Sashe 23
Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
👁🥡👁 🅿1⃣5⃣ dan haka jikinsa a sanyaye ya wuni yinin ranar. dan koda ya koma gida Zainab taita tambayarsa akan "mike damunka?" taga jikinsa sukuku haka "bakomi" kawai yake cewa da ita. mafarin knn daya shigo gidan nasu yanzun yaga yayan nasa abun ya fad'o masa arai. isma'il yaji baffa yaci gaba da cewa "ida qarasowa isma'il, haka isma'il ya qaraso ya gaida iyayen nasa ya miqawa yayan nasa hannu yana mai cewa "barkadai da warhaka yaya" ga mamakinsu gani sukayi mukhtar din yaqi miqa hannunsa ga isma'il kamar yanda ya buqata, saima kallon su baffa da yayi yace "ku shirya kayanku waje d'aya zan turo yara su fiddasu sukai gidan isma'il d'in" yana gama fad'an hakan ya juya yai ficewarsa babu ko sai anjimanku. dukkansu da kallon mamaki suke binsa dashi inno tace "isma'il waimi ke damun yayanka ne kwanan nan? yanzunfa yau kwanansa 2 baima leqo mu ya ganmu ba" baffa yace "nimadai abunda nake gani knn tun dawowarmu na lura kamar ya canza koko yanada damuwar wani abunne yake 6oye mana allahu ta'ala a'alamu" cikin murmushi isma'il ya zauna cikin son kare d'an uwan nasa wajen iyayensa yace "kuyi haquri baffa ba shakka al'amurrane na rayuwa sukai masa yawa shiyasa bai samun shigowan kai da kai" baffa yace "koyanzun mafa daya ma shigo yana daga tsaye ko gaishemu baiba yake mana zancen tashi daga gida wai zai mana wasu 'yan gyararraki ne komi" isma'il ya q'ara bin gidan nasu da kallo yace "gyara kuma anan gidan baffa?" ni banga inda keda buqatar saba ay, inno tace "ehem kaimadai kace ay, wai cewa yai ko rufin kwanon asama zaisa asa na gini? shiru isma'il yayi dan shima yanzun baisan inda alqiblan yayan nasa ya dosa ba a taqaice ma. amman dan gudun kada ya goyi bayan su baffan ya zamanto angwasale wa mukhtar bajintar da yake son qara nunawa iyayen nasu na kyautatawa ya sashi kallonsu yace "baffa dan AllAh ku karb'i tayin yaya mukhtar, yana son gyara muku ne a matsayinsa na iyayensa sai naga bayyajin dadin inya yunquro zai muku abu kuma kuna sagar masa da gwiyoyi kuyi haquri baffa dan Allah yayi abinda yace din zai muku" shiru su baffa sukayi, isma'il yaci gaba da cewa "nasan baza'a d'auki tsawon lokacin nan ba ana aikin bazai kai kamar yanda akai na gyaran gidan ba" ajiyar zuciya baffa ya sauke yace "ni bawai naqi bane kawai dai bancika son qyale qyalen nan ba na rayuwa wanda zaisa ka rafkana da bautar Ubangiji AllAh cikin lokaci, dan jiya fa saida muka makara isma'il wajen sallar asuba sakamakon wannan abar da aka sanya ta cikin d'aki mai gumi daman ga sanyin da ake" ya dubi inno yace "yama sunnta?" Inno tace "aaaaa mlm niko yazan san sunnta wannan ai saisu 'yan boko kaga mu kuma da bamu sani ba ai saimu kirata da na'urar d'umama d'aki cikin sanyi ko? isma'il kuwa baisan sanda ma dariya ta kucce masa ba dan ya fahimci na'urar d'akin su suke mgn wacce mukhtar yasa musu wacce ke bada hot a weather ta sanyi, sai da qyal dai ya shawo kansu suka yarda, sannan kuma suka wuce zuwa masallaci shida baffan sakamakon kiran sallar magrib da sukaji anayi daga babban masallacin anguwar tasu. mukhtar kuwa yana fita daga gidan nasu sai yayi wani tunani kawai sai ya nufi gidan alhaju