← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 178

Sashe 41

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

👁🥡👁 🅿2⃣4⃣. *Z* ama tayi tareda ajiye ledar Lazar gaban baba isma'il din tace "mlm gashi d'anka ne ya kawo mana" tayi maganar tana mai bud'e masa ledar a gbnsa. tuni wajen ya gume da q'amshin kajin wnda hakan yasa heenduh had'iye muyau babu shiri dudda taji haushin ambatar cewa khaleepa ne ya kawo ta, to ance musu suna yunwar nama ne dazai kwaso musu shi suga mayu ko kamar yanda uwarsa ke fad'a mata in taje gidan a lokutta da dama ma. baba isma'il yace"khaleepa dai? mama Zainab tace "eh mlm da harna gardama wajen karb'a gudun kada a koma 'yar gidan jiya shiyasa kawai na karba dan wlh bakaga ynda ya koma kalar tausayi ba, kuma gashi munce komi ya wuce gameda abinda babansa yai mana kaga knn idan mukaqi kar6a zaiyi tunanin mun qullaci abun kenan har yanzu a ranmu" heenduh tai zubut tace"to mama inyai tunanin hakan na cewa an qullaci abun ai mun huta saima ya daina shigo mana gida d'an qa'idar😏" hararta mama tayi tace"sannu marar kunya kinji? koko an tsomo dake cikin zancen ne em? sannan da kike cewa yabar shigo muku gida ke ba kina d'aukar q'afa kije gidan nasu ba? shashan yarinya kawai duk kunbi kun qyamaci junanku keda khaleepa, hm basai kuje kuyi ta yiba lokacin da zaku had'e kanunku bamuda labari saidai muga alamun hakan tartare daku inda lokacin da muke cewa kuso junanku a matsayin 'yan uwan juna kun q'iya sai kuje kuyi tayi ai, na ma gama tanka muku kan batun in kun gaji kwa 6aras ay" tuni heenduh ta cino baki tana fad'in a ranta"cabb nikam mam Allah sawaqa na shirya da wannan muskilallen mutumin dan ba halinmu d'aya bama sam sam bazamu ta6a jituwa dashi ba Inaga" kuma danma yaga kwana 2 na daina caja masa qwalwar sa shiyasa yake mun kallon uku saura kwata mako? Hmn Allah kaimu gobe kuwa zaka gani" abinda heenduh ke fad'a kenan a ranta. miqewa tai zata bar dakin mama tace "nace ki dawo ki zauna ki kar6i naki ko? "ni fa mama na q'oshi kuci kawai" sai lokacin baba isma'il yace "aa heenduh na abun kusa da baki ne tsaya ki amsa dan Allah inda Allah ya kawo mana saban tuwa" tsaye tai batace komi ba, kuma harga Allah ita tanason cin naman sai sai wanda ya kawo san ne yasa taji kanta kazar ma haushin cinta take. mama tace "inda tace battaci barta mana malam bakasan hali na yarinyar nan bane ni nasan abunda yasa tace bazata cinba bakomi bane kuwa yasah hakan face jidatai maqiyinta ne ya kawo mana ita". murmushi baba isma'il yai baice komi ba yasa hannu ya d'auko wata baqar leda cikin kayan sa na cefane sannan ya duq'o ya d'auko kazar nan guda d'aya ya saka ta cikin leda ya miqawa heenduh yana fad'in cewa "amshi kije kici heenduh na q'yale mamanki 'yata" haka heenduh ta kar6a ta fice tana jin sanda mama ke mitar cewa yacika goyon bayan 'yar tasa, shikuma murmushi yasakeyi yace "dole naso abata dan ita d'ai ce dani babu q'ari, tanaji sanda maman take magana murya a taushe take cewa baban 'oh ni kenan an ware ni yanzun an daina myn soyayyar nan ko?!, caraf taji babanta yace "zainabu ta aike ta daban ce tafo nan ma kiji wata mgn dan sonike aiwa heenduh