← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 150 OF 178

Sashe 150

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

farin ciki daga gareni ko misqala zarratun adai wannan lokacin wannan alqawali ne, sannan kuma Abu na 2 shine bazan taba yarda akaini gidan kaba kamar yanda ake fada Allah kuwa saidai akai maka zarah din ita kad'ai kaga saima kufi sakewa a gidan ku babuni 'yar had'in aure na iyaye bare natakura muku"tana gama fadin hakan tajuya zata bar wajen aiko taq'i daya khaleepa ya yariqo cinyar hannunta tareda juyo da ita zuwa gabansa, har wata 'yar qara tasaki sanda taji zafin riqon nasa uwa zai ballata kuwa taji lokacin, harara tasakar masa tace''miye haka ne? sakarmun hannu fa mlm kaje can kariqe matarka zabun ka'' kallon ta kawai yake shi dud wannan shirmen maganganun nata bai daukesu wasu Ababa face kawai na zallar kishi dan yasan data huce zata daina masa wannan borin sudawo daidai, dubanta yai yana sakin wani dafaffen murmushi idanunsa nakan baby face dinta kallon jajayen yan hyalan hyalan lebunanta yayi uwa tashafa musu janbaki amman babu komi data shafa musu akai natural haka suke daman,ji yake uwa ya jawota jikinsa yatsotse mata su tass koyasamu nutsuwa. yana qoqarin mgn ne yaji yunus yace"haba headache namu atemaka arage zafin nan da aka dauka damu haka man a ajiye kishin nan gefe muzauna muyi mgnr yanda zaku gudanar danaku hidiman bikin keda qawayenki kinga babu lokaci sauran mana sati 2 fa,,, afusace tajuya tadubi yunus tace "ina ganin girmanka yunus dan haka kaimum shiru da bakin ka kaima kannadawo kanka" tayi mgnr tana banka masa harara shima. dariya takusan qwacewa yunus yy saurin saitata saiyai saurin maye gurbin faffaden murmushi a madadin dariyar, dan yasan dayayi dariyar nan tsab headache zata qara qufuluwa ne dasu , dan haka cikin murmushin yace "a'a to Inda abun hakane kam Allah huci zuciyar ki rankishidad'e, nadaina cewa komi din kamar yanda kika buqata gani aside nazama dan kallo'' tsoki tai tareda tabe baki tace''karufawa kanka asiri knn"juyowa tai tadubi khaleepa dayaketa kallon ta yana sakar Mata wani kwantaccen murmushi sam tama lura babu damuwan komi a tareda shi, dasauri ko tajanye fuskarta danji datai gabanta na faduwa sbd kallon da yake matan ne tarigaya datasan ma'anarsa tuni kuwa, dan kallo ne nanuna tsananin buqatuwa yake Mata dud sanda taga yana matashi kuwa tasan miye aransa, amman saita basar tadinga kallon wani wajen daban tasake daure fuskarta tareda furta cewa"kada ka ciremun hannu karabu dani mlm zan wuce"tayi mgnr tana murguda masa d'an bakinta najin masifa. Cikin kalar muryasa yace"yanzun bazaki daina tsiwace tsiwacen nan ba da fushin ba lollipop na?, kai tsaye tabasa amsa da fadin ''eh danka ji ma kuma ka sani yanzu ma nafara maka hakan ehe" matsota yayi kurkusa da jikinsa yazageye hannuwansa ta bayan qugunta yariqo to gam Jin tana kicikicin zillewa yasashi cewa''nanda kwana qalilan zan mallakeki cikin gidana fa to miye nawani yimani kakkafi da yanga damage? please calm down man sugar na yayi mgnr tareda ida rungumota tsam a jikinsa enlargement ballons nata kuwa cike saman qirjinsa yajisu lausasa. cikin takaici da tsakanin kunyar abinda yai matan gaban yunus din aiko daqarfi ta turesa daga jikinta ganin jikinsa har ya soma saki. nan takoma baya tana sauke numfashi tace ''ko mafarki kayi naganin cewa zan tare cikin gidanga to Allah kuwa inka tashi kayi sadaqa dan abinda bazai taba yuyuwa bane"tana gama fadin