga uban koda kuwa mutuwa yayi to dukiyarsa rankatakaf dunta ta yaron ce kuma muma tamu" ni yanzun wani qaton gululun baqincikin takaici naji, zuba mata idanuwa firdauseey tayi tace "miya faru mama ne"? Minenema bai faru ba, wai shi dan Allah mukhtar kudin nan da ciwon sadaq'a suka zo masa ne? "miya faru to mama nike tamvayarki fa? mero tace " hmm! ay gashi can qofar gidansu ya tara uwayen jama'a sama da maitan yana basu kud'i shida d'an uwansa sirikin wannan uwar kinbibin ga miji sai bayarwa suke, Quta wa firdauseey tayi tace hmm to nan mikika ganine mama? baida aiki sai kyautatawa sheggun tsofaffin iyayen nan nasa da d'an uwansa mutane kuwa kullum sai sunzo gidannan wajensa sama da aqilga, hmm wlh mama jia fa ina jinsa yana waya da dare wai ma'aikatarsu ta basu kyautar kujerun mecca mecca har guda 6 wlh mama inaji yace babansa da mmnsa ya basu kujera 2 sai nidashi 2 sai kuma qanensa da wannan shegiyar Zainab din biyu,, tuni mero ta dafe qirji tareda bugunsa da hannunta bafffff idaninta sun firfito tace "kutumar bala'en kan uban can kayyasa kai!! yo nifa? harda fa zainabu kikace fa? tuni idanun mero suka kawo ruwa jikinta har ciri yake tace 'ca6 to billaheel azeem da sakal, dole asan nayi, taff,, takama hab'a tai shuru, firdauseey tace kuma kinga azumi baifi saura kawana 2 ba a fara kinga knn salla na bada baya za'aje hajji din, kai gskia mama wlh dada yanda zanyi dasai na saki a jerin layin tafiyar nn na fidda matsiyaciyar zainab dinnan a tafiyar nn, d'agowa mero tayi tana huttai tace "to wlh kuwa nagaji da iskancin nan na mukhtar lokaci yayi da zaisan ainahin wacece meron tsimbe!, zaisan kala na, zai kuma san had'a iri dani ba alheri bane dan dud wanda ya had'a alaqarasa damu tofa ya d'ebo ruwan dafa kansa billaheel azeem sai nasa boka na marakusa ya juyar mun da kwanyarsa garemu ya mayarmana dashi bawanmu yazamo sai abinda mukeso zai aiwatar" dariya firdauseey ta kwashe dashi suka kashe tafi da uwar snn tace"dakyau mamana mai maganin kuka na shiyasa banda matsala indai kika fuskanci damuwata, wlh mama ba qaramun baqincikin nake jiba innaga yanawa iyayensa da dan uwansa wannan kyautatawar, kamar na kashesu nakeji dan baida lokacin na sai nasu kullum hk ake tafiya, meron tsimbe tace " hm ravu da matsiyata zasusan ni suka haifawa washi kuwa, waya fad'a musu barno gabas take wakuma yaje lafira yaddawo, babushi wlh, dan haka zaisan ya nemi iri wajen meron tsimbe d'oyin kashi mai gume ko'ina har a kasa rab'ar wajen wallahi nice nan kuwa hkn..
Chapter 17 · 0% Book details