← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 178

Sashe 1

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Compiled By Umar Dalha Funtua.

Copied By Xayyneb 💤💤

https://www.facebook.com/Fasaha-Online-Writes-751775151851852/?referrer=whatsapp

*DA SAURAN KALLO*!!!
👁👁
🥡🥡🥡🥡
👁👁
Fasaha online writers f. o. w.

*🌳imparting valuable knowledge and entartaiment is our concern*🌳

story and writing
by
Xayyneb 💤💤

~In the name of Allah the benepeciant the merciful~

Bismillaheer rahmanirraheem.
.....
🅿1⃣
*T* a shigo gidan nasu hannunta riq'eda wata 'yar q'aramar baby nokia tana waya, kaida kaga yanayin halin da nokiar take ciki kasan ta fara jin jiki dan har da wata 'yar siririyar farar salatif aka nad'e a q'asan ta dashi a wajen sa cajin kenan da wani d'an falan day'a na salatif d'in gudun kada wajen ya ida su6utowa yayo qasa.
amman inkaji yanda heenduh ke faman sake nonnoq'e sanyayyar murya tata tana magana harda wani lumshe idanunta zaka d'auka wata iriyar babbar touching ce take wayar da ita, wannan karan a tsiwace take fad'in
"mtsss haba dan Allah nace ka bari sai next week zamu had'u anan gida dan wlh kokazo yanzun kayi wahalar banza danba wai fitowa zanyi ba uniform d'ina zan goge danma kaji fah, haba ka fiye naci musaddiq wallahi"
daga can 6angaren day'a musadiq ya dafe kansa ya rasa miyasa yarinyar nan ke son had'a masa hyper tention ba da sonta a ransa kamar zuciyarsa zata tsinke yakeji, da q'yar ya bud'e bakinsa yace "to.. to shiknn gimbiya ta heenduh Allah shi kaimu juma'ar lpia ai kmr gobe ne inda saura kwana 2 ko nikeji? "
tana tsoki ta katse wayar take fad'in "ban sani ba nataccen mutum kawai" tana mgnr amman still hankalin ta na kan wayar tana tafiya dan qarasawa cikin gidan nasu,
da yake babu zaure a gidan bika wuce ne.
turo lips d'in bakinta tayi hakan ne kuma ya bawa qwan zuma cwingum d'in dake maq'ale cikin bakinta da yayi q'atoto damar fitowa ya fashe sannan ta cigaba da rats rats tana cigaba da sakin qarar q'wan cwingum din a bakinta abinda babanta ya hanata kuma knn wato qas qas na cwingum indai yana gida kuwa bata yarda ma ta fara sa cwingum a bakinta saiya fita dan ita kam sam sam batta iya taunar cwingum batareda da tai masa qwai da q'as q'as ba,
tana shirin d'agowa da fuskarta kenan daga saman wayar tata sakamakon sanin jarababben qamshin mutumin da tasan waye mamallakin turaren da tayi.
bata ankara ba kuwa by mistake taji goshinta ya doki gefen chest dinsa, da sauri ta ware masa manyan fararen q'al d'in idanunta a kansa fuskarta cike da mamakin miya kawosa gidansu bayan abinda ya faru jia tsakanin babanta da nasa dud akansa kuma?
ranta taji yayi wani mugu mugun 6aci sosai, nan ta sake ware masa manyan idanun nata akansa bayan ta soke wayar tata a cikin bra d'inta daga saman rigarta ta atamfa wacce ta fara jin jiki.
matsowa tayi da sauri a gabansa ganin yanda yake shirin zagaye ta ya wuce bayan gama binta da kallon banza da ya gama yi shima harda wani ta6e red lips dinsa yayi bayan ya kakka6e gefen farar rigar sa ta t -shert da wani blue hankicerf dinsa cike da qyanqyamin abun, wato a dai dai inda kanta ya d'an gogi qirjin nasa.
cak yaja ya tsaya shima ganin yanda tasha gabansa da sauri hannuwanta na saman kwankwaminta tana binsa da wata iriyar muguwar harara a tsiwace tace "miya kuma sake kawo ka gidanmu eye d'an masu kud'i?
uhm? yaya akai mahaifin ka har yasake barin ka shigo gidan talakawa kamar mu? ko bai san kazo bane em?
dakai nike fa mlm?
wata kalar zazzafan harara taga ya sakar mata tareda sake d'aure girar sa tamm tamm babu alamun fara'a nan danan kuwa tsabar k'warjinisa mai cike wa kowane jinsin mace ko na miji ido ya bayyana garesa, hakan ba q'aramin tsorata Heenduh yayi ba tareda haddasa mata faduwan gaba babu zato babu tsammani, amman sam saita kanne bata nuna hakan ba a fili,
'd'aurarriyar fuska a wajen sa ai ba yau ta saba ganin ta ba daman can bare ta sare.
