← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 125 OF 178

Sashe 125

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

saida qyar tasamu barci yayi gaba da ita daqyar. a marecen kwana 5 da dawowarsu mama Zainab ce suna tsakar gida itada heenduh. kan heenduh na saman cinyar mama Zainab datake faman sharce mata tulin gashin nan nata sukaji sallama. da "Amin waalaikaslm Maman ta amsa. "Maraba marabanku yaya salis kaida amnat 'yata.. dasauri baby amnat ta zauna kusada heenduh bayan gaisar da Maman datai. itama heenduh ta gaisar da dady salis din cikin girmamawa. "aunty beuty nayi missing naki, inafatan yau ne zakibini muje gidanmu ko? murmushi heenduh tai tajawo kallabinta ta daura tareda miqewa tsaye riqeda hannun baby ammat tace "taso muje daki na qanwata kamun su dady sugama gaisawa ko" hakan kuwa tabita dakin nata iyayen suka bisu da murmushi. sauke ajiyar zuciya dady salis yai yace"ay da yake jia muka dawo Gari ma Zainabu". mama Zainab tace"Allah sarki andawo lpia ya aka baro masu jiki kuma?" "Alhamdulilla jiki yasamu saidai aqara godewa Allah" maman tace "hakane wannan kam, kuma Yaya salis kayi sa'a gashi baban heenduh yana wajen sana'a amman nasan inda dai marecen nan yayi yanzun zaka gansa yadawo''. dady salis yace"to babu damuwa bari nashiga naga jikin baba yawale sannan" "to Yaya salis saika fito" haka yasaka takakalmansa ya fita yana mai gyara zaman babbar rigar jiqaqqar shaddarsa a kafadarsa. yana shiga gidan kuwa da sallamar sa anan yasamu baba Ismail zaune gefen baba yawale. cikin murna baba Ismail yaje ya rungumo yayan nasa nan suka zauna ana gaisawa yayinda yayiwa baba yawale ya qarfin jikin nasa shi kuma ya amsa masa da alhamdulilla kam jiki masha Allah ya warware. suma sukai masa ya ya baro mai jiki. cikin fara'a yace "yaji sauqi yana gaisheda kuma" saida aka natsa ne sannan dady salis yace"masha Allah yanzun inda nadawo lpia qanena saimu taso da tsohuwar maganar nan danace maka ta canjin sana'a, to daman dai inada babban masana'an ta dana bude ta kwanan wanda bakowa ne yasan mallaki na bane face mamana sai kuma Ku dinnan da Nike fadawa yanzun, ana siyar da buhunnan shinkafa da gero da su alkama dadai sauran kayan masarufi babu kalar Wanda ba'a siyarwa, koda kuwa odan Sama da buhun shinkafa da kowane kayan masarufi ma komin yawansu zamu iya kawo muku shi masu siya da sari kenan a wajenmu, yara na nazuba bawai kuma nike zaune a ma'aikatar ba. dan haka daga yau kuma daga yanzun na yanke shawarar nad'aka a matsayin babban manager na mai kula da shigen da ficcen komi na kamfanin tareda shugowar Duka kudaden cinikayyar ta hannunka a hannunka dan ina buqatar mutum cikakken kamili da amana had'i da ilimin zamani kamarka qanena a masana'antar tawa ta *S L S (salis) provisions store*". daga baba yawale din har baba Ismail saida sukai mamakin jin daman *store provision na s.l.s* da aketa fadi yanzun ko'ina a gari na kayan kowane nau'i na abinci mai kyau ga kuma rahusa na salis ne? ji sukai dady salis din yaci gaba da cewa"ada nufina nabaka isasshen kudi kaja jarinka kaima amman sainakawo shawarar baka wannan matsayin da qudirin nufin a cikin kason albashinka na babban manager wanda zaikai kimanin dubu dari 2 a wata zaka dinga Tara wasu daga ciki sannu sannu anan hannuna dan Inason kudin sukai mizanin matsayin da zamu hada gwiwa dakai wajen shigowa da kayan,, kai koda ace basukai ba nizan cika maka su ida cika kaima kadinga