← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 178

Sashe 48

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

cikakka, sai manyan fararen idanun nan nata da sune suka q'ara haskake fuskar tata tareda d'an hancin nan nata mai kyaun gaske wanda ya dace da fuskarta, ga lips dinta jajur dasu masu laushin gske, haqoranta ma farare ne tasss reras dasu. jin da sa'a tai heendu ta tabota tareda cewa" Haba qawata wannan kallon qurillan fa? dariya sa'a tai tace ''hmm kallon kyaunki nake qawata, Wlh qawata kinji dad'inki ki godewa Allah da kyakkyawan sigar dayai miki kota'ina" kan heendu tace wani abu saiga kira ya shigo wayarta ganin sunan musaddiq ne yasata sakin dan tsoki tareda fadin "hoooo kai na tsani naci wlh haba dan Allah nina mnta ma munyi dashi yaune zaizo" daukar wayar tai batareda tace komi ba sai shine yace"ranki shidad'e gimbiyar mata gani fa a qofar gida ba iso ke kawai nikeda burin gani" cikin zuciyar ta tace"hmm jibesa da Allah ance maka inason namiji mai tumbi ne mtss" amman a fili sai tace"ok give me 20 mints i am coming" daga haka ta kashe wayar ta saida ta qara qara 6ata sama da minti 22 wajen gyaran fuskar nan a qalqale nan a goge nan a kuma shafa can sannan fa suka miqe Itada sa'a bayan ta yane gyalenta a wuya ta shiga d'aki ta iske maman a zaune tana Linkin kayan baba isma'il da heendu din ta gama wanke masa dazun, tace "mama zan d'an fita ne nn waje musaddiq yazo" dato mama ta amsa mata amman har a ran mama ba cikin jin dadi take barin heendu tsayawa da samarin taba inda tasan tabbas matar aure ce tun tana jinjirar ta. heendu tace 'wayyo 'sa'a wlh fitsari nikeji gashi ya isheni da waya mayen jeki dan Allah kudan fara gaisawa kanna gama" dato sa'a ta amsa sannan ta fita tanawa heendu dariyar fitsari yazo lokacin zance indama Allah yasa ba uban garin bane da kwalliyar ta tashi dan tasan halin heendu tsab zatace saita sake wani sabon wankan da kwalliyar sannan ta fito. tana fitowa daga bayin ta sawa qafafunta ruwa tareda tsanesu da wani qaramin towel ta nufi qofar fita knn taga an turo kyauren gidan tareda shigowa kai tsaye kamar ynda ya saba, doctor khaleepa knn, qin matsawa tayi dan ta basa hnya sannan kuma ga mamakinta taga ya tsaya cak gbnta batareda ya wuce ba kamar ynda tai tunani. saima wanj kallon da yakebin illahiri jikinta dashi bai kuma tnka ba, daga qarshe dai sauke idanunsu sukayi cikin na juna na tsawon daqiqu biyar sannan ya kauda fuskarsa daga tata bayan ya sake tur6une fuskarsa ya matso sosai gabnta har numfashinsa na sauka saman goshinta dan yafita tsawo. kallon takaici yake qara binta dashi wai shikam yarinyar nan mita dauki knata ne? dubi yanda doguwar rigar material din ta matse mata mama dud sun bullatso sama dan daqyar ma take numfashi tsabar mataseta da rigar tai sai wani matacin gyalenta wnda yashi y babu dud daya amman a haka take tunanin fita wani waje? , ganin yana shirin bata mata lokaci akan tsareta dayai yasata damuqe fuska tareda 6alla masa harara bayan murgudo baki datai a yatsune tayi nufin bita gefensa dan tai wucewarta, babu zato kuwa taji yasa wani mugun qarfin damatsan hannuwan sa ya maidota gabnsa ya ajiye kamar wnda ya dauki 'yar tsana dan batada nauyi sam sam, sai aijyar enlargement breast a gaba da kuma qugu nan ne masu qarfin a jikinta. daqyar ya daure ya bude bakinsa cikin kakkausar murya taji yace "kozan iy sanin miye had'inki da d'an iskan yaron nan khames headache?!.. tunani ta shigayi waye kuma khames?! dan ita kam harga Allah ta ma mnta da zancen wani khames dan haka ta zuba masa idanunta itama tareda cewa "nifa sauri nike zan wuce kabani hnya ana jira na a waje sannan ni kuma bansan wani khames ba dan haka ninka sake ni inda ba 'yar iska bace dazaka kaman hannu ka riqe" tayi mgnr tareda faman hararar hannuwansa dake damtse da cinyoyin hannuwanta. cikin fusata ya fuzgota tareda danganta ga bango yace"ok nine dan iskan knn? yatsine tai tace "nika rabu dani kona kira mama wlh" jiyayi knsa ta fara sara masa babu shiri sakamakon kwaratsin datake sashi yi batareda ya saba ba shiyasa ya cillar da ita gefe tai saurin dafe qasa ta miqe knn taji muryar mama na cewa "ya ilahi mike faruwa kuma haka tsakanunk da kuma heenduh khaleepa??,, duqewa yai wajen tareda tamqe knsa dake barazanar fashe masa lokacin dayaga heendu dun ta fice daga gidan bayan gama jifarsa datai da wani kallo wnda yafi kama da kalmar nan ta cewa *na tsaneka fa ni*,,,,, runtse idanunsa yayi tareda shiga dana sanin na harkar yarinyar daya shiga marar kunya qwarai yayi dana sanin hakan kuwa, dan dabai shiga harkar taba bazai jawa knsa ciwon kaiba anan... daqyar yasamu ya miqe tsaye tareda fita gidan batareda yacewa mama zainab komi ba. itako ta bisa da kallon mamaki na mike faruwane ga lamarin khaleepa da heendu ne wai da sam *basa ga maciji* tsakani??!! "Allah shi kyauta" abinda k-wai mama zainab tace knn ta juya ta koma d'aki dn cigaba da linke kayan wankin dan dama hayaniyar maganarsu ce dataji ta fuddo ta daga d'akin dan tasan sune daman inda sun kwana biyu basuyi ba dmn sai yau knn da mai kamawa ta kama....
Chapter 48 · 0% Book details