"mai mugun hali, mutum ko dariya baima san ta inda ake farawa ba bare wani abu waishi ma murmushi indai kaga murmushin sa to tasan suna fira da maman tane ko babanta indai har yazo gidan, inko tana kusa ko haqorinsa day'a bata gani.
abinda ta fad'a knn a qasan la66anta,
"matsa ki bani hanya"
yayi maganar yana mai fiddo mata kalar nasa idanun magargad'a gareta na rashin wargi a cikinsu ko kad'an dud ya tsattsare ta dasu.
kuma har cikin ransa hk abun yk, ga kuma fuskar nan dai still gim da ita,
mamanta dake zaune a qofan daki a saman tabarma masassara ce sosai a jikinta amman dataji abin na heenduh bana q'arewa bane sam sam dan ita kam dai batasan a inda heenduh ta d'auko wannan masifar tsiwar ba a danginsu,
heenduh da batasan mamar na wajen ba sai muryarta dataji tace "bazaka bangaje ta bane kalipha ka wuce koka mammareta inda ita ta maida kowa sa'anta?,,
ta qarashe maganar tana aikawa heenduh da harara bayan had'a idanunsu da sukayi da mamar,, baice komi ba ya zagaye ta ya wuce dan shi baida lokacin yi mata ko day'a daga cikin abubuwan da mamar ta lissafo,, hasalima shi bason mgn yake ba inba kamawa taiba yatsani mutum mai hayaniya hkn yasa yake mugu mugun jin haushin yarinyar dudda ta kasance sister tasa ta jini kuwa amman babu wanda baiqi jinin kowa a cikinsu ba hatta iyayen nasu sunsan da hakan, hakan kuma ya samo asali ne daga banbancin halayya tasu,
zumburo baki Heenduh tayi bayan ta zauna gefen mamar kamar zatayi kuka tace tace "yanzu wai dan Allah mama har kin mnta abinda baban sa yayi mana kuwa jiya jiyan nan ba har nan cikin gida?'
dubnta maman tayi bayan ta d'anyi tari da qyar sannan tace "heenduh kullum qara nusar dake nike amfanin haquri a rayuwar yau, haquri shine ya kawomu a yanzun, da bamuyi haq'urin nan ba da bazamu kawo i ya yanzu ba, mama ta nisa sannan tace haquri gadadden abuni tun daga annabin farko Annabi adamu (A.s) har ya zuwa ga annabin qarshen zamani Annabi Muhammad rasulillah (SAW).
dan haka kiyi haquri mai haquri zai cimma gaci a rayuwar sa, kije ki zazafawa babanki tuwon sa kinsan ya kusan shigowa yanzun, ta qarashe maganar tana mai maida kanta ta kwantas bisa wani shafaffen filo wnda da gani tun na amarcin ta ne,
kan Heenduh tace wani saiga Khaleefa ya sake shigowa hannunsa dauke da jikkar nan ta likitoci wuyansa sagale da abin awo yunus a bokinsa na biye dashi a baya.
"sannu mama" cewar yunus yana mai zuqunnawa saman qafadunsa, "yawwa yunusa" cewar mama,, Khaleefa kuwa kusa da mamar ya matso yace cikin riqaqqan muryarsa "mama bari na auna naga miye matsalar,,,,, mamah tace "oh ni Khaleefa har cewa nai ka barsa nasan masassara ne zansa heendu kuma ta amso min magani a chemist,,, saida ya waiwaya gefen da Heenduh din ke zaune ya watsa mata harara bayan had'a idanunsu da sukayi tun zamansa wajen, batai qasa a gwiwa ba kuwa ta murgud'a masa bakinta itama ta miqe tsaye tana shirin barin wajen taji yunus na cewa
"headache din doctor namu barka da wuni" harara ta sakarwa yunus tuni kuwa ya sinne kansa yana dariya qasa qasa dan yasan bata son sunan da abokansa suke kiranta dashi, quta tayi ta ida wucewa tana fad'i a ranta "bakuda laifi laifin shugaban naku ne da ya samun sunan, wani takaici taji ya qara shigarta wai itace headache ma gaba day'a ? (ciwon kai)
a haka ta qarasa ta fara had'a murhun garwashin dan zazafawa baba tuwon nasa.
Khaleefa kuwa tuni ya maida hankalin sa ga awon da yakewa mamah, bayan ya gama aune aunen ne ya zare abin awon daga kunnuwansa ya dubi mama dud ransa bai masa dad'i ganin abubuwan da take dauke dasu na ciwuka a jikinta,
bayan gyara farin medical glass din idanunsa da yayi fuskarsa a damuwance yace
"amman mama miyasa kike z.......

~Xexen fasaha~
f. o. w.
[1/17, 3:09 PM] Xainab Documen: 👁👁
🥡🥡
👁👁
*DA SAURAN KALLO !!!*

Story and writing
by
Xayyneb 💤💤

Fasaha online writers f. o.w.

*🌳imparting valuable knowledge and entartaiment is our concern*🌳.

-https://www.facebook.com/Fasaha-Online-Writes-751775151851852/?referrer=whatsapp.
Chapter 1 · 0% Book details