← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 178

Sashe 85

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

By
*Xexen Fasaha*
[2/13, 10:20 PM] Xainab Documen: 👁👁
🥡🥡
👁👁
*DA SAURAN KALLO*!!!

Story and writing by Xayyneb💤💤

Fasaha online writers.

*🌳Imparting valuable knowledge and intertaiment is our concern🌳*.

~dedicated to my mom Sadeeq hauwas~.

👁🥡👁
🅿4⃣0⃣.
*"A* matsayinta nawa zata temakeni kokai wannan faqiran mutanen ma?"
kai tsaye gwiwa a qarfafe yace"eah momy temako bawai yana nufin na kud'i ba ko wani abu kamar haka daya dangancesa just she...sh..'s help me na a matsayinta na mataimakiyar nan dai wacce harta iya zuwa kawomun takarkun shedar mallakan sabon company naki da dady ya siya mikin nan kanya tafi Wanda na karbosu yau daga can wajen mutanen kamar yanda suka alqawalta yau zasu bada sakamakon bugota da akai".
waro idanuwa Hjy firdausey tai tace "ban...ban gane ba fa?? miya had'ata da takardu bacin kaikaje karb'osu ne?"
"no momy ki gane dana karbo miki takardar ne na sakota a tsakan kanin wasu files na asibiti to ashe ta sub'uce ta fad'i sa'ilin da na fito daga mota na shigo nan gida to bayan ta kawomun takardar ne nima na tuhumeta a 'inane ta sameta dan nayi matuqar mamakin nima na yaddatan danai momy kinsan kuma wannan takardar in babu ita koda Wanda ya siyarwa da dadyn company din nan ne yai musun bai siyar ba ta zauna Inda shaida d'aya ce kuma mun rasata..."
d'an shiru yai da mgnr yana mai sakin numfashi zuciyarsa cikeda mamakin yanda ya iya tsara mgnr bazata haka babu ko tangard'a bare kuma tazgaro a cikinta shidai kawai yasan yana yine danya qwatowa headache k'imarta daga tozarcin da momyn tasa ke shirin yi mata dan jiyake maqoshinsa harya fara masa zafi saboda doguwar maganar dayaketa sakowa
dandai kawai ya ida wankesu daga zargi yasashi daurewa yaci gaba da cewa "kuma momy data kawomin takardar anan take shedamun a kofar gidan baba yawale danai parking din motar dazun alokacin data fito itama daga gidan baba yawalen akai sa'a anan ta hango fadowar takardar kwantiragin lokacin data isa gun ra d'auka nikuma harna shigo gida tofa mafarin knn tun alokacin bata biyoni ba saida tai shirin barci a yanzun take fadawa mamanta mafarin knn Maman tace tazo takawomun yanzun wataqil ko inada buqatar ta a yanzun lokacin dana neme takardar ban sameta ta...... sannan kuma to abinda yasa da kika shigo dakin nawa baki ganta ba ta d'an b'uya ne toilet gudun kada kiyi zargin wani abu tsakaninmu kuma gashi abinda ta gudan shiya faru kunyi zargin NATA.. yanzun dan Allah Momy ki fadamun bata temake kiba data kawo takardar nan Amman shine hadda samun gudumnuwar munanan maganganu daga gareki har kina kusantata da mazinaciya daga temako Momy??"!!
yayi maganar kamar gaske harda sauya fuskarsa ta koma kalar tausayi.
sosai kuma jikin Hjy firdausey taji yai mata sanyi duban khaleepa tai tace
"toni 'ina nasan hakan bansan wannan bayanin ba ay ko? kuma ai laifinka ne dabaka fadamun da wuri ba har saida hakan ta faru sannan"
sauke ajiyar zuciya yai ganin yanda tsarin maganar dayaiwa momyn tasa ta shigeta sosai sosai kuwa.
duban heenduh yai itama wacce tuni kukanta ya tsaya cak sakamon jin qaryar da khaleepa ke shararawa Hjy firdausey din kuma harta yarda💯.
batai auneba taga ya sakar mata murmushin nuna cewa Shifa *mai nasara* ne akan komi yasa gaba dan haka tama daina mamaki dan nasararsa a jinin sa take tuni batun yau ba.
kauda fuskarta tai ganin yanda ya zubawa hannunta ido daya d'an fasa yana jini jini inda zarah ta ciza din.
