← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 178

Sashe 91

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

yayi cikin qirqiro murmushi sannan dady salis yace "yawwa kuma insha Allah da zarar na dawo zansa a gyara gidan nan yanda ya dace kuma saimu zauna dakai kafadamun kalar sana'ar da kakeson farawa kadaina zama bakin hanyar nan saida cefane dan Sam banson hakan har a raina, kuma ma sainaita ganin kamar cewa mutane zasu zageni kan nakasa tabuka maka komi dud yanda muka taso a zumuncen nan uwa 'yan uwan jini." Girgiza kai baba Ismail yai yace "bazasu zageka Yaya salis domin halak d'ina ne na fito nema dan haka dud wani mai kaifin tunani bazai zageka ba koyaga laifinka dubaga d'an uwana na jini ma yana raye bai zamemun dole ba amman kai gashi ka zamemun". har aran dady salis d'abi'un qanen nasa Ismail kan burgesa na tsagwaron nuna tawakkali da kuma abin duniya da bai rufe masa ido ba. kan yace wani Abu wayarsa tai ringing ganin matarsa CE wato mmn baby amnat yasashi miqewa da fadin "nina wuce qanena suna can Suna jirana zamu tafi..dasauri heenduh tace"dady salis pleass inkun dawo zaka kawomun baby amnat ta kwanar mun? murmushi dady salis yayi yace"Kunlun saita mun zance ki itada dai Aunty beauty nakaita gunki harmafa ta fadawa mamanta ke? Amman dazarar mun dawo insha Allah zan kawo miki ita heendatuh" cikin murmushi tace"yawwa thanks dady salis adawo lpia. saida baba Ismail yarakasa waje sannan yadawo ciki zamansa keda wuya wayar mama Zainab dake can cikin dakinta tahau ringing duban heenduh tai tace"jeki miqomin ita heenduh". koda taje ganin sunan mama jamila wato mamar mama Zainab din yasata fitowa ta miqawa maman tana cewa qawata CE ke kiranki Ashe mama na" harararta mama Zainab tai tace"kifa kiyayeni heenduh na fada miki fa" dariya heenduh tai kawai takoma ta zauna kusada baba Ismail. mama Zainab bata sake bin ta kanta ba ta d'aga wayar da cewa "Assalamu alaikum mama barka da marece... shiru tai tana sauraran mgnr mama jamila din dasauri sukaji mama zainab tace "Innalillahe wa'inna ilaihirraji'un yaushe yarasu mama??.. dutta rud'e cewa takeyi to.. too gani nan zuwa.. dasauri takashe wayar baba Ismail suma sai tanbayar ta waya rasu ne? sukeyi. cikin hawaye mama Zainab tace"kaka liman malam ne (baban mama jamila dake zaune garin zaria). Allah yaimasa cikawa yanzun nan. innalillahe......tashi zakiyi muje tare" cikin goge hawaye mama Zainab ta kallesa tace"a'a baza'ai haka ba kamanta da baba yawale ne dake kwance shima asibiti ba lpian baban heenduh? to Zainabu naga ai mutuwa CE takauda komi ko?" "dudda haka dai baban heenduh kaga baba yawale na buqatarka wajensa kada kuma wani abun yataso babu makusan cinsa.. Kabari koda yaushe ne saika je gaisuwar inda akwai lalura data hanakan tafiya zankuma sanarwa da mama" to Amman tareda heenduh zaku! Inda kinga gidan yanzun zai zamanto babu kowa inda ni kuma zan dinga zuwa kwana asibiti." girgiza kai mama Zainab tasakeyi tace"batareda ita zaniba inda itace zata dinga muku girki tana kaiwa asibiti dasauran ayyukan gida"..shiru baba Ismail yai baisan miyasa Zainab keda kaifin hankali ba dudda ake cewa qwalwar mata bataja sosai to shikam ya Musa dan Matan ma Suna suka Tara akwai 'Yan baiwa kamarsu Zainab din kuma bugu daqari ga wadataccen ilimin addini data shawo a gidansu musamman a babanta Mlm zayyanu. "to shikenan zainabu kimin gaisuwa inkinje kamin Nazo insha Allah" miqewa mama Zainab tai dan had'a 'yan kayanta dazata jedasu heenduh tabita da kallo da tunanun abubuwan dasuketa samunsu yau na jarabawa ta rayuwa wacce dole daman jarabawa ta dinga rizqar nusulmi kodan gwada yawan imaninsa kamar yanda yazo a hadissai ingatattu. tashi tai tabi bayan mama Zainab din zuwa dakinta daidai lokacin da mama Zainab tagama zuge jikkar 'yan kayanta kala hud'u data saka a ciki. kamo hannunta heenduh tai kamar zatai wani sabon kukan tace"amman mama ni kad'ai kenan zan dinga kwana a gidan nan yanzun?! wlh mama sai nikeji kamar ma zan dunga jun tsoro bazan iyaba mama, zan dunga dai zuwa gidan baba d'ahara ina kwana harku dawon.. ajiye jikkar mama Zainab tayi takamo hannun heenduh tace"sanin kanki