← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 169 OF 178

Sashe 169

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

👁🥡👁 🅿6⃣8⃣. *G* agin datai bashida dai niyyar bud'e mata qofan ne nan tasake sakin wani qarar kukan wanda hatta zarah dake cikin d'akinta saida ta juyo ta, aiko da sauri saigata kuwa ta fito ta tsaya daga nn setin qofar dakin ta tana sakin wata dariyar mugunta tana fad'in "kai kai saurina da gobe dai kam saurin zuwa wlh, yanzu wata banza tasa aka gama qonamun rai a banza a wofi, to ashe itama natan nanan tafe? hehehe danasan hakan ma zata aiko aida banyi saurin b'ata ma raina ba dan gashi yanzu an wankemun shi tassss" hhhh may be duka kikasha ya tulloki waje ma ko? kaiiii huh,,,, abin gwanin burgewa, naji dadin ranar nan, nan taita danqarawa heenduh zafafan maganganu masu dauke da qasqanci, amman ita heenduh kam sam zarah bata gabanta dan ita abinda ya dameta ya da meta shiyasa kawai taga babu dalilin da zaisa ma ta biye mata dan ita kam yanzun bata d'auki zarah mai cikkaken hankali ba yanzun,,, dan haka miqewa tai daga wajen ta goge hawayen fuskarta tareda watsawa zarah kallon tsana da qyama snn tace "uwa da uba sun bani tsabtatacciyar tarbiryar dako ina naga dabban mahaukacin mutum ko kallon Inda yake bazan iya ba gudun kamuwa da jahilci kalar nasa kuwa, dan haka ina umartarki a shawarance da cewan kije ki samu karya abokiyan haushinki kuyi tayi amman badai niba heenduh na wuce class d'in musayar harshe da kishiya, kishiyar ma musamman ballagaza kamarki, kuma ki sani doctor na da kike taqama da wai kin samu power a gunsa kike wani tadamnun kai da hura hanci ko? to ki sani ganin damata ne na bar shige masa har yasa hakan ya faru, in yanzun nayi nufi maidosa gareni to ina mai tabbatar miki da cewa ruwa saisun miki wuyar had'iya kuwa a maqoshin ki cikin gidan nan, dan in baki wasa ba da kanki zaki bar gidan nan qafa ana kare, domin yaya na aronsa na baki, kuma aron nasa ma dana baki photocopy dinsa ne tare dake dan original dinsa na waje na damqe a tafin hannuna, so da fatan kin d'auki darasin karatun nawa ko? nina wuce dan ban iya jin zan tsaya sauraron wannan haushin naki ba na manyan karnuka"!!!! tana gama fad'in mata hakan kuwa ta zagayeta tai shigewarta d'akinta. aiko zarah cikin zafin zuciya na kalar zafafan maganganu da taji heenduh ta gama dandanqara mata su ata cikin ruwan sanyi yasa nan take kuwa taita sako ruwan bala'e tanata qunduma uban zagi na munanan ashar wanda sak 'yar bariki zakaji tana sakin kalar wannan zagin , tanayi kuwa tana dukan qirji bakinta na fitar da farin kunfa ata geffensa,,, ganin datai babu wanda yasan tanayi ne yasata had'iye masifar tata ta koma cikin d'akinta tana cigaba da zagin heenduh, dan qwarai maganganun data ya6a mata sun ta6a mata zuciyarta matuqa. jitai gidan yayi mata zafi tuni ta daura after dress saman kayan jikinta ta figi key d'in motarta ta shige bayan ta kira hafeez tace su had'u a hotel d'in da suka saba had'uwa. heenduh kuwa najin tabar wajen da wasu mintoci nan tayi saurin qara futowa ta koma bakin qofan dakin khaleepa daga ciki wajen qyauren ta raku6e ta zauna gamida dunqule jikanta waje daya ta sanya fuskarta cikin gwiyoyinta, zuciyarta naci gabar mata da zafi na ciwon fushin da yakeyi