← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 154 OF 178

Sashe 154

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

👁🥡👁 🅿6⃣4⃣. *D* ady salis ne yayi qoqarin jawo hannun khaleepa d'in suka koma can dakin dasu mama zainab suke dukkansu, su mama zainab na ganin shigowarsu sukai saurin tarbarsu, momyn amnat ce tai saurin furta cewar"yaya anganta kuwa? Allah yasa, dan ubangijin mu na roqeku kada kuce muna sace heenduh azayi?!,,, tayi mgnr hawaye na zuraro mata daga fuska yayinda mama zainab zaiyi wuya kace ita ga yanayin halin da take ciki dan kuwa, dan kwata kwata ma kasa mgn ma tayi saidai binsu kawai da takeyi da idanunta... su dady mukhtar kasa amsa musu sukai kowa yai jigum jigum sai khaleepa kawai ne yafara mgn yana mai cigaba dajin wani dandanon maqaqin daci a idanunsa banda azaban zafi da harbawa babu abinda zuciyarsa tafiye yimasa lokacin, daqyar yadago jajayen idanunsa yadubi su mama zainab hawaye na tsiyaya gefe kuncinsa na dama, sosai mama zainab tai mamakin abinda yasaka khaleepa kuka haka, dan iya sanin ta dashi mutum ne shi mai taurin rai farin cikinsa da baqincikinsa ma ba fiye gane masa su zakai ba in yana cikinsu amman yau kam da alama babban abu ya girgiza zuciyarsa rawanin buzu yayo qasa warwas, abinda kaga khaleepa ya zubarwa hawaye kansa lallaikam abun azeemun ne kuma yanada matuqar mahimmanci garesa, babu zato taji yana fadi cikin muryarsa da cewa, "mama heenduh mun duba a gaba kidayan hospital din nan bamu sameta ciki ba, mama waye zai daukemun mata? mama ki fadamun waye shi bazan taba yafe masa wannan mummunan sa6on zunubin daya aikata gareni har abada kuwa na rantse!!!!" mgnr yake cikin wani sabon tashin hankalin dayake Jin yana sake shigarsa lokacin. gaba daya suma su mama zainab sai suka ida rudewa tareda rawar jiki daya kwashe su nan take, suna faman cigaba da tsattsafo hawaye na tunanun ina heenduh tayi a cikin wannan rayuwa haka mai ban tsoro?? daqyar dady mukhtar yashawo kansu suka zauna kowa yai shiru bakkajin motsin komi face na shessheqan kukan momyn amnat da amnat d'in yayinda mama zainab tunda ta sadda kanta qasan wajen bayan ta zauna to bata sake marmarin sake dagowa ba saidai tanajin komi ke faruwa a wajen, sosai mama zainab takeda tsananin nuna alkunya akan dud wani lamari daya shafi heenduh. dady mukhtar ya dubesu dukknsu shima yasake sauke wata ajiyan zuciyar sannan ya hada hannunwansa waje guda ya dunqule su ya daura saman qafafunsa sannan yace"ya ilahi ya rahman innalillahee wa'inna ilaihirr ajiun,Allah ka kawo mana dauki, haqiqa daga ubangiji Allah muka fito kuma daga garesa ne zamu koma, tabbas tashin hankali yasamemu ba kadan ba, dan 6acewan d'a ba qaramun tashin hankali bane ga iyayensa wanda kuwa har gwada ace yau ga gawarsa a gabanka kasan wannan Allahn daya bakannan shine ya karbi abinsa tareda sanin daka qarayi na cewa kaima adud sanda Allah ya buqaceka tabbas ko second bazaka qara ba,, shiru yai nadan wasu daqiqa sannan yasake duban fuskokinsu kowa yayi jigum jigum jiki a matuqar sanyaye,,, cigaba yai da cewa '' to bare kuma wannan b'ata ce bawai mutuwa ba, saidai kuma ni'inaji a jikina adud Inda heenduh take bata mummunan waje cikin hukuncun Allah, dudda dai dukknmu nan bamu da tabbaccin cewan shin ya'ilahi d'auketa akayi ne? ya'ilahi ita d'in da kanta tabar nan d'in to allahu