← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 178

Sashe 27

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

qatuwar private hospital wacce akwai mnyan likitoci a cikinta. harda baqin turawa maza da mata kuwa a cikin likitocin nata qwararrun gaske wanda suka qware ta kowane fanni. sakamakon ciwon da firdauseey ta kwana dashi a daran jia wanda kamar zata mutu, suna zuwa wani babban likita ya dubata yace nan da rabin awa zata iya haihuwa, shiru kakeji rabin awa ta koma awa daya, awa daya ta koma biyu biyu ta koma uku, abudai har marece bnda 'yar banzar azaba babu abinda take sha dole likitoci suka sa mata ruwan naq'uda sannan ta fara nishin gasken gasken na haihuwa, tasha baqar azaba kuwa dan aqarshe tana yin wani bbn yunquri kan baby ya fito likitoci na ida janyo mata babyn ita kuma tana sumewa. mukhtar na waje amman hankalin sa baqaramin tashi yayi ba jin wani ihun kukn azaba da firdauseey keyi, jiyo kukan jaririn dayai ne yasashi hamdala dasauri ya nufi shiga dakin aikuwa security suka hana sa dole ya haqura ya tsaya, acan kuwa sunyi matuqar qoqari sannan firdauseey ta farfado. haka suka gyara kyakkyawan jinjirin yaron wanda suka tabbatar ya zuwa yanzun yanada matsala danko numfashi ma saida qyar yake yinsa, nn suka ta masa aune aune har suka gano inda matsalar take. wani baturen likita ne ya fito daga labour room d'in ya kira alhaji mukhtar d'in zuwa babban office dinsa bayan ya zauna nn ya dubi mukhtar yace cikin yarensu"yalla6ai babynka yasamu matsalar toshewar numfashi wanda har matsalar ta shiga cikin wasu hanyoyi dasuke da dan gan taka da numfashin sa wanda yake shaq'a, to zamu sanyashi a cikin wasu einges na na'ura har tsawon sati biyu dan munada tabbacin 2 in akai masa hakan zai dawo normal, zai yiyu kuma ya rayu ko akasin hakan" cikin rawar jiki mukhtar yace "doctor ban... bangane ba? kamarya zai rayu bazai rayu ba?" baturen doctorn yace ''eh, ina nufin a qa'ida naurorin sune zasu fudda masa sanyin da mamarsa ta dunga shayar dashi a ciki lokacin ta hanyar kayan sanyi data dunga sha, yanzun haka, so yanzu zamu baka uniform saikasa kashiga ka gano su dan mu ba,a shiga room din saida uniform na hospital namu a jiki, haka kuwa aka bawa mukhtar wasu tsanwayen kaya da sunn hospital a gabn rigar sai wata farar hular leda yasa yashiga room din da sauri. yana isa kan gadon firdauseey yaganta rungume da jinjirin ansa masa kayansa blue amman sai kuka take, karbar yaron yayi. "ya subhanalla" yace ganin gaba daya yaron kamar baffansa ya d'auko sak. dogo ne sosai fari tas ga hanci sannan gashin kansa da jikinsa kwance laya laya alamun na cikakken fulanin usuli knn. Amman kuma sai dai kash dud wannan baiwar kyan sura da AllAh yaiwa babyn bayya numfashi saida qyar da qyar yanda kasan bazai qara koda second ba kuwa a duniya saboda hatta mad"igar babyn nasa ana ganin tashin bugawarta. kuka firdauseey take tana cewa "dan AllAh mukhtar kada yarona ya mutu ina sonsa wlh zuciyata zata fashe nima wlh inbisa, dutta rude ta gigice sai sambatu take. rungume jinjirin mukhtar yayi a jikinsa ya zauna bisa wani gado dake gefen na firdauseey saboda yanda yaji son yaran na ratsa b'argo da tsoka na jikinsa kaishi fa jiyake baiqi a halin da ake yanzun ba ace yabada komi nasa ba saboda d'an nasa yasamu ingantacciyar lpia kamar kowa. kawai sai qara rungume jinjirin mukhtar yayi yana kuka. suna haka saiga wata 'yar tsamurarrar baturiya ta shigo room din ita da 'yarta. nan baturiyar ta cirewa firdauseey drip din ta fita yayinda 'yar tata ta matsa kusada mukhtar ta dan riqesa ganin yana kuka kamar qaramim yaro yasata fadin "oh sir yi hakuri kada ka damu babyn ku zai samu sauqi insha Allah" amman ina kwata kwata mukhtar baisan ma tana yiba kuka kawai yake firdauseey na tayasa dan ganin da suke a yanzun rashi zai risqesu dai dai lokacin da sukaga samu Allah kenan!
Chapter 27 · 0% Book details