← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 178

Sashe 93

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

👁🥡👁 🅿4⃣3⃣. *T* unda heenduh ta shiga d'aki kwance take rigingine tana kallon silin yayinda wayarta ke aje saman shafaffen cikinta hannunta na akai kuma, tashiga tunani mai zurfi dan sosai itama ta damu da rashin dawowar baban har zuwa wannan lokacin. gashi kuma bayyada waya bare akirasa aji ko lafia shuru. jin wayarta na ringing ne yasata da sauri ta duba ganin kowaye mai kiran...6ata fuska tai ganin musaddiq ne yasata daga wa akaro na biyo da shigowar wanj kiran jiki a sanyaye. "halo my beautiful lady hope dai kina lpia da kuma wannan ne Nike roqon a yafe mana bamusan miyasa inmun kira ba'a amsa mana ba kuma koda text mukai bawani reply please tell me my beautiful baby miyasa?" yatsuna bakinta tai sannan tace"no bakamun komi ba bandai jin dadin jikina ne shiyasa kaga hakan,amman yanzun nasamu lpia" "Ayya to alhamdulilla dan bansan naga komi na matsa miki 'yar kyakkyawa ta". dakatar dashi tai da fad'in "naji ngd zan yi wani abu yanzun musaddiq" "to babu laifi nima ina kan aiki ne na turesa gefe nakiraki da taraddadin kozaki dauka koko? Amman yanzun naji wani qarfi mai tartare da kuzari ya zomin inda naji muryar beautiful na" "Ok ngd tum" abinda tace knn yaji tana qoqarin ajiye wayar dasauri yace"ah pls wait beautiful baby na kinko duba message nawa? a taqaice cikin qosawa tace "zandai duban tukun" dasauri yasake cewa"no bama saikin duba ma daman namiki text dinne sbd tafiyar gaggawa da tatasomun zuwa wani aiki a Cameron har tsawon 2 month shiyasa nai mk text din, yaci gaba da cewa nayi missing dinki na rashin ganin wannan 'yar kyakkyawa ta kamar na biyo iskar duniya ta nikeji wlh kodan na ganki heenduh sarauniya na Wanda ba'a cika samun mai kalar sunanki ba sai gidajen masarautan mu" hmn kuma ni gashi banje masarauta ba amman kuma Allah yaban sarauniyar kyawawan duniya" murmushi tai sannan tace "Sry musaddiq kamar gobe ne ay zaka gama aikin ka dawo inda kwanakin ba suna jimawa bane yanzun ko?" sauke ajiyar zuciya yai yace"naji dad'i 'yar kyakywa ta shiyasa nike q'ara sonki dan kin iya kwantarwa da mutum hankali" batace komi ba sakamon tuno khaleepa datai a yanda suka kasance a daren jiyan nan da kalar kuma dramar da akasha kan fitarsa.. bata ankara taji murmushi ya su6uce mata tana mai rufe idanunta taq'ara miqewa sosai kwance a katifar tata tana mai kuma q'ara shaqar q'amshinsa daya had'e dukkan katifar tata da marufin da suka lulluba kuma dashi.. sam shaf ta manta da musadiq nakan layi ma it's, saidai ta tsinkayosa yana cewa"alo alo 'yar kyakkyawa ta kina jina kuwa ko network ne ya riqeki minke banjinki?, furgigit ta dawo tunanunta tai saurin tashi zaune saman katifar lokacin ne kuma tad'an sausauta murya tace"network ne amman ynxun yy daidai" "yawwa shikenan to 'yar kyakkyawa ta amman dan girman Allah ki taimaka ki turomun pics din da kikai mun alqawalin zaki turomin kuma shiru? tana d'aya daga cikin mutane masu cika alqawali saidai ko halin mantuwa yasa ta mantan. dan haka tace "ok Sry na mantane afuwan" cikin wanj jin dadi yace"emhem koda naji dan nasan 'yar kyakkyawa ta batta qaramar mgn intace yes to yes ne haka ma in tace no tofa no d'inne" hakanan mgnr tasa tasata murmushi dan musaddeq akwai barkwanci lokutta da