q'anwa haka nan itama" aida sauri ko heenduh ta ida gangarewa zuwa dakinta a kunya ce, ita kam soyayyar iyayenta na burgeta, tana matuqar son miji wanda yayi masifar sanin kansa wajen love, jawo filo tai ta rungume sa q'am a jikinta tareda lumshe ido ita da zatai karatu saigata ta 6uge da rungume filo, wata zuciyar taji tace da'ace zaki samu saurayin da zai zama mijinki kamar dai khaleepa da kin dace dan tsarinsa ya nuna cewa zai iya fiye da yanda kike ma tunanin samun mijin. zumbur tai tareda wurgar da filon ta miqe zaune tana yamutsa fuska a fili take fad'a da zuciyar tata da cewa "tur!! tuf tuf! da wannan kalar mummunan tunanin naki dud ki rasa wanda zaki kawomin tunanunsa ma a daidai lokacin da nike tsaka da jin dad'i sai wannan mai mummunan halin? gskia my heart banji dadi ba" miqa hannunta tai ta janyo handouts dinnan ta yakice tunanin komi ma a ranta ta fara karatun ta, sai gab da magrib sannan ta ajiyesu ta miqe tsaye tana yin miq'a dan ta gaji sosai daga nan kuma ta fita tsakar gida saiga sa'a sunci karo da ita, rungume juna sukai suns murnar sake ganin juna. anan sa'a ta shiga d'akin mama tai mata ya jiki sakamakon heendu dataje gidan nasu dazun take fad'a mata maman bata lpia, anan sa'a tace mamanta ma na mata ya jiki zata shigo dubiya kuma insha Allah. mama Zainab tace"bakomi sa'adatu ngd ai" nan suka tattara suka koma d'akin heendu ko zama basuyi ba aka kira sallar magrib sa'a tace "kai limamin nn qawata da azarbabi yake ina lura dashi fa da zarar lokacin sallah yayi wlh ko second d'aya bazai mana gyaransa ba zakiji ya wani d'ale mumbari yana kira" qyalqyacewa da dariya heendu tai tace "ke sa'a kiji tsoron Allah fa, yanzun sa'idon naki har yakai gasu baba yawale liman? hmm to nidai wlh daga nan kada ki qara ta6omin baba yawale na. zama sa'a tayi tace "hmm AllAh jiqan mlm tsalha shiyasa nike yinsa kan ya rasu zakiji har sai masallacin cikin anguwar nan wasu daga ciki sun kira salla sannan zakiji sa shima, anman tunda ya rasun nan aka nad'a wannan kakan naki yadaina mana gyara wlh haba babu wanda yaqi bati fa qawata" heenduh tace "hmn anman da cikin azumi ne kinfi kowa qagarar ya fara kira" dariya sa'a ta saki tace "ah aikuma cikin azumi masifar son baba yawale nike yanda kikasan nai miki qwacen sa na aure maki shi fa kodan kiran sallar da yake mana da wuri" wata dariyar suka sake yi heenduh tai kwanciyar ta tace "mudai Allah ya d'auke mana dan ko ni hutun salla nike wanda na farasa daga yau. wani qarar ihun sa'a ta saki wanda yayi dai dai da wucewar mama Zainab ta gefen dakin ns heenduh, alwala tayo, dan haka dakin ta shiga ta dubesu tace" ku kuma ihun miye kuke haka da dararraku saikace baqin mahaukata? maza ku fito kuyi salla kada lokacin ta ya qure muku" heenduh tai saurin cewa "sai dai sa'a taje tayi tata sallar mama danni bannayi hutu nike" wata hararar mama ta sakar mata tace"to rasa kunya nace ki kawomin laluri ne? shiru heendu tai tareda kanne dariyar ta ganin yanda sa'a tayi wiqi wiqi tana sosa jiki alamun sanyin ke ratsata gashi tana shirin ta6a ruwa. dole sa'a tabi mama zuwa waje nanta dauro alwala ta shigo d'aki tana kyarma saboda sanyin daya