tanimu mai filin nan, yayi sa'a kuwa ya samesa shida wani abokinsa sunyi sallama zai koma ciki ganin mukhtar din yasa alhaji tanimu tsayawa nan suka qara gaisawa, anan mukhtar ya nuna masa yadai dawo kan maganar filin ne babu b'ata lokaci kuwa sukai ciniki ya siyar masa dashi yaje cikin gida ya d'auko masa takardun filin yai sign ya miqa wa mukhtar ya karba nan ya tura masa kudin ta account dinsa sukai bankwana ya koma cikin gida shi kuma mukhtar ya nufi gidansa. da daddare ne bayan sallar isha'e nan mukhtar ya miqawa firdauseey takardun filin ta karba tareda dubnsa tace "aa alhajina wannan fa? cikin murmushi yace "fili ne na siya wanda zan ginawa mama sabon gida fil a leda" cikin jin dadi da salon yaudara tace ''ayi haka alhajina kuwa? kada hidimar tai maka yawa ay, qwamma dai kabata gidan nasu baffa kamar yanda muka tsara" "kada ki damu ay matata wannan filin ma anan anguwar yake zanma iya cewa baifi gida 7 ba daga nan kafin namu" rungumesa tayi cikun dariyar dadi tace "tnccckyu alhajina,,,,,,,,,, to nace amman kuma maganar gidan naku fa wanda kace gashi canma kasa ana fidda kayan nasu ana kaiwa gidan Ismail? ya ya knn? basai ka barsun ba inda ka fasa?, dubanta yayi fuskarsa a sauye yace "bazan canza ba dan inada buqatar gidan nima, mizakai da wannan gidan alhaji na to? saida ya kauda fuska daga kanta amman hannunsa na bisa cikinta yna shafawa dan har cikin jinin jikinsa yake qaunar babyn cikin firdauseey, sanda ya sumb'aci cikin sannan yace cikin halin rashin damuwa ''sawa zanyi a rushe gidan duknsa inda gidan qato ne babba dan zan had'a sa da wani filaye guda 4 da na siya a bayan gidan sainasa ayi man shaguna nasa 'yan haya a ciki kota nan na huce hushin kud'ina na mecca dana kashe musu" dariya firdauseey ta qyalqyace da ita sosai dan ta lura kam mukhtar yanzun yayi nisa bayyajin kira, saida ta ruqo hannunsa guda biyun sosai tana shafawa tace "naji dadin hakan sosai kuma nima na goyi da bayan hkan alhaji na dan gskia kam asara bata da dadi koda kuwa ta miyan barci ne bare ta kud'i"!. miqewa mukhtar yayi yace "mtss bari ma naje naga in sun gama kwashe musu kayan dan gobe goben nan nikeson ganin gidan ya koma fili". "to alhajina saika dawo saimu tsara yanda za'a ginawa mama nata gidan ko?, yace "eh saina dawo d'in" tace "to adawo lpia amman dan Allah ka tabbatar komi an rakasu baffa dashi can sabon masau kin nasu a gidan isma'il" yace "zan tabbatar miki da hakan kuwa matata" abinda yace knn ya fice daga falon. yana isa gidan nasu kuwa dai dai lokacin da masu kai kayan suka fiddo fridge da katifa, yayinda shi isma'il ya fito daga gidan shima yana cewa musu "kai kai ku tsaya banda wnn kayan d'akin ai zaku fitar, inda kun gama fiddo na wajen kubarsu haka kawai, kamar daga sama yaji muryar mukhtar yace "injiwa yace su d'in ba za'a futar dasu ba?, yadubi isma'il cikin kallon tsanarsa dayake ji cikin ransa fiye da kowane mahaluqi kuwa a duniya yake tambayar tasa, Allah sarki isma'il da sauri ya matso wajen yayan nasa cikin fara'a yace"ah yaya ne yaushe kazo bn gnka ba ai, dan ni ina nan tun lokacin da aka fara fitarda kayan ma" ko kallonsa mukhtar baima qarayi ba bare ya basa amsar tambayarsa kawai saima ya dubi yaran da suke tsaye da kayan yace "kai ku wuce dasu kukai su can inda kuke kaiwa ku tabbatar da cewa ko tsinken tsintsiyar kwakwa nasu bai kwana a gidan nan ba" sukace "angama oga tuni wasu daga cikin yaran suka koma cikin gidan dan kwaso sauran kayan yayinda wanda suka d'auko fridge da katifansuka fuce dasu gidan isma'il, isma'il kuwa cewa yake a ransa "miye haka yaya ke fad'a harda cewa koda tsintsiya kada ta kwana saikace ana tada 'yan haya? 