Sashe 62
Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
tana d'aga masa hannu alamun bye bye snn tayi cikin dakin nata da sauri tana share qwalla. fita yai a gidan zuciyarsa cike da tunanin kukan miye kuma take? yasan dai bana tafiyarsa bane dan tayi missing nasa, wata zuciyar tace kukan dad'i ne take q'ilan na katafi kabata filin wajen tasha iska da samarinta. saiyaji baiji dadin hakanba kuma da zuciyar tasa ta basa amsa ta samarinta. sosai zuciyarsa ta zurfafa tunanika kn heenduh batareda ya ankara ba. heenduh kuwa samun kanta tai da fadawa kan katifar ta tana kuka sabo tafiyar dataji yace zaiyin, yanzun bazata sake ganinsa ba knn sai nan gaba kuma? "wayyoni Allah"!!! Kalmar data fada knn cikin share hawaye. haka ta wuni har dare kamar maras lpia danko abinci kasa cinsa tai yanda ya dace. yau kwana uku knn da tafiyar doctor, heenduh dutta koma silently ko mgn batta sonyi sosai, mama inta tambayeta mike damunta? da ''babu komi'' take bata ansa dan ita kanta batasan mike damun taba bare ta fad'a. kamar yau laraba sun taso islamiyyan safe, sanye suke da uniform itada sa'a sun shigo layinsu sunata firarsu kan littfn sira da tarihin annabi muhmd ke ciki sai zuwa can sa'a tace''qawata muje gidanmu inason zamuyi wata mgn a nutse. hakan kuwa akai bayan sa'a sun zauna a dakin mamarta da batanan ta dubi heenduh tace "qawata dud duniyar nan banda qawa amintacciya sama dake kema kuma nasan hakan amman mizaisa ki dinga 6oyemun damuwarki? kwanan nan kowa ya ganki saiya san kinada damuwa dan har baba yawale saida ya tambayeni konasan damuwarki sakamakon kince masa lpian ki lau,naroqeki qawata dan Allah ki daure ki fadamun damuwar ki ta d'oro ko inada shawarar dazan baki dan Allah qawata" fashewa heenduh tai da kuka ta kwantar da kanta bisa qafar sa'a tace "qawata so baimun adalci ba bai kaini inda za'a daraj tani ba nida iyayena ba,! ki gayamun miyasa zuciyata zatace Sai shi ne dan Allah? miyasa!!! miyasa?!!!! ta fad'i hkn da qarfi. duttabi ta rud'a sa'a sai haquri sa'a take bata gamida rarrashin ta. daqyar ta samu ta baryin kukan "kigayamun waye wannan Wanda ya ciri tuta cikin maza harya karya tattaurar zuciyar qawata ya sanya ta kuka? kamo hannuwan sa'a heenduh tai tace"son doctor son Yaya khaleepa yaimun mugun zarge na qulli sa'a kuma wlh koda sonsa zai kasheni bazan ta6a bari yasan ina sonsa ba muddin bashine ya furta mun ba dudda nasan hakan bamai yuyuwa bane sa'a, cikin takaici ta cije le6enta na qasa tace" saidai na sani ne zanyi ta dakon sonsa a raina harna koma ga mahallici na ne sa'a!!" mamaki yai matuqar kama sa'a sosai najin hkn daga bakin heenduh wanda tasan daba a bakin heenduh taji wannan zance ba da bazata ta6a yarda ba kuwa. "walkahi qawata so masifane fa nikega mizai hana ki fada masan hakan inda shi d'in d'an uwanki ne? da sauri heendu tace "har abada wlh kima daina mun wannan maganar" sanin taurin kai iriyar na heenduh da sa'a tai yasata cewa"to shiknn qawata ubangiji Allah yasawa doctor sonki shima a ransa fiye ma da naki addu'ar da zanta miki knn Kunlun" sosai heenduh taji dadin adduar kuwa. nan sa'a ta sake cewa"kinsan kuwa babana ya saka ranar d'aurin aurena da hussain d'an yayarsa dake garin bauci nanda sati hudu?" da sauri heenduh tace"amman shine baki gayamun ba?! sa'a tace"ai shine mgnr danaso miyi dake danace miki ina cikin matsala saikuma kema kika shiga taki matsalar mafarin knn na danne tawa matsalar da roqon Allah har gashi kuma naji sauqin abun" daman nasa rai ne da auran mustafa saurayina, saigashi koda nai masa maganar