ta'ala dai a'alamu, yanzu ina roqonku da girman Allah ku kwantar da hankulanku kada kubawa jama'a damar sanin halin da muke ciki ta hanyar ganin damuwan a fuskokinsu, dan Allah inaso ku dauka cewa tanfar heenduh na gida ne dan yanzu daga nan Inmun tashi zamusa afara mana roqon Allah ubangiji daya bayyana mana ita ko jin wani lbr daga gareta,, insha Allah zamu dauki tsawon sati Ana wannan roqon Allah daga bangarenmu mudaku dakuma sauran malamai na Allah, dan tabbas dud wanda ya maida lamarinsa ga Allah bazai taba tabewa ba da fatan kun fahimci ni, kaima kuma khaleepa ka fahimci zancen nawa kuyi haquri zata dawo nan bada jumawa ba da yardar Allah dan dukknmu nan dama sauran musulman Allah munsan adud kan lamari in akasa ubangiji Allah a cikinsa to zakuga abun yazo cikin sauqi da yankewan wahala insha Allah, zamu cigaba da addu'a bazamu taba gajiyawa ba har Allah ya bayyanata garemu'' daga dady salis har baba isma'il dasu mama zainab sunji hankulansu kashi 50 cikin dari daya bar kansu to jin wannan sanyayen hikayan fasihan bayanai da dady mukhtar yayi ba qaramun sanyaya musu zuqata sukai ba, nan take sukai na'am da shawarar da ya kawo musun Inda babu yanda suka'iya da tsarin Allah wanda sunsan daman Allah ne ya hukunta heenduh zata barsu a wannan lokaci to yaya zasuyi da ikon Allah Inda babu damar yin shisshgi a lamarin ubangiji, dan kuwa dud inka cika musulmi na qwarai kuwa tofa jarabi na qaddarori da dama zakaita cin Karo dasu a rayuwarka dan auna imaninka, kuma daukan qaddara ma ga musulmi na abunda Allah ya nufesa dashi to wannan ma lada ce mai zaman kanta. baba isma'il ne ya sauke ajiyar zuciya ya dubi yayan nasa cikin qarfin zuciya yake " hakane yaya munkuma ji dadi sosai da wannan tunasarwa taka ubangiji Allah kuma yasa tana hannu na gari" da aminn aka amsa yayinda shima dady salis yace "amman kuma mutane 'yan biki yaya za'ayi dasu knn dan kaga dole zasu tuhumi Inda ita heenduh take dan kaita gidan mijinta kamar yanda a'lada ta sabar" momyn amnat cikin sanyayen murya tace '' hakane kam dady amnat dan wlh kaga wayana nan tun dazun mama(maman salis d'in knn take nufi) taketa mamu waya nida momyn heenduh kan mutane 'yan biki sun fara jaje na babu ita heenduh babu mamanta kuma kasan mutanen yan biki basusan ita heenduh d'in nama asibitin ba'' dady mukhtar yace "yanzun abunda za'ayi ke maman meenat kikira maman kice ta sallami kowane abokin arziqi da fadin cewan an d'aga tariyar heenduh gidan nata sai nanda wani dan lokaci, sannan kuma dan Allah ina roqon kada kowa a cikinmu ya sanarwa da wani batan heenduh inkun dauke mama daya zama dole ta sani daman ita, dan muddin mutane sukaji b'atan nata to Allah kadai yasan surutun da mutane zasuyi tayi, dan wasu zasuce ma gaban kanta tai tatafi dadai sauran su,,, kunsan mutane da maida qaramun magana ya zama babba, musamman ma in mgnr ta dura cikin taron mata to insha Allah in ba'ai sa'a ba yanzu kaji an murd'e mgnr lokaci daya ta bada ma'anar wani batun na daban kuma,, koni kaina bazan fadawa hjy furdausey wannan batun ba dan bansan mgnr ta fita, mucigaba da roqon Allah har Allah ya kawo mana mafita a lamarin, saidai batun ita zarah d'in babu matsala zata iya tarewa a gidan dan gudun zargi na cewa itama d'in adaga tarewar ta gidan kunga knn za'a sakawa mutane wasu wasi a zuqatansu ace mata biyu babu