hakan tafuce dasauri ganin datai khaleepa din yana qoqarin isowa wajen nata da nufin sake kawo mata caffa kuma ita bata shiryawa hakan ba. murmushi sukai suda yunus sannan suka fuce suma suna dariyar mgnr shirmen mgnr tata dansu a shirme suke jin komi nadaga bakin nata kam. wasa wasa har sauran sati daya biki amman khaleepa yaqi yarda WA yunus sufara tsarin fatittika na bikin dan har yanzu heenduh taqi kwantar da hankalinta itama shiyasa yakejin komi bai masa dad'i shiga, danta rantse masa bazata halarci party ko daya ba suje suyi da zarah mafarin knn abubuwan suka qara dame masa. gefe guda zarah sai faman shiri akeyi na gyaran amarci dan tunda satin bikin yashigo take tara qawayenta maza da mata kullum sai sunje anyi party na innaniha ayita shaye shaye da sauran abubuwan ko kyan gani babu kuwa, zarah ta yanke shawarar yin wannan fatittika ne tun sanda tajewa da khaleepa da mgnr shagulgulan bikin kai tsaye yace bazaiyi ko daya ba in ita zatayi taje tayi yabata change. mafarin knn take bushasharta na fatittika fitsararru da friends nata maza da Mata haryau gashi gobe daurin aure. mama zainab ma tayi qoqari sosai wajen gyara d'iyar tata ciki da waje harna tsawon sati kuwa, shiyasa nn danan fatan heenduh taqara kyau ko'ina ta gitta tashin qamshi ne kawai ke maye gurbin wajen, kallo daya kamata bazakace tana d'aukeda ciki bama sam tsaban bin jikinta dayai. hausawa na cewa komi akasawa lokaci zanzo, yaukam dandazon mutanen a bababan masallacin juma'an dake anguwar tasu baba isma'il bayan sllr jumaan daaka gama suka shaida daurun auran zarah da khaleepa ananne kuma take mai shaila awajen yasaka amsa kuwa ta masallacin yana qara jaddadawa mutanen wajen da cewa kamar dai yanda dady mukhtar yabasa izini, nan yafara dacewa "Aassalamu alaikum jama'a gawata sanarwa daga bakin iyaye ango since a shaida muku cewa yau ango khaleepa da qanwarsa 'yar uwa tasa heendatu auransu ya jima da d' auruwa tun azamanin jarintarsu aka daurasa, wannan jaddadawa ne ga jama'a domin wanda baisani ba yasani yau,, aureeeee daikam ya jima da dauruwa tsakanin heenduh da khaleepa, dan haka yanzu heendatu na mazaunin uwargida ta khaleepa zarah nazaman Amarya ubangiji yasaka albalrka ga auran gamida zuria dayyaba,........ " Ana gama daurun auran kuwa aynan take wajen kuwa yakaure da hayaniya mutanen nata mamaki auran heendatu da khaleepa kowa nata fad'in albarkacin bakinsa kuwa, cikin mutanen dasuka halarci daurun auran kuwa harda haruna mai khemist da abokansa wanda mamaki suma nawai jin jimammen auran heenduh da khaleepa jiki a sanyawa haruna yaja tawagarsa suka tafi, dan harga Allah yaso heenduh amman yazaiyi Inda da auranta ba batun so yaqare kam yana fatan Allah masanya masa dawacce yake so kamar heenduh shima. ango khaleepa kuma yaci adonsa cikin dakakkiyar shaddarsa dark blue sai maq'in nera take, yasha yar ciki da babban riga kansa hular nan ta zauna sosai gwanin kyau haka kwantacciyar sumar sa ta kwanta bayan gashinsa nakan nasa baki Kirin sai sheqi yakeyi kuwa, qafafunsa sanye da takalman sawu ciki, hannunsa d'aure da agogonsa q'irar diamond light blue, kowa kuwa yaggansa yasan yana cikin farin ciki lokacin na ganin yau lollipop nasa zata zama mallakinsa suyi rayuwa gida daya na har Abadan abidina, danshi harga Allah mantawa ma yake dawata zarah cikin rayuwarsu, lollipop ce kawai tsaye cikin rayuwarsa. hakanne yasa yasamu yazulle daga cikin abokansa su yunus kai tsaye gidan baba isma'il yashiga dudda