← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 129 OF 178

Sashe 129

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

da su mama Zainab suka dawo kunga kenan kusan wata daya da Yan kwanaki, dan haka izuwa yanzun yakejin haqurinsa narashin jin ni'imar ta garesa yakusa kai maqura kam dan yamayi qoqari sosai. dan haka yana ko ganin fitar su mama Zainab daga dakin yayi saurin dawowa saman gadon ya zauna a kusa da ita tareda zuba mata idanunsa Uwa zai hadiyeta. Lumshe idanunta tai daga kallon nasa idanun dan kuwa fushi takeyi dashi akan danmi dud yau vai kirasu yaji lafian su itada baby neyler ba Yakama waya ya barta kashe. sarai ya lura da fushin nata ganin yanda take yatsine baki tana masa wani kallon harara qasa qasa. dudda kewarsa da takeji amman dannewa tai saima yinqurin miqe datai zata fice waje ta barsa nan aiko nan taji yasa dukkan qarfinsa ya matseta jikinsa gam ko motsin kirki kasawa tayi ma kamar an hadata da super glue taji. cikin rad'a a kunnenta daya lalubo ya daura bakinsa akai yace "baki iya kula da miji ba lollipop? kina ganin yanda mama keta tarairayar small dad"yayi mgnr cikin laso mata kennen nata.. sosai ta shige jikinsa ta narke cikin shagawaba tace"bakai bane kaqi bude wayanka ba dud yau, har ban san sau nawa bane na kiraka ban samu ba, to zaka cemun shima wannan ba kulawa bane knn?" tayi mgnr cikin tsunkulin masa gefen cikinsa. wata 'yar qaramar dariya ya saki snn ya dafe kansa alamun mantuwa. zuwa can kuma sai yace"sorry my sugar na na manta nafada miki ne @ jia yau zanyi aiki sosai hospital, kuma daman q'aida nane Indai nasan zanyi aiki switch off nake na dukkan wayoyina harsai nafito snn, amman kina cikin raina kowane motsina keda baby na lollipop" cikin wani salon harararsa ta turo lips tace"aikin mikayi to?" saida ya dan sumbaci 'yan jajayen leb'unan nata sannan yace "kamin kiji wannan amsar ki fadamun miya saki amai haka har mama na mgnr kaiki asubiti?" sauke ajiyar zuciya tayi snn tasake nutsar da idanunta cikin nasa tace "fersesun kan rago mama tayi shiyasa naji zuciyana na tashi hartakaini ga fita waje amai,,shine take tambaya na mike damuna, to nikuma dana rasa amsar da zanbata gudun kada ta gano abinda yasani aman yasani cewa mata ulcer nace ta tataso dayake tasan daman tun can Indai tatasomun har amai take sani yi, kaga kuma kai tun magungunan daka bata kwanaki na ulcer din tata tama warke tace fa, tokaga ashe ni gudun gara nai abinda naguda shi mama ta fada wato mgnr zuwa asibiti shiyasani kukan damuwa, saikuma akai sa'a kuma gashi kashigo lokacin... murmushi yai taredakai hannunsa a mararta yana shafa saman cikinta inda zuwa yanzun har wajen yadan fara tauri tauri, "laulayi ne kika fara yanzun shiyasa zakita jin kina qin abubuwa da dama yanzun" zaro idanuwa tai tace"wayyoni kenan bazan daina aman ba? please doctor kabani wani maganin da zan daina jin hakan" girgiza mata kai yayi yace"kiyi haquri lollipop na amman babu wani tsayayyen magani daka tsaidawa mace laulayi harsai yakai gejin dainawar tasa" saiko ga hawaye sharrr nabiyo mata fuska. "to ko baki son cikin mu cire sa inda baki iya jure kwaikwansa nanda d'an wani lokaci?" yayi mgnr cikin tsokanarta. wani kallo tai masa tace"inma wahalan tafi haka zan jure ne at kaima kasani mlm" dariya sosai yayi tareda sake matsota jikinsa yana shafa wuyanta yace"emhen nasan daman ai matar tawa jaruma CE" murmushi kawai tayi ta shigar da fuskarta a cikin qirjinsa tana shaqar qamshinsa mai saka mata nutsuwa. cikin qasa da murya tace"to kaima ynx ay saika fadamun miya tsaidaka asubiti sosai yau harda rufe wayoyinka?, ince dai ba wadannan sisters din bane iyayen shisshigi suka shiga aikin naka ba?" tayi mgnr cikin daure fuskarta tam tam. kamar zaiyi dariya ganin yanda tasauya fuska a zuwan kishi amman saiya kanneta baiba dan yasan zata iya botsare masa kuwa botsararrar tasan, a fili kuma yace "hoho mata! Mata! Iyayen kishi ko? to kwantar da hankalinki badasu nai aiki ba am yau, kuma tun misalin 12 na safe na kewa wasu mata da zasu haihu operations shiyasa baki jini ba , banine nasamu daman fitowa daga aikin ba sai ana kiran magrib dan sunada yawa wanda naiwa aikin gskia, kinga ma shigowa ta knn anguwar ko gida ma ban nufa ba nayo wanka nayo miki nan dan kawai naganki lollipop na" sauke ajiyar zuciya tayi tazagayo da hannuwanta saman sumarsa tana shafawa sannan