Ita kuwa miqewa tsaye tayi lokacin ne taji Hjy firdausey ta dubeta taci gaba da cewa
"ay ke kuma saiki haquri ki kuma kifita kibar man gida angode ba'a godeba".
"Heenduh ta maimaita kalmar
"angode ba'a godeba kuma? mikenan take nufi to?
d'an qaramin tsoki taja cikin ranta tace
""wannan kuma matsalarku ce inda Allah dai yasa nayi free daga sherrinki ahaka tafice daga gidan cikin saurin son ta qarasa gida kozafin dake hannunta bataji sbd qagararta datai ta isa a gida kodan mama Zainab ma kuwa..
zarah kuwa tana ganin heenduh ta fita khaleepa yayi komawarsa saman sa ta kuwa rushe da kukan baqinciki dantaso a 6atawa heenduh suna yau na abinda sukai zargi daga farko ashe abun ba haka bane.. wani kukan ta sakeyi tana kuka tana cewa "toni Momy Yaya zanyi da bakina data fasamun? gashi dutta bi ta wani yayyakushemin jiki ta fasa mun shi kamar wata hatsabibiyar mage,,, shegiyar yarinyar nan sai zugin zafi nikeji kallafa wasu gun harsun fasa ni haqorina kamar yana mun girgid'a inda takaimun duka shegiyar nikeji."
kamota Hjy firdausey tai suka Shiga toilet tasa ta wanke bakin dake yoyon jini da sauran wurare ta baro mata toilet din tabaro zarah din tana gasa jikinta da ruwan zafi sannan da ta gama hhy firdausey ta koma ta kamota suka fito suka dawo daki ta bata magani tasha tace "sannu kiyi kwanciyarki @ nan ki huta sai gobe kya koma gidan naku inda nafadawa momynki nan zaki kwana daman yau."
haka zarah ta kwanta zuciyarta fal tsanar heenduh kam ga ciwukan data jijji mata a jiki sun hanata sukunin rayuwa awahalce barci ya dauketa ko'ina na jikinta na mata zungar ciwo.
shiko khaleepa dasauri yasauko samansa hannunsa daukeda wani dan box aids na dressing din ciwo lokacin dayaga momyn da zarah sunyi daki aiko ya ida fita yabi bayan heenduh dan kareta daga fadan mama Zainab itama inda dai silar sa ne komi keta faruwa yau din kuma daga nan har ma yadan duba mata hannunta daya lura taji ciwon nan.
heenduh kuwa tana ra6e ra6e uwa wata marar gskia ta shiga gidan nasu takuwa iske mama Zainab tsaye tsakar gida tana d'aura musu net itada baba Ismail.
har kusada ita ta isa ta kamo hannun maman nata tace"dan girman Allah mama kiyi haquri mama na ban ankara dare yayi har aka bane wlh" fuzge hannunta mama Zainab tai taqi tanka mata ma taci gaba da qulla gidan sauron saida ta gama tsab sannan ta juyo ta dubi heendu dake tsiyayar qwallan fushin mama Zainab din gareta har haka.
fuska daure mama Zainab tace "kinko san har gidan baba d'ahara d'in naje bisa umarnin babanki akan natafo dake ganin yanda na kasa nutsuwa a Daren nan heenduh yau?
Ina kikaje kenan?,,,
tuni henduh ta fara qyafqyafta idanuwa dan wannan karon kam ta rasa ma ta cewa.
mama Zainab tace"wai badake nike mgn ba bazaki bani amsan daga inda kika fito ba inda yanzun sa'a batanan bare kice mun tare kuke??"
itawai miyasa komi tai sai ace sa'a bata bare....
kuka take shirin saki dan tunaninta uku ya kasu na farko fadan mama Zainab a gareta,,,
na biyu mgnr Hjy firdausey ce kawai ke mata kuwwa a kunne na inda take cewa khaleepa ya auri zarah dazaran dadynsa mukhtar ya dawo ya taimaka yai mata ladabin umarni a hakan ga amince warsa.
na uku kuma zafin marin zarah ne datai mata sai yanzun zafin ke qara shigarta zam zam dan daman hannun zarah kona wani qaton gardin namijin albarka kan tauri.
hannu tasa a kuncin nata tana sosawa zuciyarta na fada mata cewa kema ai kin rama bata shaki a basilla ba ...
