← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 178

Sashe 80

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

👁🥡👁 🅿3⃣7⃣. *S* aida yad'an jima a toilet d'in sannan ya fito ya zura wata farar jallabiya suka sauko qasa nanma dai tsattsakuran abincin yai dan yanajin still dai bakinsa babu wani d'and'ano mai gamsar wa bare. dudda haka Hjy furdauseeyn taji dadi nanma ta barsu ta koma daki sbd hjy Hadeeza data lokacin. miqewa tsaye khaleepa yai ya dubi yunus bayan ya dubi agogon hannunsa yaga 4:34 A:M, na marecen ranar knn. yace"bari na shirya ka rakani hospital namu zan dauko wasu files ne a office na dana manta. "OK saika fito" cewar yunus din yana mai cigaba da latsa wayarsa" koda ya fito a shirye cikin qananun kaya dan khaleepa kam mayen qananan kaya ne shiyasa baya katsewa jubgosu dud inya tashi siyo su kuwa, dan har mncewa ma yake da wasu kan yasa. farin medial glass dinsa d'an qa'ida shine ya saka a fuskarsa zarah da dud inta gansa da glass din takance "yaya khaleepa kodan kaga yana qara fuddo maka kyawun kane muraran?". babu wata amsa shi kuma dayake bata lokacin illa ma yaci gaba da abunda yakeyi kan yabar wajen. haka suka shiga motar khaleepa suka isa asibitin nan suka shiga asibitin sauran nurses da sistoci daketa kaikawo lokacin sukaita gaishesa kamar yanda suka saba, haka har suka isa cikin office din nasa ya dauko files din ya fito kenan a bakin office dinsa sukayi clarshing da doctor mus'ab yazo wucewa nan suka cafke hannun juna suka gaisa sannan suka sake gaisawa da yunus doctor mus'ab yace "mutumina ya muka jika d'uf ne yau tun safe baka shigo hospital ba dudda naji wayarka switch off? dan yamutsa fuska khaleepa yai tareda dafe saman goshin sa ya saki sannan ya dubi files din dake hannunsa yace ''kagane ne musab banjin dadi ne yau shiyasa ban samu shigowa ba yanxun ma in urgently ne nashigo daukar wannan files din dan akwai abinda zanyi dasu" murmushi musab yayi yace"wsh you recovery mutumuna, koda yake mai duba mutane ne shima aka dan bud'a file dinsa koko sbokina yunus? dariya yunus yai yace "gskia kam mus'ab" dariya sukai sannan mus'ab yace"amman fa doctor yaune za'aiwa matan nan aiki fa koka manta? kuma sanin kankane sunfison aikin naka Inda harma ka sa musu rana toya knn ynxun? dafe goshinsa doctor khaleepa din yasakeyisannan ya dan huro sansanyar iskan bakinsa yace "na fada maka matsalata ay, kuma asibitin nan namu cike yake da qwararrun likitoci ta fannoni da dama bawai no kadai ba OK?, musab yace''yes dudda hakan dai please mutumina kaje kai musu kamar yanda ka maganta musu, dubnsa khaleepa yasakeyi yace"zanwa doctor bala mgn saiya fansheni ince fine? yunus har hada baki suke shida doctor mus'ab wajen cewa wait mike damun kanka ne yau? shiko gaba yayi yana cewa yunus inkun gama karadin naku saika tafo mitafi..... maganar tasa ta laqafe a bakinsa sakamakon momynsa da hjy Hadeeza daya gani sun tallafo zarah a kafada sai faman kukan wayyo Allah cikinta ciwo takeyi. suna qarasowa suka lura dashi dansu sam bama su lura dashi ba sai yanxun din. cikin rudewa Hjy Hadeeza tace "yawwa dan Allah khaleepa kamata ku dubamun mike damun yata wlh inna rasa zarah zan mutu ne dan itace burina ita dai ce dani... dud tabi ta gigice take maganar. Hjy