tace"to bazasu iya haihuwa bane da Kansu sai anmusu operation?" taqarashe mgnr cikin jin tausayi. jitai yace "no ,, zasu iya haihuwa da Kansu man sosai,, abinda yasa 'yan gayu ne kamarki masu qwalisa shiyasa sukaqi yarda su haihu ta qasa.. tsaida mgnr yai yana kanne mata ido daya ganin yanda take masa wani kallon hararar shagwaba. cikin 'yar dariya yaci gaba da cewa cikin ta6e lips kuma "wai a cewarsu basu son *haq* nasu wai yayi damage nan danan shiyasa suke dubaran zuwa amasu aiki afiddo babyn ta cikinsu basusan wannan ba dabara bane dan yawan yankar fatar cikin d'an adam lokutta da dama anasamun mas'aloli ta jikin mutum,, dudda dai yanzun akwai kayan aiki na zamani sosai wanda za'a iya wa mutum operation a cikinsa qasa da sau 7 a maimakon uku da akeyi a qa'idan dokan likitanci,,dan dakatawa yayi ya ya mutsa fuska kadan sannan yaci gaba da cewa"Amman nikan bazan iya barin matata ai mata hakan ba saidai inbari inta haihun inma qaruwar tayi na tsaya na dinke abina cif cif yanda zanji dadin harka tamfar ranar dana bare ki a Leda" yayi mgnr cikin tsotsan lips dinta na qasa. Kunya da takaici dud suka isheta, kunyar datakeji shine mgnr dayai ta dinke hanyar jin dadinsa alal misali inta qaru gun haihuwa kenan nufinsa, takaicin dataji kuma shine yanda yakewa mata kalar wnn aikin, dan haka kamar zatayi kuka ta kallesa tace"yanzun dan Allah shikenan saikaga jikinsu din dole sannan zakai musu wnn aikin? shi tambayar tata har dariya tabasa yad'an dara sannan yace"aikin mijinki ne ay kulawa da lafiyan mata kota'ina inta kama kuwa zan duba domin temakonsu sugar na" yasuna fuska tai tace"zanyi zuciya nayi karatun doctor danna dinga qwatarwa mata 'yancinsu,, ganin yana mata dariyar mgnr tata datai ne yasa ta janye daga garesa tace"dan banson jin hakan ne daga bakinka ni daina fad'a mun wannan abun haushin mgnr ta'isa haka kuma" sake maidota jikinsa yai yana qoqarin had'e bakinsu waje daya danya ko rage zafi ne aiko yajiyo mgnr mama Zainab tana cewa ga abincin khaleepa fito nan kaci ga shimfida nan nai maka dan wajen nan yafi iska mai dad'i. dasauri ya miqe tsaye yace"to mama gani nan" yayi mgnr tareda daukar magun gunan daya bata yasaka a jikkarsa jikinsa a mace. Lura da hakan da heenduh tai har yabata tausayi hakan yasata ruqo fuskarsa tabasa full deep kisses wanda ta tabbatar sun shigesa snn ta janye bakinta cikin nasa sunawa juna murmushi yafito dakin. saidayaci ferfesun sosai sannan yawuce gida cikin farinciki da annushuwa dud inya tuno sugar lips dinsa kuwa. hakama bangaren heenduh sosai takejin farincikin tuno daddaden firar dasukai yau da doctor dinta hartai barci cikeda mafarkansa kala2. washe kuwa tunda sassafe Hjy Hadeeza da Hjy firdauseey suka dauki hanyan qauyen marakusa sune basu isa qauyen 'yan maraya ba sai qarfe daya da rabi na rana. babban tashin hankalin dasuka taras ne wato mutane suka samu sunyi dafifi saman bukkar bokw marakusa hakan ne yasa hjy firdauseey tambayar wata mata a wajen mike faruwa?,, budan bakin matar kuwa sai cewa tai "kitayamu murna Hjy wlh mugun azzalumin fitinanan matsafin kafirin bokan nan marakusa wanda ya addabi qauyen nan namu da dodannin matsafan nasa, to yau kuma cikin dare munata jin ihunsa da kururuwa harda tartsatsin wuta dake tashi kota ina a jikinsa damuka leqo ta katangu muka gani to munzata ma ko tsahin nasa ne daya saba yakeyi cikin dare,,,yau kuwa muna wayiwan gari anan mu jama'a muka iskesa nan ya qone qurmus ko tokar tsokarsa ba'a samu ba sai dai qwarangwal din jikinsa gata can yashe saman bukkarsa tsutsotsi na dandamalin na cinta" aikuwa da gudu Hjy furdauseey ta juya tana ihun kuka tana fadun"wayyo Allah shi knn madogarata ya tafi nikam yau na shiga uku na lallace a duniyar nan..said sambatu take yi sai daqyar Hjy Hadeeza takamota tana fadin"haba waikinyi hauka ne hjy firdausey kinutsu man musamu mafita aiba shikadai ne boka ba qwararre a duniya" kuka Hjy firdauseey take tana qarawa kamar zautatta take cewa"bazaki gane bane Hjy wannan bokan nayi imanin nagama samun kamarsa a duniyar nan,shike nan ni tawa ta qare'' tayi mgnr cikin gunjin kuka tareda daura hannuwanta saman Kai kafin kuma taji idanunta sun rufe tayi baya talauuu ta kife cikin ciyayi a qasa tu6us rica uwa giwa ta fadi, jikinta yahau karkarwa kamar wacce ciwon farfadiya yake son shigarta nan take kuwa a wajen....
Chapter 129 · 0% Book details