zungar da hannunta yasakar mata na cizon zarah din yasata babu shiri sakin kuka a wahale ta durqushe wajen tana matse hannun...daidai nan khaleepa yashigo gidan ganin kukan headache datake yayi zaton ko wani abu mama Zainab tai mata ne dan haka yaqarasa shigowa gidan dad'an sauri sauri byn sallamar dayai.
sosai mama Zainab tai mamakin sake shigowarsa yanzun kuma kan tace wani abu har yayi saurin duqawa kusada heenduh a saman qafafunsa ya dubi mama Zainab bayan sauke idanunsa dayai kan heenduh yaja numfashi yace
"Momy headache nita raka kasuwa zab'an wasu kayan kyautarwa na mata Wanda nikeson bawa abokina gudunmuwa da zaiyi aure, kuma ma to sai banyi zaton zamu jima ba haka shiyasa dana gamu da ita zata shiga gidan matar can tsohuwa lokacin daman nan na nufo danta rakanin shiyasa kanma tashiga gidan nanemi alfarmar ta rakani din to shiyasa mama muka jima din ayi haquri."
sauke ajiyar zuciya mama Zainab tai tace"babu komi to amman aiyaci ace ta qirani a wayar ta inda tafita da ita saita shaidamun kokuma Dana kiratan ga dazun saita fadan din ko? Inda tasan fitarta a dare bana nutsuwa a hakan yanda duniyar nan keta garambawul da mutanen cikinta khaleepa?..
gyaran murya baba Ismail yayi tareda ajiye butar hannunsa daya fito daga ban daki ya qaraso wajen yana cewa "dud naji komi na abinda kuke tattaunawa zainabu kuma inda gashi shi khaleepa yazo yai miki bayani kuma sundawo lpia ai alhamdulilla ko?"
"hakane Mlm nidama laifinta nagani ba nasa ba data kasa mun bayani tu wuri shiyasa"
baba Ismail yace
"ai komadai mikenan shikenan magana ta wuce"
"To ai shikenan mlm tayi mgnr tanufi daki dauko musu sauran kayan kwanciya shima baba Ismail ya Shiga d'akinsa dan canzo kayan dayake kwanciyar barci dasu shima wato Wanda suka fara danyin taushi cikin kayansa na sawa.
kallon mamaki kawai heenduh kewa khaleepa na qarairayinsa yau din nan kuma wai dud dan ya kareta? batasan sanda da suka had'a ido ba tasakar masa murmushi ba shima taga ya kashe mata ido daya wanda yasa take taji wani iri a jikinta har saida ta lumshe idanunta tana kuwa bud'esu
babu zato kuwah taga khaleepa ya miq'e da sauri cikin shigarsa dayayi ta qananun kayansa dasuka haskasa inda akwai NEPA lokacin ga mamakin ta d'akinta taga yayi shigewarsa.. zaro fararen idanuwanta tayi waje a matuqar mamakan ce da kuma tunanin miyake nufi to??!,
jiyo muryar mama Zainab tayi tace
''saikije ga ruwan wankan kican a boket rufe na hada miki run dazun".
dasauri ta miqe tana kallon hannunta tayi saurin b'oyesa ganin yanda jini ya biyo gefen hannun saurin boyesan da tai gudun kada mama Zainab ta gani ne.
dakin ta shiga ta iskesa ya hard'e q'afafunsa kan daya yana zaune kan kujerar dake dakin ta gaban Mirrow dinta yana latsar wayarsa hankalin sa kwance...batace masa komi ba ta dauki towel dinta ta fita daga dakin bayan ta kunna fankar Sama jin akwai zafi lokacin... kashe qwan dakin tai taja qofar ta saya.
lokacinda ta fito harta iske su mama Zainab sun kwanta a net dinsu bayan kullo gidan da akai.. jitai gabanta ya wani buga dammm!! Damm! sanin datai khaleepa na gidan basu saniba su kuma sun rufe Yaya kenan to?
dan haka jikin nata a sanyaye ta dauko kwandon sabulun nasu kawai tadauka takai bayi tadawo ta dauki
bokitin ruwan da hannunta marar ciwo ta Shiga dashi bayin sannan ta fara wankan zuciyarta na tunanin zaman mi wai doctor din kemata ma a daki yaqi tafiya?? !!!
tsoro taji ya shigeta na gudun kaddafa mama Zainab taje cikin dakin in case shiyasa tafara wankan cikin hanzari tana Allah Allah tagama taje ta setasa qofar fita inda tanada tabbacin su mama Zainab sunyi barci zuwa yanzu......
Chapter 85 · 0% Book details