shugo da naka kayan kaga kenan dud wata ribar da masan'anta ta samu tareda ni da kai zamu rabata dan so nike kaima naga ka tsaya da qafafunka qanena, dan tuni nama gyara takardun mallakan masana'antar da sunan ka da nawa a jiki singing kawai zakai akai dafatan ka fahimceni?" tsananin mamakine na alheran salis yahana Ismail koda qwaqqwaran motsi danji yake kamar a mafarki yakejin batutuwan na zuwar masa. saida dady salis din yatabosa sannan yadawo cikin tunaninsa yayi saurin matsowa kusada dady salis din Yakama qafafunsa yana zubda hawayen farinciki yake cewa "narasa ma dawane bakin zanyi maka godia Yaya salis'' rungume juna sukai kowanensu na hawaye, yayinda shi kukan baba Ismail yafi ta'allaqa da tunanin alheran ubangiji Allah lallai tabbas sun yawaita ga bayinsa, kuma wani hanin ga Allah baiwane haka batun yake, dubadai yanda yayansa wanda suke uwa daya uba daya yayi cancelling rayuwarsa tasawa asoke masa dukkan takardun sa na dud inda zaije Neman aiki a qasar nan indai na government ne bazai taba samumsa ba komin qarantarsa kuwa bare girmansa, wanda sanadiyyar hakan dayai misu ne yasa rayuwarsu durqushewa wanda hartakai takawo wani sa'in saidai gidansa su kwanta da yunwa dud asanadiyyar dan Uwa daya? kai duniya. dayake Allah hanyoyin alherinsa yawa ne dasu gashi haqurin dayai da jarabtar da Allah yanufesa da ita shekaru da dama yau yakai ga gaci, inda babu zatonsa babu tsammani alheran Allah ya iskesa har gida lokaci daya, to shikam badole yai kukan farincikin godiyar baiwan da Allah yaimasa ba. dakuma nuna zallar farincikin sa ga salis din wanda yazame masa gudan jini ya daukesa qanensa na gasken tareda maye masa gurbun abinda yaci ace yayansa mukhtar ne yacancanta yai musu hakan bawai amininsa ba. yayinda shi kuma dady salis kukansa ta'allaqa yai kan tunanin yanda mukhtar ya iya yasar da gudan jinin sa qwallin qwal garesa a rayuwa haka akan mace wai? abin baqaramin sosawan zafi yakewa zuciyar saba sosawa kuwa mai q'una. shidai baba yawale kallonsu kawai yake cikin murmushin farinciki yanaji inama hadda mukhtar a wannan daddaden zaman nasu? amman yanaji a jikinsa zaidawo garesu mukhtar nan bada jimawa ba insha Allah kuwa. saida baba yawale din yataushesu sannan suka daina hawayen jimamim. anan kuma dady salis yaja numfashi yadauki wasu ruwa dake gefen baba Ismail yasha sannan ya ajiye tareda yin dan murmushi yace "zuwa gobe insha Allah zanzo da yara su fiddo muku kayanku akawo su nan dankuma saikun dawo gidan baba din saboda gyaran gidan naku daza'a fara. baba yawale yace "Kai Masha Allah salisu Allah shi qara kareka yasaka maka da mafificin alheri, Allah shiqara kuma arziqi mai amfani angode angode." bakin baba Ismail harsai da dady salis yarufe masa shi da hannunsa sbd godiyar tasa, "Ismail kaifa qanena basaika mun godia ba jinike kamar munfito ciki daya ne dakai da mukhtar dan haka babu batun godia a tsakanin mu kaji?" murmushi sukai Sannan sukaci gaba da tattaunawa kan lamarun harzuwa sanda dady salis yakoma gida dan baby amnat kuwa ma k'in binsa tayi azuwan sai tayiwa aunty beautyn tata kwana 2. saiko gashi washe gari tsab aka kwashe kayan aka kaisu gidan baba yawale. danko khaleepa saida heenduh ta gaya masa sun komo gidan baba yawale sannan yssani. shikan jiyai ma kamar taqara masa nisa dashi ne dan ynzun iyakarsa da ita kallo dan babu wata hobbasa dazaiyi ga baby amnat manne da ita koyaushe ga iyayen nasu kuma haba da kunya