furdauseey CE mai tausarta da cewa"kiyi haquri aminiya zata samu lpia ay insha Allah" adaidai nan ne wata nurse wace doctor khaleepan ya umarceta data kawo keken daukan marassa lpia ta iso su Hjy Firdausi dinne suka daura ta a kujerar sannan aka kaita room female one shima ya bisu yayinda doctor mus'ab yayi masu momy fatan samun lpian zarah din ya wuce danba likitan mata bane shi bare yasa hannu shima. shiko yunus motarsu ya koma ya zauna abinsa tareda kunna wata yar qaramar TV plasma dake jikin motar daga sama tareda qara ware ac din motar yana kallonsa abinsa. su kuwa su Hjy Firdausi zama sukai jugum jugum suna sauraran fitowar khaleepa din a dakin. acan kuwa doctor khaleepa cikin minti biyar yayi nasarar kwantar mata da ciwon cikin nata sakamakon wata 'yar na'ura mai qaramar danja jah daya hada ya dinga danna mata a cikin nata da taimakon wata sister laure data riqe masa qafafun zarah sakamakon wani fuzge fuzge datake na zafin ciwon dake shigarta. abinda ya basa mamaki bai wuce ganin yanda zarah din take sakin wani bleeding ba babu qaqqautawa kuwa, sosai yaji hankalin sa ya tashi dubata yayi yaga dole tana buqatar dinki a wajen to miye haka ya sa haQ nata ya bude haka wagaga a lokaci daya? tambayar dayaiwa Kansa kenan kansa sosai yaji ya daure masa, da sauri ya fita zuwa wajen su momyn yana isa dud suka miqe tsaye suna tambayar jikin zarah,, da dan hanzari ya dubi hjy hadeeza yace momy tun wane lokaci ne tafara wnn ciwon? Cikin rawar murys hjy hadeeza tace "tun jia ne data dawo partyn qawarta wajen goma na dare take fama da ciwon" yasake cewa "ok taci wani Abu ne bayan 12 na daren ranar? tace a'a dan tunda ta dawo bataci komiba saifa yanzun dana jiyo kukanta a dakin ta ashe abin ya ta'azzara danni dayake ina wajen hajiyarka a gidanku sai ynxun na dawo na isketa a hkn tana mad'od'owa a daki, nan doctor khaleepa ya juya ya koma ciki dan dama yayi mata tambayar ne kafin ayi mata aikin dan qa'ida ne in dai za'aiwa mutum aiki bazaici komi ba after 12 pm. dan haka nan da nan yasa aka canza mata kayan jikinta zuwa na aiki, dudda zarah na hayyacinta a lokacin amman tanajin sanda ya zurkula mata allurar nan tasu ta c.s mai rabaka da hankalin ka a jikinka ka koma tamfar gawa bata sake sanin inda kanta yayi ba ta daina motsi ma kwata2. yana gama yi mata allurar c.s din dan a ganinsa dinki kawai ne yakega zai mata ganin yanda yaga wajen ba kyu dan har tsikan jikinsa yaji tana tashi tsabar cakwalewar sa. nan yasa aka shigar da ita theatre room ya fara mata aikin tareda wannan sauran patient guda 3 da aka tsamosu dan musu aikin dama kuma ranar aka shirya suma za'a musu aikin dandai su nasu na haihuwa ne sakamakon qaruwar tiyar da suka samu kuma sune daman doctor mus'ab ke masa magana a kansu yanzun. to ganin na zarah din kamar nasu ne wajen shiyasa yana gama mata dinkin suma yai masu kalar nata dinkin ana gama musu dukkansu aka fuddosu zuwa other rooms. bashine ya futo zuwa wajen su momyn ba sai misalin qarfe 8 na daren ranar, Ko uniform dinsa bai cireba ya futa zuwa office dinsa inda Momyn nasa suke zaune lokacin har Hjy Hadeeza taci kuka ta qoshi harta sadaqat wataqil ma zarah ta mutu yanda taji shirun nan tai yawa. da sauri ta miqe tace ''Yaya khaleepa jijin zarah ta? zama