iyayen mutanen yan biki dake cike da gidan kuwa sai tsiya ake masa amman haka yashiga kutsawa ciki burunsa kawai yaga heenduh a lokacin saiko yaci karo da mama zainab tafi to daga daki, babban sanda yace Mata bak'in abokansa ne sukazo zasu gaisa da heenduh shiyasa yashugo da knsa, take kuwa mama zainab tace''ayya khaleepa ay tun safe heenduh na gidan kawunka salis,, Sosa kansa yai cikin yar kunya sannan yace"to mama shikenan bari saina kaisu can din'' yana fita kuma nan waje yasamu su yunus yakoma cikin su yana shirin ma yunus zancen zuwa gidan dady salis din knn nan yaga maroqa da mawaqa goge na gargajiya sun tunkarosa suna qarasowa kuma suka qara bude muryan su suka hau masa kirani da fadin '' *🥁🎸kaga jajirtaccen tsayyen namijin Mata 2 gimbiya heenduh uwargida sarautar mataye ta kyawawa da fatima zarah, gimbiya heenduh mai babban suna wanda sunan sai a gidan masu masarautar musulman nuggeria shikan dada bayyana sarauniya heenduh uwargida ga khaleepa Allah ja kwana yabar masoyi da masoyiyarsa injini Usain mai goge jiqan audun malam*.. sosai khaleepa yaji dadin wannan waqar dayaji mawaqin yafiya saka lollipop din nasa aciki ,nan kuma yabude bakin aljihunsa yaita musu ruwa dubu dubu karshen kudin Nigeria suko suna kwashewa suna sawa aljihu bashine yabar musu ruwan kudinba har saida su yunus suka janyesa sannan. sosai yunus yaji dadin hkn danshine dmn dakansa yasanar da maroqan yanda zasu tunkari khaleepa da waqar tasu sanda yashiga gidan baba ismail din. daman abokan angon sun hada reception nasu na abokai da aminan arziqa da zarar an gama d'aurin auren shiyasa dud yawancin abokan suka fara nufan garden din gidan so khaleepan inda nan suke fatin nasu. yarage daga yunus sai khaleepan tsaye wajen mota wanda ganin wajen yayi sauqin jama'a yasa khaleepan ya dubi yunus bayan yakalli watch din hannunsa sannan yace "yunus kashiga ciki kufara event din nan please zanje wani waje ne yanzun nan zan dawo'' cikin mamaki yunus yace '' dadai kahaqura an gama event dinnan sann kaga ynzu friends namu zasuta tambsyar ina ango fa" 6ata fuska khaleepa yayi yace"no,, no bazan iyaba yunus dud yau ban saka lollipop na a idanuwa naba ,wlh ba kaji yanda nikejin jikina ba uwa nayi rashin wani abu daga jikina please yunus kaje kaji da friends din namu kaban 15 mnt naje gidan dady sales naga lollipop na ko naji qarfin jikin gudanar da event din nan yau cikin dadin rai., " sosai yunus yaji tausayin khaleepan,, lallai so maisaka abu laushi komun taurinsa kuwa, bayaga haka dubi yanda so yakejan abokin nasa dud miskilancin nan ya'ajesa gefe yana nan nan da abokiyar fadan nasa ada ayanzun kuma abokiyar rayuwa ta aure tahar abada, dan haka cikin murmushin sauke ajiyan zuciya yunus yace"jeka abokin adawo lpia tareda gaishe man da mutuniyar tamu , murmushin Jin dadi khaleepan yasaki yace"yawwa friend tnxx yanzun nn zndawo" yy mgnr cikin saurin shiga motorsa ya wuce, shima yunus ya wuce wajen abokan nasu, daidai qofar gidan dady sales yy parking yarasa tayaya zai shiga gidan, aqalla yajima zaune a cikin motor harya fara yanke shawarar yafito ya aiki yaro sakamakon wayar tata dayaita bugawa taqi shiga, yana shirin kirawo wani yaro saiko ya hango baby amnat tafi to daga gidan nasu. da sauri ya bude motor yafito itama tana hangosa tayi murmushi tareda nufosa tana fadin "oyoyo uncle khaleepan " sanyayyen murmushi yai yace" oyoyo babyna amnat aunty ki heenduh na ciki ko? "eh uncle doctor
Chapter 150 · 0% Book details