ay. Shiyasa kwana biyun nan dabai jita itada babyn saba ko kuzarinsa ya rage. saida aka kwashi kusan wata guda sannan aka gama musu gyaran gidan wanda baqaramin kyau da tsari yai ba sai daukar ido yake dan yasha tayils kam qasa dakuma bangunayen daga tsakar gida har dakunan. dan harda kayan daki dady salis ya canzawa mama Zainab na zamani. tuni baba Ismail kuwa yafara zuwa masana'anta bayan trening dinda yasamu ba koyan kasuwanci daga masabinta harkar. aranar yaune laraba da safe kuma suka dawo gidan nasu cikin farinciki, baba Ismail da mama zainab sai shi dady salis din dud suna tsaye cikin gidan "babu abinda baison gyara kam" cewar baba yawale yana murmushi shima lokacin dayaga gidan.. danshi hana salis gyara masa nasa gidan yai waishi yafi sonsa haka gidan tsoho maishirin tafiyan bankwana da duniya yau ko gobe ina yaga ta qyale qyale. salis dariya yai lokacin yace"baba yawale ai mutuwa bataga babba bare yaro dud wanda tanufo saita iso garesa. baba yawale yace "eh nasan da hakan kaidai banni haka d'an nan. baba yawale na gama sawa gidan albarka Yakoma gida. bayan su mama zainab sun gama gyara gidan komi a muhallinsa sannan suka kwanta sudan huta. heenduh nacikin dakinta kwance wayarta na hannunta dud takasa sukuni sakamon dud yau datakejin wayar doctor kashe batasan miyasa hakan ba. gakuma kewar baby amnat data tafi jia said abun yaqara hade mata. da tunanun hakan ne barci yai nasarar surarta. akuma marecen ranar ne Hjy hadeza tashiga falon gidan Hjy furdausey cikinta fal tsogami kuwa. saman kujera ta iske Hjy firdauseey tana waya da dady mukhtar bada jumawa basuka gama daidai sanda Hjy Hadeeza takai cup din lemu abakinta ta kurba ta ajiye. "aminiya ta sai zuwa ina kuma?" cewar Hjy furdauseey tana dariya gamida girgiza qafa tanadaga zamanta a hakimce. gyara zama Hjy Hadeeza tai tacr"uhmm gulma ta fiddoni dan infesa miki kema kiji dan nasan bakida labari" babu shiri Hjy firdauseey ta gyara zama sosai tana kallon Hjy hadeezan tace"harkinsa gabana yafadi wlh Hjy, miye ke faruwa haka dan wlh nasan alheri bakasafai labarinsa ke fitowa daga bakin kiba bare nasa rai ko shi ne" bushewa da dariya Hjy hadeeza tai tace. "Ai kinsan ba son labaran alheran nikeki ba bare na fadesa qwamma na sherrin zaifi dad'i" Hjy firdauseey tace"naji nidai fada mun mike faruwa haka?. saida Hjy Hadeeza ta dafa kafadar Hjy firdauseey sannan tace"kinkosan salis yadawo gari?. cikin tsoro Hjy firdauseey tace "wann...wanne salis din kike nufi?" saida Hjy Hadeeza tayi wani murmushi sannan tace"salis dai wanda kika sani abokin mijinki makusanci, yadawo gari dan kuwa yazama billionier na qashin kansa shima, motocin dayake hawa ma abin kallo ne, ke intaqaice miki karkiso kiga yanda yasa aka gyara gidan matsiyacin qanen mijin nan naki ismail abun saidai wanda yagani, wlh ingaya miki aminiyas sosai nayi baqin ciki kuwa dawannan canjin jin dadin Sabinta gidan Ismail da akai masa'' wani kutukutun mulmulen baqinci ya taso ya tokarewa Hjy firdauseey bisa qahon zuciya harta kasa motsawa tayi wani qwaqqwaran mgn, dan dud inda ismail zaiyi farinciki baqincikin abun takeji iya wuya kuwa. Hjy Hadeeza taji taci gaba da cewa"kiyi tunani dakyau Hjy ta billahel azeem dawowar salis ba alheri bane gareki, barazana ce a rayuwarki dan inada tabbacin zaiyi dud yanda zaiyi domin yaga hankalin mukhtar yadawo garesa kinga kuwa wa gari ya waya? zaki wayi gari kiga tsaf mukhtar
Chapter 125 · 0% Book details