qara saukowa a lokacin. dariya heendu ta saki tace"shiyasa nike son harkar hutu wlh qawata hmmn musamman ma lokacin sanyin nan fa, kinga knn tab'a ruwa sai naso znyi" sa'a tace "hmmn kedai qawata bari, bari dai na gama sallar tukun" bata jima ba ko ta sallame nan ta koma ta iske heendu gefen katifarta dake shimfid'e a q'asa tana cigaba da qara duba littafin handouts dinnan. zama sa'a tai tace "nifa ko karatun test din nan banyi ba qawata dan narasa gane wane abu zanyi choice? kinsan malaman nan muggai ne abunda ka karanto bashi zasuyi maka test akaiba shiyasa kawai na haqura innaje ai muna a together dake banda matsala, bare yanda lectures d'in nan su mlm bala yakeda da tsinannen zafafawa kan test, wlh kuwa ya baqinsa ya baqin halinsa tsohon kawai" heenduh tace "yanzun sa'a bazaki karatun ba da gaske? "Yaseen kuwa bazan ba qawata" shiru heendu tai jin wayar ta na ringing sunan musaddiq ne ya fito, lumshe ido tayi tace a fili "Wayyo ni Allah wannan karon Allah ya had'a ni da super glue fa" leqowa sa'a tayi ganin mai kiran ne yasata cewa "yi maza yi maza qawata kiyi holding kada ta katse" tsoki heendu tai taq'i d'agawa saida ta katse ya q'ara kira sannan ta d'aga da cewar"wai miye haka dan Allah musaddiq?! waiba d'azun mukai waya ba kuma miye naka na q'ara kirana?! sakin baki sa'a tayi tana kallon heendu jin wulaqancin datake kartowa musaddiq din yanaji kuma, baida zuciya dai to. to ina laifin ma wanda ya ce yana sonka? girgiza kai kawai tayi tace "qawata har yanzun banga gwanin da zai miki gwanunta ba Indai ta fannin maza ne, amman zanso inga gwaninki gskia konan da wane lokaci ne kuwa. abunda sa'a take cewa knn a ranta. saida heendu ta gama wayar ne ta dubi sa'a tace"hmn wai kinsan mi yace ne qawata ? cewa yai wai gashi yazo shagon da ake siyarda manyan wayoyi ya rako abokinsa siyawa budurwarsa wai dan Allah in fad'a masa wacce nikeso saiya suyomin ni kuma nace yabari inna tashi koda yaushe ne zan fad'a masa saiya suyomin sbd yanzun banda buqata" tayi maganar tana dag'e kafada 🤷🏼‍♀. wata raruma sa'a takaiwa wayar heendu itako tai saurin sanya wayar ma'ajiyarta wato cikin bra dinta ta kwanta ko luf,, sarai tasan sa'a tsab zata kira musaddiq ta basa sunan wayar, saiko gashi ile sa'a tace ''wlh qawata bakiyi ba, dan iskanci arziqi na kiranki tsiya na hanaki? shike nn ai kin kwafsa da yanzun kin rabu da wannan rakani kashin banza kawai,, mtsss Wlh kinma b'atan rai tafiya zanyi," da sauri heendu ta janyota tace "haba qawata banson class dina ne fa ya zube shiyasa na nuna bnda buqata amman bawai dan wani abu ba" tsoki sa'a tai tace "kina sane fa da bikin qawarmu hafsat bala da zamuje cikin satin nan kuma sanin kanki ne 'yan boko na qarya zasu halacci wajen ga kuma yan school namu da suka sa mana ido kuma kinsan dole ai qaryar touching phones a wajen gashi kuma dagani harke d'in babu mai touch bare muma muyi bagarar nan da ita, gashi kuma an mana tayi abun yazo a sa'a kin mana baqinciki kince masa a'a mtss wlh banza ce ke tanan fannin" heenduh tace "ke dalla malama shouting din nan naki wlh ya fara hawar mun kai, dole sai munje da wayar ne? yanzu
Chapter 41 · 0% Book details