← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 178

Sashe 26

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

👁🥡👁 🅿1⃣6⃣. *B* affa da qyar ya samu hawayen suka tsagaita masa ya shiga gidan isma'il d'in wanda har lokacin suna zaune a inda ya barsu. zama yayi tareda zuba tagumi batareda yace komi ba, baba yawale ya dubesa sosai yace "mlm Abdallah badai wajen yaron nan kake ba?" baffa dai baice komi ba saida ya zauna sannan ya dubi kowa dake wajen kana ya tsaida fuskarsa ata baba yawale yace"eh can naje yawale, saida ya dan dakata yana mai sake jin ciwon cin mutuncin da mukhtar yasa akai musu, hmm duniya knn wai ace d'anka? d'anka na cikinka ke cewa in kazo gidansa kada a kuskura abarka ka shiga ciki dan yayi kudi komi ne? kuma bama wai iya kaiba harda 'yan uwansa ma?, baba yawale ya katse wa baffa tunanin da yakeyi yace "to masha Allah babu laifi ai, dan nasan indai mukhtar din yaga kaine kaje masa da knka dole ya haqura ya daina halayen da ya tsirowa kansa ya saurareka'' 'd'agowa baffa yayi sosai yace "yawale nayi dana sanin zuwa na gidan mukhtar ba kadan ba, dan ko arziq'in ganin sa ban samu nayi ba sakamakon wani mummunan sallahu daya barwa maigadin gidan nasa wanda yace a fad'a mana idan daya daga cikin ahalinmu yaje masa......... atake kuwa baffa ya fad'a masu komi da mukhtar yace gameda barin zuwa gidansa. babu wanda jikinsa bai qarayin sanyi ba na tunanin cewa lallai ko abun na mukhtar yayi mtqr girmama. baffa ne kadai ya lura da kukan da inno keyi yayi saurin cewa"subhanalla inno ki daina masa kuka dan hawayenki garesa masifa ne dan zai qara dorasa awata iriyar masifar ma wacce tafi haka" cikin shessheqar kuka inno tace "ai abinne da ciwo mlm ace kamar kai da yawale mukhtar zai wulaqanta ku? gskia ban haifi d'an da za'a ce ya wulaqanta mu ba kuma sannan inci gaba da riq'esa a mazaunin d'a na gari ba, indai kuwa haka ne daga yau wlh na zare mukhtar daga cikin yarana dana haifa da ciki na,,,,,,,!" tuni baba yawale da baffa suka qara fadin "subhanalla Allahuma ajirni fi musibati wa khalapni khairan minha kada kice haka inno, kiyi tunani ai ada ba haka yake ba" Allah sarki kuwa isma'il d'an uwa rabin jiki, jin abinda inno take shirin yankewa mukhtar din baqaramin cira ta rawar jiki ba ta sake sauko masa ba nan take, dan haka yana hawaye ya kwantas da kansa kan cinyar inno yana cewa "dan Allah inno kada kice zaki tsine wa yaya mukhtar dan wlh inaji ajikina bayin kansa bane tursasa akayi ba halinsa bane kuma koma wanene kuwa yai mana sanadin faruwar rushe mana farincikin zumuncin mu wlh bazamu ta6a yafe masa ba" zainab da tun lokacin da aketa maganganun tana gefen inno banda hawaye babu abunda ke surnanowa daga kuncinta na tausayin su baffa akan wannan masifar data samesu tasan ko rantsuwa tayi bazatai kaffara ba wulaqancin da mukhtar yaiwa iyayensa dasa hannun yaya firdauseey matarsa dumu dumu kuwa dansu kowa yasan haka suke baza'a taba hada zama inwa daya dasu a kuma wanye lpia dan sai sun rarwatsa na cikin inwar nan gaba daya sannan hankalin su ke zama nasu ita da meron tsimbe mahaifiyar tata. har lokacin isma'il kuka yake kada inno ta tsinewa mukhtar sai lokacin ne tace"ni bawai nufi na in tsine