← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 133 OF 178

Sashe 133

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

kwana uku" gaba daya miyan bakin Mama Zainab taji ya qafe mata a baki tareda jin wata mummunar qishin ruwa dake shigarta sakamakon maqoshinta daya bushe qayau2. daqyar ta kalato murmushi tace "anya kuwa dai doctor wannan inaga ba result din'yata bane ko kake fad'a?" murmushi doctor ladan yai yace"kada ki damu munsan aikimmu kuma abunda nagani ne a rubuce shina fada miki kisani kuma awo baya qarya dan haka ga result dunku nan" yayi mgnr tareda fadin"next" saiga wani mutum yashigo ga alama shine mutum na gaba wanda za'a duba. daqyar mama Zainab tamiqe daga kujerar datake kai tareda daukar result din tafice kotakan heenduh bata biba dan gaba daya kwanyarta ta tushe hatta tafiyar datakeyi jitake kamar ba qafafunta bane ke taka qasar ba Uwa saman iska takejin ta. dasauri heenduh ta iskota tana gabda fita asibitin daidai inda babu yawan jama'a nan ta zube gwiwoninta qasa gbn maman tana faman kuka hannuwanta hade👏🏻take cewa "mama dan Allah kiyi haquri" cikin zafin qunar rai mama Zainab tadubeta hawaye na zubowa a fuskarta itama sannan tace"ni zaki tozarta cikin anguwar nan Hindu? mi iyayenki mu muka rageki dashi daidai azancin qimar iya qarfinmu? dahar zaki je ki bayarda kanki ga wani?!!. yaushe kika zama haka heenduh? yanzun tarbiyyar danai miki kenan kirasa sakamakon da zaki bani saina cikin d'an waje? wasu zafafan qwalla suke sharewa dukkansu ganin hankalin mutane yafara zuwa Kansu yasa mama Zainab qara share qwallan fuskarta zuciyarta kamar zata fashe dan baqinciki bama sosai take ganin heenduh ba dake zube gabnta, bayan ta share kukan taci gaba da cewa "heenduh kin ganni nan ko? to insha Allah daga nan gidanmu zan koma da zama dan bansan da wanne idon zan fadawa mahaifinki wannan ta'asar dakikai ba kije ke kuma dan kanki ga abinda kikayo" haka mama Zainab tafuce daga asibitin heenduh kuwa saka fuskarta tai cikin jikinta tana kuka wanda muryarta harta dishe, sosai takejin bazata iya taba furta cewa khaleepa ne mai asalin cikin nata ba, hakan ta kudurta a ranta dan tana tunanin in tace shine tofa batasan kallon da iyayensu zasuyi masa ba wanda take tsoron hakan na'iya janyo batawar sa da iyayenta wanda bazatai fatan hakan ba ta qwammace tabar sirrin a ranta tareda daukar dud wani hukunci dazatai *gamdakatar* dashi daga iyayenta na wahala ko kuma tsananin azaba kala kala darashin nuna kulawa kmr yanda mamanta tafara mata yanzun na juya bayan ta gareta lokaci daya datai!!.. hawaye nabin wasu a fuskarta ta dago kai tana hango mman tata bakin titi tsaye goslow ya hanata tsallakawa zuwa anguwar tasu dayake dmn asibitin bayan titin anguwarsun CE sikazo ga dazun din, dan tasan maman tasan bata iya zuwa qasa shiyasa tataro musu abun hawan. kafin kuwa tadauke idanunta ta hango mama Zainab har ta kuwa tsallaka titin hankalinta kamar bai kanta wanda hakan yasa ita mama Zainab din Sam batasan da tafowar motar nan mai tsinannen gudun gaske ba ta 'yan smogal tayo kanta kiyyyyy!!!!! wata qara heenduh ta qwalla tareda furta"mamahhhhh ta"!!!!! tuni numfashinta taji yaja ya tsaya mata cak zuciyarta na bugawa da tsananin qarfin gaske fat! fat!! fat!!! kafin ta ida sulalewa wajen qasa ta zube a sume ba'inda ke motsawa a jikin nata kuwa...
Chapter 133 · 0% Book details