ne bannason kina fita waje koda yaushe heenduh , ki daure kiyi zamanki anan din cikin gidanku kada kije kuma ki takurawa baba inda kina ganin yanda yaran danginta dud sunzo mata Hutu kuma gashi babu wani isasshen fili a d'akinta nata kada ki takurasu dan Allah ki zauna abinki anan kinji?." d'an qaqalo murmushin dole mama zainab tayi tareda d'an jan hancin henduhn snn tace "kima daina jin wani tsoron zama waje d'aya danko ba jima zakije d'akin mijinki kinga ta tsoro yakau inda shima zai dinga fita nemo muku abinda zakuci bawai zaman gida zaiyi tareda keba , kema a haka zakiga har kin samu 'Ya'ya abokan zama kema ko? dan murmushin jin kunya heenduh tai batace komiba kawai ta sungumi jikkar Maman suka fito itada baba Ismail suka rakata har gidan mama jamila bayan guzuri isasshe daya bata sannan suka dawo. kozama basuyi ba baba Ismail yace su koma asibiti. suna isa kuwa cikin d'akin cikin ikon Allah babu jimawa baba yawale ya farka. sannu suke masa cikin murna saiga doctor mus'ab ya shigo ya q'ara duba sa sannan ya juyo tmya dubi baba Ismail yace"yanzun zaku iya basa abinci yaci amman mai d'an ruwa ruwa haka" daga haka ya matsa kusada gadajen sauran fatient din yana cigaba da dubasu. duban heenduh baba Ismail yayi yace"muje na tsaida miki napek sai kije gida kid'an dafo masa wani abun saiki dawo ki kawo ai zaki iya gane asibitin ko wajen dawowa?" "eh baba na" "to ungo wannan ya miqa mata dubu biyu yace ''saikiyi abinda yadace" amsa tai suka taso zasu fita a karo na barkatai suka sake hada idanu da doctor mus'ab din. tsoki taja dan tunda yashigo ta lura da kalar yawan mugun nacin kallon dayake mata tatsani kallo fa ita. daidai suna fita harabar asibitin shima doctor khaleepa ya fito daga office dinsa cout dinsa sagale da kafad'arsa dan babu wanda ya lura da junansu shidasu baba Ismail sai sukaji muryar doctor mus'ab dake tafe a bayansu yad'an d'aga muryarsa yace doctor wait mana" d'an jimmmmm na dakatawa khaleepa yayi bayan bud'e murfin bayan motar tasa yasaka jikkarsa a motar sannan ya juyo. ai kiwa yayi arba dasu baba Ismail da heenduh dake gefensa suna tafiya. cikin mamaki yayi saurin yin dogon taqi yaci gabansu yace ckn muryarsa "small dad kunzo dubiya ne asibitin namu?" daidai nan doctor mus'ab ya qaraso wajen zuciyarsa cikeda mamakin daman doctor khaleepa yasan sune? to Indai haka ne bazaiyi qasa a gwiwa ba wajen saka abokin nasa yai masa jagorar samun auren kalar wannan zuqeqiyar hot babyn dayaji ta kwanta masa tashin farko da ganinta dashi a yanzun. Baba Ismail yace "a'a yarona baba yawale aka kwantas ay anan din yau". cikin mamaki yace baba yawale kuma! awane bangare aka kaisa" caraf doctor mus'ab yace "mutumina wannan patient din d'an bangarenmu ne banaku ba. (male section patient) yayi mgnr cikin tsokana. tsoki Doctor khaleepa yayi yace"dudda haka amman kasan takowane fanni ina zagayawa daiko cechking? dan murmusji baba Ismail yai yace "yanzunma munfito ne na nemawa heenduh abun hawa zataje gida ta d'an dafo wa baba yawalen abinci." "OK small dad muje saina sauketa gidan inda nima can zanje." baba Ismail yace"AF to shiknn ma heenduh ga d'an gida ma jeki kuje." doctor mus'ab yace "badai katashi ba?" saida yashiga motarsa ya tada sannan yace "saika duba tyme ai kagani" daidai nan heenduh ta qarasa zagayowa ta shiga motar. dariya doctor mus'ab yayi ya maida idanunsa kan fuskar henduh datai saurin janye fuskarta tana kallon wani shashen cikin Jin haushi q'arin kallonsa. haka yaja motar suka tafi bar suka d'au hanya baice mata komiba tuqinsa kawai yake Yakama fuska ya daure tamau. Kallonsa tad'an sata tayi da gefen idanunta ta6e lips tai tace a ranta "miskilancin ne ya motsa maka yau knn?...to muje a hakan dan nima bazan kulaka ba muje zuwa... tana gama tunanin hakan ta maida kanta gefen titi tana kallon mutanen dake tafiya kan gefen hanya bata Ankara ba saiji tai yataka wani wawan burki harsaida ta firgita. "kee dubeni nan abinda yace knn fuskarsa babu walwala ko kadan a cikinta. q'in juyowa tai saima sake maida fuskarta waje datai ranta itama a b'ace da bahagguwar halayersa karkatacciya maras tabbas....
Chapter 91 · 0% Book details