masa nadai kawai ciresa daga sahun yarana har sai ya dawo da halayen sa masu kyau kamarda, wannan shine magana ta" tana gama fad'an hakan ta tashi tsaye Itada Zainab suka koma d'aki aka bar su baffa nan su uku jugum jugum sai da baffa yayi qoqarin yakice damuwarsa ya saki fuskarsa tareda nuna wa baba yawale da isma'il komi mai wucewa ne bnda ikon Allah dan haka su daina damuwa abinda yafi su taya mukhtar da addua dan ita yafi buqata a halin daya tsoma kansa a ciki, sun jima a haka sai daga bisani baba yawale yai musu sallama ya tafi. nan baffa ya sa isma'il ya tafi dakinsa shima ya kwanta kan dole isma'il ya miqe tsaye jiki babu lakka ya wuce dakinsa shi kuma baffa ya daura alwala ya shiga d'aki shima. mukhtar kuwa yana komawa gida bayan ya fadawa mai gadi abinda yace ya fadawa su baffa kai tsaye falo ya wuce ya hau samansa ya wuce toilet ya watsa ruwa sannan ya fito ya kwanta a gado zuciyar sa sai zafi take da tunanin wai har shine isma'il zai ware dashi suyi fad'a? lallaikam shima yace wani abu kuwa,, firdauseey ce ta murda kofar dakin ta shigo da turtsetsen cikin ta tafiya daqyal, zama tayi tareda dafasa sai lokacin mukhtar yasan ta shigo dakin ma, zuba mata idanunsa yayi da sauri ta riqo fuskarsa tana shafa idonsa da zuwa yanzun jinin cikinsa daya kwanta yadan fara washewa nn ta fara tambayarsa a rude da cewa "wayyo ni firdauseey mijina miye yasamu idonka ne haka? dud tabi ta gigice kuwa, daurewa yayi tareda qalato murmushi yace "kada kidamu wifey na, wannan ba wani abu bane ba ay, qwace hannunta tayi ta miqe tsaye tace "nidai fad'an gskia dan Allah" kwata kwata baisan 6acin ranta dan 6acin ranta hana masa shaqar numfashi yake cikin hankalin sa dan haka yai mata bayanin fad'an da sukai da Ismail yanzun. nan take ta fara masifa dacewa"wannan wane kalar dan iskan yaro ne wai? miyakeji dashi dahar zaice zaiyi fad'a dakai? yana talakkansa lis shida matsiyatan iyayensa har sunada qarfin gwiwar ciwa mai kudi kamarka mutunci, to wlh bazai yiyuba dan haka gobe goben nan za'a rushe gidan nasu muga ta qaryar iskanci da rainun wayau in kuma sun isa su 'yan kansu ne suce wani abu wlh kuwa da gaba dayansu zansa ka watsamun su a magarqama suda fitowa kuwa saidai a lahira" kamo hannunta mukhtar yayi yana cewa"zauna haba kiji uwargidan mukhtar ai bakida matsala abunda kikeso shi mukhtar yake so, dan haka gobe zansa a rushe gidan jibi a hau ginin sabbin shagunan da zan bude miki kisa 'yan haya koba haka ba matas? yayi maganar cikin murmushi dason burgeta. abinka ga mai son abun duniya da nuna ita watace nan ta kalaimayesa da manaqisarta kala kala wai taji dadi dan haka kuwa wanshekare kamar yanda suka tsara saiga masu tarakta dinnan ta zybda gidaje tazo ta saita gidan baffa ta kuwa rushesa tsaf kamar titi ta maida wajen sannan ta tafi, su baffa basu san mi ake ciki ba sai dai kawai ganin isma'il ya shigo gida hannuwansa dafe bisa kai yana kuka sosai ya zube gabansu baffa, a zabure baffa da inno sukai ta tambayarsa mike faruwa, kwata kwata ya kasa magana dan tsabar baqinciki sai saqyar ya iya dubn iyayen nasa yace"baffa ashe yaya mukhtar da gaske yake zai rushe muku gida, wlh gashi can ya gama rushewa ku taso idanunku su gane