da'ita. tarasa ma mike mata dad'i a cikin rayuwar ta, tana nan zaune harta fara jiyo kiran sallah daga babban masallacin dake anguwar,,, sake lafewa tayi wajen ta kwanta, babu zato taji qarar bud'e qofa kokan ta yunqura ta janye jikinta daga jikin qofar inaaa,,, dan har ta fad'i qasan farkon shiga dakin,,, "washh Allah na!!!" abinda heenduh tace knn sanda ta miqe zaune tana luliya damtsen hannunta ta na dama data fad'i samansa,, binta yayi da kallo cikin mamaki na tunanin kaddaifa ace yarinyar nan tana wajen nan zaune tun dazun gashi yanzun duhun magrib harya fara,,, ganin datai ya d'auke kansa daga gareta yana qoqarin tsallaketa ya wuce wanda ga alama masallacin zaije Inda ga prayer mate nan da nurussubahe na cazbaha a hannunsa. aiko da sauri ta ta yunqura tareda durqushewa gabansa ta rungume qafafunsa tsam tsam a cikin qirjinta tana matsar qwalla take fad'in "doctor please ka yafemun na rantse maka fa da Allah nace bazan qara maka rashin kunya ba, ka yarda dani bazan sake b'ata maka rai ba I will promise"!!!! qwace qafafunsa yayi har tana fad'uwa qasa, baice mata komiba yayi ficewarsa masallaci" tashi tai daga wajen tana share hawaye ga kuma yanda takejin kanta na wani mummunan sara mata kuwa a lokacin, toilet ta wuce ta shiga tareda yo alwala ta fito tayi sallar, tajima bata d'ago ba, tanata kai kukan ta ga Allah cikin sujjadarta ta qarshe na roqon Allah ya sanyaya zuciyar doctor d'in nata, ba'ita ta tashi ba daga wajen ba saida tayi sallar isha'e sannan ta miqe ta cire dogon hijab d'in jikanta, tayo wanka tadawo saman gadonta daga ita sai towel daure a qirjinta ta kwanta tayi lamo idanunta a rufe..... jitai wayarta dake gefenta ta d'auki ringing, bud'e idanunta tayi a hankali gamida tareda miqa hannunta ta jawo wayar,,, number sa'a ce tagani. dasauri tayi qoqarin miqewa zaune ta daga wayar tunkan tace wani abu nan ta jiyo dariyar sa'a d'in cikin tsokana take cewa "uwargidan doctor khaleepa yakk ya amarci, na bugo ne na goge lefina nasan cinmutunci da zagi daga bakinki heenduh saidai na to she kunne Inda nai miki tonon silili, sorry qawata bazan juri ganin iyayenmu cikin damuwar rashin ganin kiba, na boye musu alhalin nasan Inda kike,, shiyasa tun ranar da kika dawo dudda nasan kin dawo wato doctor ya je ya d'aukoki naqi kiran ki na bari ne daman ad'an kwana 2 inkin huce saina kiraki dan nasan nida qawata bata 6aci ko? to kiyi haquri yiwa kaine shiyasa nai hakan" wani murmushin dole heenduh ta qaqalo, dan kuwa tabbas tayi niyar wanke sa'a datai mata wannan tonon,, amman ina yanzu ta rusa budget d'in komi dan labarin kuwa yarigaya da yasha banban, dan yanzun Inda akwai abinda take buri bai wuce ace ta samu mafita wacce zata shawo kan doctor d'in nata ba, shiyasa tace " hmnn sa'a da knn kika sani, yanzun nayi sanyi, wlh ina cikin matsala sa'a please yaushe zaki shigo ne?" sa'a tace "cab ke d'in ke daukar shawara? aini na daina baki shawara Inda ba dauka kikeba 'yar renin hankali kawai da shegen taurin kai uwa a garin arna kika fito" marairaicewa heenduh tayi tace "yi haquri qawata, wlh komi dakemun yawo aka yanzun na ajiyesa waje d'aya, please ki taimaka kizo dai d'in dan nasan bama bari na zaiyi nina zoba yanda yake fushin nan dani, ay da saidai kawai ki ganni" sa'a tace "to