wacce aka kai a ranar da aka tabbas daza'a kaisu gidan mijin nasu rana daya kuma ko ba haka ba?" baba isma'il da dady salis suka amsa da hakama shawarar ce yayi, dan haka nan take momyn amnat takira mmn salis ta shaida mata dud abunda akace itama ta buqaci Jin dalilin sallaman mutanen amman sai momyn amnat din ta nusar da'ita data bari insun dawo daga asibitin sayi mgnr. a haka suka baro asibitin amman dudda wannan kalamen da dady mukhtar yayi zuciyar khaleepa batabar masa zafi ba, shiyasa koda ya had'u da abokansa su yunus suna shirin masa complain na yaje wajen amarensa ya sharesu dakatar dasu yayi tareda basu haquri ya nuna baijin dadin jikinsa mashi yanzun haka, dole suka tausaya masa kuwa dan sun kula da rashin nutsuwa kuwa muraran daga doctor d'in nasu musamman da kalolin idanunsa suka sauya daga na'uin asalin fararensu zuwa na'uin jaaa....daga nan ya karb'i key d'in dakin yunus ya wuce danyafi son ya kwanta Inda zaisamu yayi jinyar zuciyarsa shi daya batareda an takura masa ba, asali ma shi koyaye ne baison yaji kowa ya rab'esa bare yasa shi mgn, mafarin knn ya kashe dukkan wayoyinsa bayan kiran number heenduh daya tayi tafi shurun masaqi amman taqi shiga, kwanciya yai a katifan yunus idanunsa na kallon sama yayinda wasu zafafan tafasassun ruwan hawaye suke qara baquntar fuskarsa batareda ya ankara ba,dankuwa jiyakeyi in bai bawa hawayen damar futowa ba tofa bazai taba samu sukunun sauqin zugugin zafin da zuciyarsa ke masa ba a lokacin. acan kuwa gidan su heenduh bayan 'yan biki dud kowa ta tatafi su dady mukhtar suka iso gidan suka iskesa rufe dole suka nufi gidan mmn salis d'in anan suka sameta itada baba d'ahara ananne kuma mmn salis d'in tashaida musu dalilin rufo gidan datai wato sbd yan biki basu katsewa shugowa gidan, wato wasu na tafiya wanda sukaji lamarin d'aga tariyar wasu kuma na shigowa wadanda basusan da mgnr d'agawan tariyar ba. mafarin knn ta kallo gidan sbd kowa yazo dole dai yaja daga knn. mama zainab ta nuna hakanma yayi, babu b'ata lokaci kuwa nanma dady mukhtar ganin baba dahara dayai kuma yasan itama tanfar jinin suce yasa yafada musu batan heenduh, sosai hankulansu kuwa ya d'agu dan baba dahara hannuwa ta daura aka tana kuka daqyar dady mukhtar ya shawo kansu suma suka dan haqura ta hanyar bayanan dayaiwa su mama zainab d'in a dazun suma. haka sukai jigum jigum har aka kirayi sallar magrib sannan su mama zainab suka fara shirin salla dan qara had'awa cikin adduo'en'insu na salla da roqon Allah ya maido heenduh gida lpia ko hankulansu ya kwanta. suma su baba isma'il koda suka fito daga masallaci byn sungama sallar isha'e bin baba yawale sukai har gida shima suka shaida masa batan heenduhn kuwa. Allah sarki har rikicewa baba yawale yasoyi saida salati da fadin Allah sannan ya dawo dadai gamida tausarsa dasu baba isma'il d'in suka dinga yi.. baba yawale bawan Allah dakansa yayi musu alqawalin farayin qiyamullailai tundaga yanzu kan batan heenduhn har sai Allah ya bayyanata lpia tukun, sosai sukaji dadi daga nan bayan sun fito wajen mlm zayyanu baban mama zainab suka nufa basu fito fili sun shaida masa 6atan ba amman sunbuqaci yatayasu da addu'a kan wata 'yarsu data b'ace,, babu b'ata lokaci kuwa tun anan wajen mlm zayyan yafara addu'a kuma sunji dadi sosai daga nan suka qara nausawa wasu
Chapter 154 · 0% Book details