muku,, aida sauri baffa ya fita inno ma ta janyo mayafinta suka fita suna isa wajen kuwa daqyar suka gane inda mukhtar yai musu ta'adar kuwa sakamakon mutane da suka iske wajen dayawa suna kallon abunda mukhtar yasa akaiwa gidan nasu dan yana tsaye lokacin har aka gama kuwa snn ya tafi. nan kowa yaita tofa albarcin bakinsa, gameda rashin mutuncin mukhtar a yanzun kuma. Allah sarki inno tana yin arba da filin gidan nasu ba gida ba tuni ta zame qasa ta sume, a rude jama'a sukai kanta ana mata fiffita amman shiru inno bata tashi ba, aida gudu isma'il ya sa6eta a kafada ya nufi wani asibiti dake tsallaken titin anguwar tasu, cikin tsautsayi wajen tsallaka titin baisan mota ta tafoba tuni kuwa ta kwashesu ta watsar shida inno din a gefen titi, mai motar kuma maimakon ya tsaya saima qarawa motar tasa gear da yayi sanin dayai koya tsaya aljihunsa ne zai koka haka ya wuce batareda ya damu ba shin mutanen nan daya buge ko suna raye ko suna a mace ba. dudda mutane sunso kamo sa amman abun yaci tura baffa da baba yawale kamar su katse dan tsuma ganin jinin dake fitowa jikin isma'il da inno d'in. nan aka ida isar dasu asibiti bayan an kai zainab gidansu wajen mamarta sakamakon gigicewa datayi tana shirin fara naqudar dole a saman titi. daqyar likitoci suka tsaida jinin nasu, saidai sunyi asarar jini da yawa saida aka qara musu jinin baffa da na baba yawale sannan aka dora musu drip. saidai sakamakon gwajin da akaiwa inno ya nuna cewa jininta yayi mugun hawa ba kadan ba, dan haka likitan yaja su baffa office ya nuna musu cewar dud wani abu dazai sa hankalin ta ya dinga tashi to su kiyayesa matuqa dan zata iya rasa ranta ta sanadiyyar hakan. wasa wasa saida su baffa suka qulla sati 3 a asibiti amman kuma mukhtar ko leqe tame AllAh bai leqosu ba dudda yaji labarin hatsarin kuwa. a sati na hudu ne aka sallamesu suna shiga cikin anguwar kuwa sukaga har angama ginin shagunan inda gidan nasu yake har shago kusan ashirin da wani abu kuwa sakamakon wasu filin daya hada dasu ya siya din kmr ynda yace, yanzun haka fenti kawai ya rage a qarasawa gidan, AllAh sarki su baffan kallon wajen kawai sukayi tareda girgiza kai suka wuce gida kawai. haka rayuwa ta dore mukhtar kwata kwata ya d'auke qafansa da zuwa gidan iyayensa suma kuma sun haqura sunsa masa idanu indai duniya ce ai tafi bagaruwa iya jima kamar yanda mutanen anguwa suke cewa knn ga mukhtar a vayan idonsa, dan yanzun taimakon ma da yake wa jama'a ya rage sosai saiya ga dama yake bayarwa. watan haihuwar firdauseey ya tsaya dan haka kullum cikin saurare suke kamar yanda itama Zainab take sauraran tata haihuwar tunda satin ya kama bata komi face naqudar tsattsaye danma Allah yasa tanada juriya, gashi kuma itama ta kowane 6angare tana samun kulawa su inno da baffa da mmnta gakuma isma'il dan baffa kam cikin ragunansa daya siya guda uku harya bawa su isma'il din biyu yace a yankawa Zainab inta haihu, hakan kuwa ba qaramin dad'i yasa isma'il ji ba dan daman gashi duka duka yanzun wata yayi rabi bare yasa ran samun albashi har ya siya mata ragon sunan, danma sauqinsa sunada abinci da mahad'ensa. yau Monday tun da safe su mukhtar da firdauseey suka nufi wata
Chapter 26 · 0% Book details