← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 178

Sashe 33

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

dashi, yanzu kam jitake koda yau Allah zai karb'i ranta itadai kam burinta ya cika Alhamdulilla harma takejin ta yafewa mukhtar abinda yai mata kmr ynda baffa ya jima da yafe masa shima a wata tattaunawa dasukai kwana 2 da suka wuce, sun masa afuwa dan sunsan dan nasu ba haka yake ba a da wataqil ajizanci ne na mutum shiyasa kullum suke masa adduar dawowa madaidaiciyar hnya yaci gaba da kulawa da kowa nasa kamar da. Ismail da zainab kuwa jin bayanan baffa dayai yinin ranar sukuku sika yisa dan sun san km *da sauran kallo* ga wannan al'amari kam wnda basusan iya halin da zai sanyasu ba suda su baffan kuwa, shiyasa kwata kwata basuyi farinciki ba dan sun tabbata akwai mabi baya daga su mukhtar yanda suka qisu dinnan sunsan da sauran rina a kaba. a ranar kam bayan taron suna ya tashi inno da wata maqauciyarsu hawwa'u suka gyara gidan yadawo fes kamar ba'ai taro ba, sannan ta tafi gida inno ta rakota har waje tana godia dashi albarka sanna koma daki, sai kuma ta fito ta leqa dakin mai jego zainab daga bakin qofa tace "zainabu ince dai akwai shauran tuwon suna dan nida mlm kam shinkafar nan ta ishemu zainabu ku yara kuma na lura batta isarku ko" inno ta qarashe maganar cikin fara'a. zainab tai saurin tasowa cikin murmushi bayan ta ajiye heenduh tace "wlh inno ban sani ba amman bari na duba miki naga ni" tana maganar ne tana qoqarin zuro qafarta waje inno tai saurin tareta tace "kul zainabu ai mu bamu barin mai d'anyen jego fita inba wanka ba, da wani uzurin na jikinta kuma, bayaga haka komi kuwa komi zatayi a daki zatai muna fiddawa waje mu kuma, dan haka yi zamanki d'aki bari naje na duba madafin naga" haka inno ta wuce zainab ta bita da kallon batasan mi zata sakawa inno dashi ba tasan inno na qaunarta ta riqeta kmr ynda ta riqe isma'il sam batta nuna mata banbanci tsakanin su bata dauketa suruka ba kokadan, wasu yan siraran hawaye zainab taji sun sauko mata batareda tasan dalilin zubowar tasu ba. komawa tai ta zauna ji heenduh ta motsa tana shirin yin kuka tana zama ta dauketa tareda sa mata nono a baki tafara sha ita kuma. Inno kam ta duba kicin cikin manyan languna da aka zuba shinkafa taga ta rage nan ta rufe tareda bude dayan langar taga tuwo yayi sauran mulmile uku saidai babu miya, shiyasa ta d'aura sanwar miyar kan baffan ya dawo da yake har an fara kiran sallar isha'e shiyasa tana had'a jajjagen kayan miyan ta barta kanta tafaso saitayi alwala tashiga d'aki dan gabatar da tata sallar ishae d'in. a kuma dai dai wannan lokacin ne firdauseey ce sanye cikin baqar after dres da gyalanta ta nade fuskarta da wani baqin niqaf ta fito daga gate din gidan nata danko jaririn na hannun hjy Hadeeza badashi ta fito, yanda take sauri sauri kasan ta qagara ta aiwatar da abunda ya fiddota lokacin. kai tsaye inda ake siyar da shinkafar 6era ta nufa ta siya sannan aka had'a mata da fiya fiya original din marar sirki ta zuge jikkarta ta sanyayasu ciki ta wuce da wani d'an saurinta kai tsaye gidan isma'il ta nufa daman kunsan qofar babu zaure shiyasa tana zuwa kawai tasa hannu ta turata a hankali bata kaiga shigowa ba ta zuro kanta a tsakar gidan tagan shi wayam babu kowa da sauri ta ida kutsa kai cikin sanda ta ida shiga tsakiyan gidan taja ta tsaya a tsakar gidan dan tarasa inda madafin nasu yake damba zuwa take gidanba bare tasan kansa, kallon gidan kawai take a ranta take cewa matsiyatan banza da wofi harni zaku so d'ana to wlh yafi qarfinku d'ana ba kalar auren 'yar talakawan 'yarku bane dan kuwa yau gaba d'aya zanyi maganinku kowa saiya baq'unci lapira yau dinnan tsinannu zakusan ni