ya turo magabatansa cikin wasa saiya kama kawomin dalilai wai shi baima tashi aure ba yanzun sai yayi masters degree nasa nan da tsawon shekara biyar daga nan na fahimci al'amarin nasa akwai yaudara dan damn ina zarginsa da son matan tsiya shiyasa na nuna masa babuni babu shi dan iyayena aure zasumun nan yakama borin kunya wai naci amanar qauna inda bazan iya jiransa ba just five years, kijifa?" nan na barsa bai dawowa na gida jia wannan abun ya faru fa" tsoki heendu tai tace "rabu dashi damn baimun ba ni wlh sabida mayen mata ne ko auren sa kikai bazai daina halin saba kawai ya maje ya d'aura miki damuwa, ki haqura da Husain dan yanada nutsuwa sosai kuma" sa'a tace"nima shawarar dana yanke knn nima bin umarnin iyaye sbd gobenka tai kyau, kuma sau tari abinda kkso ba alheri bane gareka sai wanda bama ka sa rai ba zaka ga yazamar ma alheri" haka sukaita tattauna batun, koda heenduh ta koma gida ta iske yunus ya kawo musu buhunnan abunci harda fridge da dubu 200 yace saqo ne daga khaleepa kamar yanda mama Zainab ta sanar da ita. hakan kuwa baqaramin famin sonsa ya sake jazawa heendu ba har saida ta kwanta barci sannan fa ta sami sauqin lamarn a cikin zuciyarta. akwana a tashi babu wuya wajen Allah tun satin da khaleepa yace zai heenduh taita fmn d'auki amman har satin ya wuce shuru bb doctor. dole ta gaqura har yau gashi sun shiga satin bikin sa'a. yau juma'a takama ake kamu gobe kuma daurin aure. 'yan mata cike a wajen kowace tasha ankon ta na kamu a cikin wani ash din lace mai d'igo d'igon baqi. dayake wajen kamun anan cikin anguwar aka samu hall tareda qawata wajen sosai sai walainiya yake. wajen cike yake da dangin amarya da ango tareda aminan arzuqa sai cashewa ake kan isowar amarya da ango da amarya kuma. acan kuma gidansu amarya an gama shiryata an dauko masu makeup sun gwangwaje amarya sa'a da heenduh baqaramin kyau sukai ba, musamman ma heenduh da kyaunta ya fita daban a wajen wanda ma bai sani zaice ma itace amaryar kai tsaye. dan kalar lace din ash colour da d'igon baqaqe nan a jikinsa ba qaramin amsar jar fatar ta yaiba, an gyara mata gashin kanta yai qwarya qwarya laya laya kwance a saman goshinta sannan aka daura mata wani farin flane da beba akai daurin dan kwalin yai kyau sosai yanda aka dan jasa baya bai 6oye gyaran gashin nata ba, sannan aka sa mata wata baqar duguwar sarqa mai yara yara da qulalai har saman qirjinta, sannan kuma da baqaqen 'yan kunnayen sarqar q'ananu. an gyara mata girar ta data idanunta, idanun sunsha eyeliner, yayinda idanunta suka qara wani mugun haske gwanin sha'awar mai kallonta, sannan aka shafe lips din nan nata da wani Jan baki pink colour hakan baqaramin kyau ya qarawa zagayayyar cikakkar fuskar heenduh ba har masu kwalliyan suka kasa jurewa suka dunga daukar ta fics tana dariya fararen haqoran nan nata reras dasu bari kalla masha Allah. saida suka gama kintsawa ne sannan amarya ta fito waje nan suka jera da ango suka nufi hall dunda ake wasu daga dangin ango suna take musu baya. da sauri heenduh ta fito daga gidansu sakamakon manto jikkarta datai. zaune ta gansa cikin majalissar su datazo cewa nan saman fararen kujerunsu. dayake hnyar ne ta kamun. ga alama shima ya gantan duba da yanda ya wani tsareta da mahukuntan idanunsa kamar mai mata gargad'in data koma gida. itako heenduh ta dage tambayar zuciyarta yaushe doctor ya dawo har bata saniba??? toko daren jia ya dawo inda gidansu amarya sa'a ta kwana ba gidansu ba? zuciyarta ta bata amsa da cewa "eh tabbas tabbas haka ne kam kuwa heenduh........!!!!"""