shikenan Inda kin kawo uzurinki, kinci sa'a da gobe zan koma amman zan daure nazo da wuri gobe d'in da safe insha Allah kanna wuce baucin" cikin murna heenduh tace "yawwa qawata ta kaina ina jiranki" a haka sukai sallama. komawa tayi ta kwanta jitake ta qagara gari ya waye sa'a tazo, dan uwa ta jawo gobe da safe takeji saidai inaaa. haka ta kwanta taita juye juye hardai tayi nasarar bacci ya dauketa. washe gari Monday tunda wuri khaleepa ya fuce zuwa office zuciyarsa cikeda mamakin yanda zarah bata kwana gida ba, saima text datai masa nawai tana gidansu can zata kwana sai gobe zata dawo, ko replay bai mata ba a lokacin saima barcinsa daya shigayi bayan dawowarsa daga gidan su, da kuma gidan su heenduh, wato wajen mama zainab da baba isma'il gamida baba yawale daya biya yakai masa gasassun kaji, sanda ya fito daga masallaci yashiga mortarsa yanufi anguwar tasu iyayen nasu knn. heenduh kuwa bacin ta gama komi tayi wanka ta shirya cikin wani milk d'in lace riga da zane sai faman walainiya takeyi cikinsa, nan ta dawo falo ta dake, zaune take saman kujera hannunta riqe da wayarta taga har goma da kusan minti arba'in sa'a bata iso ba alhalin ta mata text d'in address d'in gidan da anguwar dataje ta tambaye maigadinsu wani soja ne, kuma gashi sa'a d'in sai ce mata takeyi gata nan a hanya ta tafo amman kuma shiru kakeji har yanzu, d'an siririn tsoki heenduh taja tana qoqarin sake kiran number sa'a d'inne kawai taji sallamarta ta shigo falon gidan,, aida gudu heenduh ta miqe ta isa wajen sa'a suka rungume juna suna faman qyalqyata dariya. saida suka natsu ne sannan ta miqe taita cikewa sa'a gaba da kayan ciye ciye danginsu kwad'ai. saida sa'a taci dambun naman nan sosai da holandia yoghurt snn suka bar falon suka shige cikin lambun gidan suka zauna saman wasu blue d'in kujeru bayan sa'a ta daura jikkarta a tsakiyan tebur d'in kujerun. shiru heenduh tayi tayi qasa da kanta dan tarasa ma ta Inda zata farowa sa'a mgnr ma kwata2. dafata sa'a tayi tace kinacin tym dinki fa matar doctor kinsan da tafiya a gaba na kuma nazo kinyi shiru kinqi cewa komai"tayi mgnr tareda sakin murmushi. sauke ajiyar zuciya heenduh tai snn ta kwashe komi ta fadawa sa'a dangane da abinda tace masan nan har yayi fushi, snn kuma da qofar da zarah ta samu ta sanadiyyar hakan tana mata cin kashi kala kala, dubanta sa'a kawai take kamin tace "komi ke kike jawo wa kanki shi heenduh, yanzun to da kikayi wannan katob'orar zancen wa gari ya waya knn? kefa knn, snn kin bawa kishiya kofar sanin babu jituwa tsakanin ki da mijunki har tana miki habaici,,, gskia in zaki chanza kawai ki canza qawata dan wannan hanyoyin da kiketa bi bamasu 6illewa bane kwata kwata, dan banda wahala babu abinda halayenki ke ja miki " kamo hannunta heenduh tai tace" naji komi kikace kuma na rigaya danasan nayi kuskure tunma kan kizo, please sa'a kibani solution wlh gaba daya banjin dadin zuciya ta" taqarashe mgnr daqyar uwa zata fashe da kuka. itama sa'a kamo hannun heenduh tayi cikeda tausayin ta kuma, sakin murmushi tayi tace "mafita daya ce dhe first solution shine kasan yanda zakiyi har kishawo kansa ya haqura, karkice kin gaji yaqi haquri, no daurewa zakiyi kina basa haqurin gamida yar kissar nan tamu ta mata, dadai
Chapter 169 · 0% Book details