dama kobatai niyyar masa abuba saikiga tai masa dan tanasan mutum Wanda yasan mutuncin mutane dukiyarsa bata sa yadinga d'agawa ba kamar yanda kawunta keyi. amman a fili sai tace "zan turo maka ynxun kayi online you can see it" "tanxxx somuch 'yar kyakkyawa ta ki gaisar mun dasu mama dan Allah" "Tom" abunda tace knn ta latse wayar ta Shiga bincika photos nata nanta tura masa har guda uku babu Wanda naturally zallar kyaunta da dirinta bai bayyana ba kuwa a cikinsu. koda yagansu kamar zai rikice mata yabaro garin cameron yakeji yadawo ya ganta a ranar ya juya, saidai da qyar ta shawo kansa ya haqura ta hanyar yimasa voice message mai sakawa mutumin da ake son rarrashinsa cikakkiyar nutsuwa gamsasshiya tofa sai snn ya haquran yaso ta tsaya suyi chating amman ta zulle masa tana mai masa tunin aikin dazata taya mama sannan fane ya haqura badon yaso bane suka rabun. tana kashe wayar kuwa kamar daga Sama ta jiyo muryar baba Ismail a tsakar gida yana sallama. Allah sarki heenduh aida gudu ta miq'e kuwa tayo waje ta iske mama Zainab tsaye a gabansa riqeda hannunwan baba Ismail din tana tambayar sa ina ya shige tun asubar yau ne a rud'e. kan ya bata amsa kuwa har heendu ta ida qarasowa wajen ta rungume baban nata cikin murna harda 'yar guntun qwallan ta tace "babana munyi kewarka nida mama hankalinmu ya tashi sosai da rashin dawowar ka gida". murmushi baba Ismail yayi bayan ya shafa kan heenduh sannan ya d'agota ya kamo hannunta da hannun mama Zainab suka qarasa kan tabarmar dake tsakar gidan suka zauna. mama Zainab tasake miqewa ta d'ebo masa ruwan randa masu sanyi sannan ta dawo ta durqusa a gabansa ya karba tareda cewa"Alhamdulilla zainabu sannunki" zama mama Zainab tai gefensa tana dubansa cikin tsabar murna koda baikai ga cewa ga abinda ya tsaida sanba tasan tana cikin farinciki ma'ishi kuwa na ganin mijin nata lami lafiya zaune a gabanta itakuwa miyafi wannan farinciki a gareta cikin marecen ranar yau bayaga data cigaba da hamdala wa ubangiji a cikin zuciyarta kamar yanda ta fara tun farkon ganinta dashi a shigowarsa cikin gidan. "Huuh!! kai masha Allah Alhamdulila Allah mungode maka da kayo ruwa duniya Allah shi qara mana lpia dan darajar ma'aiki saw." abinda baba Ismail yace knn bayan gama shan ruwan dayai dan kuwa ba qaramar qishirwa ya taraba da "aminn" suka amsa. sake sauke ajiyar zuciya yai sannan ya dubi mama Zainab yace"kunjini shiru ko? Wlh nima hankalin na nan gida gunkun dan nasan zaku damu daman... kuma bakome ya jaza rashin dawowata gida ba sai rashin lpian baba yawale dan daqyar ya gama mana jam'en salla a masallaci da asubar n@n , tofa koda yagama kasa ma tashi yai daga nan inda ya sallame sallar...mutane nan muka rufesa ganin ko mgn yakasa ne yadafe qirjinsa da hannuwansa yasa yaya salis da shima yazo sallar a masallacin bada umarnin kada a d'aukesa zuwa gida kmr yanda wasu kW cewa yace zaifi kyau street awuce dashi asibiti to fa kowa saiya aminta da hakan dan sungano cewa ba'a d'au ciwo a kaisa gida a jinginar ba dudda dai lpia ta Allah ce a ko'ina ka zamo to Amman Allah shiyace ka nemi sauqin magani awajen bayinsa da yabaiwa baiwar damar sanin hakan dan samuwar lafiyar sauran bayin nasa marassa lafian. saida yaya salis ya koma gida ya dauko motarsa sannan muka nufi dala hospital wai Ashe su yajin aiki suke shiyasa muka juyo muka