← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 172 OF 178

Sashe 172

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

dazarar hakan ta faru nan take yarinyar da iyayenta gamida dud wani makusancinsu inkin d'ebe mijin naki da babansa , to sauran fa zasu haukanta subi duniya haihata haihata bazaku sake jinsu a rayuwarku ba, hatta yaron da maifinsa mukhtar bazasu tab'a iya bud'an baki su tambayeku Inda suke ba har a bada " sosai sukai murna nan yaci gaba da musu kashedin kada a samu kuskure wani ya gitta maganin ba khaleepa ba, hjy furdausey tace"baza'a samu matsala ba mlm ay" "kwantar da hankalinka mlm lamma na, ay aiki zai tafi daidai yadda akeso" cewar hjy hadeeza " koda hjy furdausey ta tambayesa nawane kudin, dahar mlm lamma zaice a'a nan hjy hadeeza taimasa alamun ya karba kawai yasha shagalinsa, nan take yace dubu 50, sai gashi ta fiddo dubu d'ari ta ajiye masa sukai masa bankwana suka tafi. koda suka dawo gida su hjy furdauseey suka dinga cewa zarah data kiyaye maganin wajen sakasa a kan lokaci,,, zarah na komawa gida lokacin har angama sallar isha'e nan cikin falo ta dake number ta zauna Inda tasan dud Inda khaleepa yake to ranar weekend da wuri yake dawowa gida ya huta, heenduh kuwa na gaban mirror a daidai lokacin tana daura kallabin shaddar data saka hadaddiya kalar purple tasha aiki kuwa shaddar uwa wata yar tsana wajen kyaun datayi. dan yanzun suka gama waya da khaleepa akan cewa suna hanya shida yunus, babu zato taji qarar shigowar motorsa a farfajiyar gidan, haka nan taji gabanta na yawaita faduwa babu adadi,,, zama tayi gefe gadon nata tana karanta "ya hayyu ya qayyum a ranta... sam taji tama kasa qoqrin miqewa. acan falo kuwa zarah na juyo qarar shugowar mota d'in khaleepa aiko ta miqe jiki na rawa tana murmushi ta isa bakin qofar shigowa falon gidan ta barbad'e maganin dukkansa daqyar hannunta na zafi sbd zafin maganin na jikinsa har yanzun. komawa tayi dakinta da gudu kuwa tana tsalle murnar ta ta zauna bisa gadon ta ta hard'e kafa daya bisa daya tana girgizasu tareda jiran sakamon. dai dai nan Khaleepa da yunus suka tunkaro shigowa falon suna fira suna dariya dan khaleepa shine a gaba yana cewa "wait,, wait mlm bari mai gida ya fara shiga gaba kamin tazurawa susawo kai,," yayi mgn suna dariya a haka har suka iso gabda shiga falon kuwa....
Chapter 172 · 0% Book details