Sashe 9
Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
daki yaji meron tsimbe tace "mu kuma da ba'a son mu AllAh ya tsine mana ko? ko sauearen ta mlm zayyanu baiba yai komawarsa wajen almajiransa ransa a 6ace matuqa da mugun halin mero da 'yarta. mmn salis tace "oni Jameela haka kike zaman haquri daman knn? Ashedai maganar jama'ar anguwar nan da gaske ne na matsin da kike amsa daga mero da 'yarta? kan mmn Zainab tace wani abu saiga Zainab din ta shigo bayan ta ajiye kalanzir din nasu ma'ajiyarsa takai dubnta kan igiya taga babu kayanta data shanya taga saima kallon banza da tsana da firdausey din ke aiko mata dashi. daurewa tayi tace "yaya firdausey ina kayan shanyata kuma?" "suna gidan ubanki koni tsarar kice dazakimin mgnr wasu banzan kayan tsummokara naki shegiyar yarinya kawai " "Allah shi baki haquri yaya firdausey ai abin baikai na zagi ba, "inma yakai ko zaki rama ne? mmn Zainab tace "zo nan Zainab baro wajen" haka Zainab ta wuce dakin nasu firdausey ta bita da harara tana fad'in "masu baqin hali" tana gama shanyar kayanta tai komawarta dakinsu. Saida maman Zainab ta gama shanya kayan Zainab din a saman qyauren dakin sannan ta dawo wajen mmn salis ta zauna tace "hmm kedai kawai ayi sha'ani mmn salisu, wlh tunda mlm ya auro meron tsimbe ban sake samun kwanciyar hankali ba, takai ta kawo in dare yayi har barci ke qauracemun sakamakon firgitani da akeyi cikin dare da wasu halittu wanda tunda nike ban taba ganin suba, wlh saida mlm yaita mun addu'oen sa nima yabani wasu inayi dare da rana, bana zama jikina babu alwala to sannan na samu lpia fa, rigimar gidannan da masifar mero bata qaro ba saida ta tusa mlm gaba akan saita d'auko 'yarta ta dawo gidan nan, wlh dawowar 'yar tata gidan nan baqaramin gaggarumin wani tashin hankalin ya qara jefa muba, dan tun mlm na mgn harya kai ga ya daina dan masifarta sai Allah kam, kinga zainab nn wlh jininta saman akaifa yake a gidan nan danko jia saida firdausey ta kwada mata bokitin qarfe a goshinta kinga wajen nan sai yau da safe kunburin ya dan sace dan har yanzun da sauran gululun " tayi maganar tana nunawa mmn salis goshin Zainab din da hannunta, haquri mmn salis taita bawa mmn Zainab din da taketa faman kuka baqincin mero datake qunsa mata kullum a zuciya, da tsananin tausayin mmn Zainab mmn salis ta dawo gida kuwa ranar, to shine har take tausayin mukhtar dayakai kansa ga wannan mugun ahali gskia kam dole gobe ma taje wajen mamarsa inno taji kotasan da wannan mummunan al'amari, sauke ajiyar zuciya tayi ta d'auki fitilan ta sawo gidan ta dawo cikin daki ta shiga zuciyarta nata mata saqe saqen. Mukhtar kuwa wani yaro ya tura ya kirawo firdausey dan babu wayar da zai kirata kamar yanda ya saba in yazo. salis kuwa yana zaune saman dakalin qofan gidan ransa fal takaicin inda abokinsa yazo neman iri, jiyake wata sabuwan tsanar firdausey na lunkuwa a ransa sbd shan gaban mutumun kirki iriyar mukhtar mai tausayin ahalinsa datai. babu jimawa kuwa saiga yaron da firdausey a gabansa sun fito, sai wani karairaya take. "hubbi nayi mamaki danaji kaine kazo bakaimun waya ba kuma? cikin murmushi mukhtar yace "Wlh kuwa wayarce ta samu matsala,, ya kauce maganar da cewa ga salis nan ku gaisa tare muke da shi" da sauri kuwa takai kallon ta ga salis shima kuwa ya watsa mata nasa kallon cikeda q'iyayya, tuni firdausey tasan cewa salis bai son ta da mukhtar mafarin knn shima tai masa waje a cikin zuciyarta ta sanyasa a layin maqiyanta na sahu sahun farko kuwa, amman kuma dud rashin kunyarta ga mutane sam batta iya yiwa salis sabida wani iriyar mugun shakkunsa takeyi batareda tasan dalilin hakan ba, indai ko hakane na mawaqin nan da yake cewa wanda rai ke ajikinsa na *da sauran kallo*....