nufi hospital nasu khaleepa inda daman ita asubiti ce mai zaman kanta. to nan aka karbesa emergency aka Shiga dashi dan checking nasa mune tun abun asuba saifa yanzun muka samu muka dawo gida nida Yaya salis din danshi baba yawale sun basa kwanciya sakamon hawan jininsa daya taso masa lokaci daya ga kuma massara harda tari babu qaqqautawa. amman yanzun alhamdulilla inda yasamu barci shiyasa muka dawo gida danni komawa zanyi can wajensa da zama inda mune dai dolen nasa makusantansa a yanzun masu kula dashi" Mama Zainab tace "kaiii subhanalla ubangiji ma'allahu yabasa lpia" "aminn" cewar heenduh da baba Ismail dan har a ran heenduh ta tausayawa mai ran qarfenta fa ciwon nan da akace ya taso masa lokaci daya. sunyi shiru babu Wanda ke cewa komi dan matuqa tausayin baba yawale matuqa yai tasiri a zuciyar su.. babban abinda me tayarwa da baba Ismail hankali shine tunaninsa ina zaisamo kudin dazai biya asibiti da kuma sauran hidimar can? shiru yasakeyi kawai yana kiran Allah a ransa tareda tazbihi yanawa annabi salati.. suna a hakan ne kuma sukaji sallamar almajirai iriyar yan matasan samarin nan su wajen goma kuma kowanne Kansa daukeda buhun shinkafa wani kuma taliya ko macroni dasu man turkey da manja suma jarka biyar biyar kamar yanda buhun shinkafa da na su masara da cattons na taliya da kuma macronin suka kasance da yawa suma. dan wani zaiyi tsammanin cewa inyaga kayan wani dan matashin shagon saida kayan masarufi za'a bude. dady salis ne ke biye dasu a baya saida ya sallamesu almajiran da suka gama shigowa da kayan duka sannan ya zauna aka gaisa ya dubi baba Ismail yace"qanena kaga KO yanzun nan tafiya ta kamani can garin dana baro yayan mama ne baya lpia shima, kuma tareda Maman zamu tafima da Iyalan nawa dan dubosa" sosai su baba Ismail suka jajanta masa wa rashin lpian yayan maman salis din kuma surikinsa. yaci gaba da cewa "ga abinci nan qanena sannan kuma.... yad'an karkata aljihun rigarsa ya qirgu musu kudi dubu 150 ya miqawa baba Ismail yace"wannan kuma kwayi hidimar data taso a gida sannan ya sake qirgo wata dubu 60 daban ya sake miqawa baba Ismail yace"wannan kuma a siyawa baba yawale komi yakeso yaci inda narigaya danaje na gama biyan kudin gado harna tsawon kwanakun dasuka shard'anta masan zai kai dakuma magungunan dud na siya nan yagwadawa baba Ismail bill din na asibitin dakuma qa'idar yanda baba yawale za'a dunga basa magungunan nasa har jikin nasa yayi daidai. sosai baba Ismail ke fiddo hawaye bayan gama karanta bill din dayai danshi tunaninsa dabadan Allah ya kawo musu Yaya salis d'unba tayaya zasu iya biyan kudin nan na private hospital dinnan? dudda suna kulawa da patient dinsu sosai amman asibitin bata kamarsu ce bane masu qaramin qarfi inda su tasun masu qaramin qarfin ma aikata sunyi yajin aiki nan dai. ahaka yahau godiya da fadin "ngd sosai Yaya salis Allah shi qara arziqi mai amfani haqika ka riqe zumunci kadawo kana mana abinda d'an uwan na ya gaza munshi a rayuwa wato taimakawa rayuwar da Mike ciki a buqatance ngd Allah saka da alheri yajiqan magabata" dafasa dady salis yai yace"haddasu baffa da inno da sauran musulman Allah amunnn, sannan kuma shima yayan naka zai dawo ya kuma soka kaida iyalinka ya qaunaceku da izinin Allah wataran saidai labari kaji ko qanen?" gyada masa kai baba Ismail
Chapter 93 · 0% Book details