firdauseey bala'e ce masifa ce a gareku da kuma qazaman rayuwarku ta talauci. da sauri ta boye jikin bayan qyauren qofan waje dan motsi da taji. ta leqo sai taga qanwarta zainab ce ta fito da lullu6in zane da buta a hannunta ta nufi qofan bayi ta shiga ta rufe, hango hayaqi na fitowa ne daga wani tsukakke waje wanda ke nesa da bandakin kadan da firdauseey taine hakan ya tabbatar mata da nan ne kicin dinsu, cikin sand'a ta isa wajen ta iske yar qaramin tukunya a wuta sai tafasa take dasauri ta bide tukunyar taji qamshin daddawa a ciki da cefane tuni ta tabbatar da miya za'ayi ga lokacin, murmushin cin nasara ta saki dan haka a hanzarce ta bude jikkarta ta fiddo kwalbar fiya fiya din duka ta juye musu ita tareda shinkafar 6eran ta d'au muburki ta motse su ciki ta snn ta maida murfin tukunyr a hankali ta rufe tai saurin ficewa daga gidan har tana kaiwa qyaure karo a dai dai nan ne kuma inno ta fito ta shiga kicin din da kuka a hannunta cikin leda, nan ta duq'a ta d'auko muburikin ta bude murfin ta fara zuba kukan tana murtsukawa saida ta gama tsab miyar ta dafu sannan ta zuba tuwon a roba ta juye miyar akai ta koma d'aki, tasake fitowa tana cikin gyara wajen knn zainab ta fito daga kewaye da addua dauke a bakinta nan taiwa inno sannu ita kuma ta amsa sannan ta wuce d'aki. ana gama sallar isha'e kuwa baffa ya dawo ya shigo da sallama har d'aki nan ya iske inno sai fifita tuwo take da mafecin kaba dan tasan baffa baison abu da zafi in zaici, akai sa'a kuwa duka zafim ya fita, bayan ya ajiye buzun sa da carbinsa ya zauna gaban tuwon yana cewa "kai Allah shi miki albarka innon yaranta kamar kuwa kinsan dama yunwa nikeji ta tuwo aamn, murmushi inno tai tace "hmm ai gashi saikasa hannu muci daman kaina tsaya jira, yana gyara hannun rigarsa bayan ya gama nad'eta yace "sannunku aiyau kunsha aiki ya hidima da jama'a na suna?, yayi maganar tareda sha'afa wajen bismilla sai kawai ya tura lomar abuncun a baki, itama inno dai dai ta gama had'iye lomar tata tuwon tace ''Alhambdulilla anyi taro lpia an tashi lpia kuma mlm" masha Allah abinda baffa yace knn nn sukaci gaba da cin tuwon, baffa yace "kash kaga mantuwa iriyar na d'an adam ko, wlh nmnta bnyi addua ba, inno tace wlh nima na shafa'a mlm kuma kaga yaune kawai aka samu akasin dan bismila aita zame mana jiki kam" baffa yace kinsan addini sauqi garesa yanzun ma bamu makara ba sai muyi tare ay, nan take yace "bismillahe fi awwalihi wa'a khirih,,,,,,, tsit yai ya kasa qarasawa jinda yai a lokaci guda cikinsa kamar an daddaure masa hanji waje guda kuwa, kankace mi baffa ya fara fita hayyacinsa tuni le6una sa sika bushe suka koma fari fat dasu sai shaqquwa yake, bnda salati bashi komi lokacin, inno na shirin yunqorowa itama taji cikinta ya kame kam kwata kwata babu dadi abun kamar ana jujjuya ta takeji tuni suka kwanta wajen sai wutsil wutsil na billaye sukeyi dan zuwa yanzu kam abun yakai geji dan har wani kakkauran kunfa kunfa fari tass mai sirkin jini jini ya fara fitowa daga bakunansu idanunsu a kakkafe rai yazo maqwar qwara madakata suna kallon sama sun kasa motsi kalmatisshahada suke yi daqyar Allah sarki kankace mi su baffa har rai yayi halinsa, dai dai nan aka dauke wutan nepa, babu jimawa da dauke wutar zainab ta fito da fitila ta dakinsu inno da nufin kai musu ganin an dauke wuta kuma inno batazo karba ba, sallama tai tashiga dakin tana cewa inno ga futilan taku nak.. Sakin fitilar tai tayi kansu inno a gigice ganin da tai musu a halinda suke aciki shine ya tabbatar mata da cewa babu alamun rayuka a jikinsu ko. sakin fitilar tai qasan wajen takuwa fasa wata mummunan qara ta fadin wajen tana shure shure kanta daina motsin itama.....
Chapter 33 · 0% Book details