'yan hayar ma kuma marassa galihu? dudda haka ismail bai daddaraba da shariyar da yayan nasa yai masa ba yasake kusanto dan uwan nasa yace ''yaya amman sai nikega da ba'a fidda kayan d'akin nasu ba inda kace ginin sama kawai za'a d'an dora masu. kuma yaya... wata mugunyar tsawa mukhtar ya sakarwa isma'il da fadin "kaiiiiii jahilin mutum kaimun shiru bansan jin wasu banzayen kalamanka, wai bakasan cewa na tsaneka ba?! bansan ganunka?! naqi jinin ace mani kai d'an uwa nane?! nifa zaman nan da ake banqi ace baka cikin doron duniyar nan ba Ismail wlh kona huta ma da ganinka" cikin rawar baki da wasu zafafan hawaye jikinsa na kyarma kyab kyab kyab Ismail yake fad'in "innalillahe'wainna'ilaihurraji'un yaya?! minai maka?! nifa dan uwanka ne?!, dan girman AllAh ka yafeman innai maka wani laifi kayi haquri ka fad'a mun yaya" cikin dolen wani wulaqantaccen kallo mukhtar ya gewaye isma'il yanufi cikin gidan dasauri isma'il ya riqo hannunsa yace plsss yaya ka tsaya ka saurareni dan Allah kaj.... afusace mukhtar ya juyo a zafafe ya d'auke isma'il da wani wawan mari a kumatunsa guda biyu sannan yasa qafa ya doki cikinsa saiga isma'il duqe wajen a qasa baki ya fashe jini na futowa ta hancinsa sakamakon ha6on daya sauko masa babu shiri. cikin azaba ya dafe gefen cikinsa yana salati saida yadauki tsawon minti 15 ahaka sannan ya dago yaga mukhtar din bai wajen ya shiga d'aki yanawa yaran magana akan suyi sauri su qarasa aikin soyake ya kulle gidan, wani ruwan hawaye ne sukaita cigaba da saukowa isma'il aransa yake cewa "mike faruwan ne a rayuwarmu?! yau yayane yakaiga dukana?! abinda bai taba faruwan ba a tsakaninsu tun lokacin yarinta bare yanzun da kowa ya mallakin hankalin kansa yake shirin fara ajiye iyali?!" amman dudda haka isma'il bai sare ba danshi yafi tunanin wani laifi ne yaiwa yayan nasa wanda bai sani ba haryake hukunta sa da wannan iriyar kalar mummunan d'anyen hukunci. dan haka a daddafe ya qarasa miqewa tsaye ya nufi bakin famfo ya wanke fuskarsa ya nufi dakin harkusa da mukhtar sannan ya tsaya yace yaya k.... afusace mukhtar ya juyo ya kallesa tareda nunasa da yartsa Yace "wai kai dabban mutum d'in inane??! nace kadaina mun magana sannan kuma kada ka kuskura ka qara kirana da yayanka danni ba yayanka bane, I hate you in my life dan Allah, haba I'm tired,, kai wane iriyar mayen mutum ne nace ka rabu dani kaqi ko? to wlh dud illar danai maka konasa akai maka kai kajawa kanka, kuma koda a hanya ka sake ma ka ganni kada kasake ma ka kalleni dagayau barema ka nuna cewa ka sanni, kuma wannan gidan da kake magana to inma baka sani ba ka sani yanzun, daga yau ba naku bane mallakina ne ni daya na amshesa ne sakamakon in huce hushin asarar takaicin biya muku mecca danai dan haka na karb'i gidan