yayi ya dubi momynsa da itama tambayar jikin zaran. saida yaja dogon numfashi sannan yace "yanzun komi lpia Momy saidai mu saurari farkowarta nan bada jimawa ba dan aiki akai mata". har hada baki suke wajen cewa"aiki dai?" "eh Momy theatre akai mata ya juyar da kallonsa zuwa ga Hjy Hadeeza yace "sorry to say momy binciken mu ya nuna anyi raping na zarah Wanda hakan ya haddasa mata zubar jini sakamon hakan data faru shine HQ nata ta kusan zama one ward mafarin knn akai mata dinki" yayi maganar yana mai zubawa Hjy Hadeeza ido. dudda tasan 'yar tata tana harka da maza Wanda sarai tasan ga jian bayan fitarta datai anguwa da safe tana dawowa wajen qarfe 9 na dare kamar ance ta fara Shiga dakin zarah din nan tai gamdakatar da 'yar tata uryatan itada wasu 'yan iskan samarinta a saman kanta suna lalacewarsu, subhanalla!!! maimakon data gansu ta dauki mataki saima taja qodan dakin ta rufe ta koma falo ta zauna a ranta take cewan shegiyar yarinya yanzun da dawasu na shigo dakin nata aidata sa naji kunya mtss tai tsaki gamida cewa Allah dai shi yaye miki wannan jaraba taki zarah wacce kika gado ta ga ubanki jarababbe. haka tai zamanta a falo har tsawon awanni sannan taga zarah din sun fito dakin itada samarin NATA zata rakasu nan sika ce wa Hjy hadeezar "hy Momy mu munwuce,, cikin maganarsu ta tantiran 'yan iskan 'yan masu hannu da shuni kuma wayayyun 'yan boko wanda duniyar ke gaya musu qarya. daga haka suka wuce zarah kuwa tabisu tarakasu har waje cikin motarsu,,, nanma sadda suka qara watsewarsu sannan ta fito a motar tadawo falo ta zauna kusada uwar tana sosa wuya na kunyar qarya, dan sarai taga shigowar uwar tata lokacin a dakin nata to batada qarfin kuzarin tashi ma bare itadai kawai tasan tanajin dad'inta batason katsesa lokacin shiyasa. Hjy Hadeeza tace "Ke yanzun dan ubanki daya haifeki da'ace mun shigo tareda Hjy Firdausi kina tunanin zata yarda da aurenki da d'anta bayan ta ganki ra'ayul aynun zigidir haihuwa ta da qattai har guda biyu a kanki kuna bankad'a dan ubanki eye? daya kike tunanin zan mata bayani ta fahimta shegiyar yar banzar yrnya lalatacciya? tayi maganar tareda dungure goshin zarah din. zarah kuwa cewa uwar tai ''haba Momy to kintafi kin barni gida nikuma gashi ina cikin halin buqata shiyasa na kirasu.... Classmate dina ne mun saba ay Momy kada kidamu inma gudun kada nayi ciki kikeyi inashan maganin hana daukar cikin ay" harararta uwar tai tace''ni dai ina fada miki ki kiyaye wlh dan dud randa kika kuskura Hjy Hadeeza tasan kina wannan bad'alar wlh nasan keda samun auren khaleepa haihata haihata dan nasan bazata bawa lalatacciya kamarki auren d'anta ba,,,,,,,,,maganar ta Hjy Hadeeza ta katse sanda taga zarah din ta sulale wajen tana shan kayan mayenta data fuddo cikin riga. tashi tai tabar mata wajen, haka washe gari da marecen ranar yau din tana baro gidan hjy firdausy kamar wasa ta iske zarah falo riqe da cikinta tana ''washh zafi!! kankace mi Abu yaci tura mafarin knn a rude taje ta kirawo Hjy Firdausi din suka kamata zuwa asibitin su khaleepa din sukai sa'ar saminsa kuma dudda basu zaci yana hospital dunba sanin da momyn tasa tai bajin dadin jikinsa yakeba shima. salatin dataji Hjy Firdausi tasaka ne yasata firgigit ta
Chapter 80 · 0% Book details